✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani: Na bar wa Gwamnan Zamfara Naira biliyan 7 – Yari

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya musanta rahoton da ke cewa, Kwamitin karbar mulki da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya kafa ne ya bankado…

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya musanta rahoton da ke cewa, Kwamitin karbar mulki da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya kafa ne ya bankado wasu bayanai da suka nuna gwamnatin Yari ta bar bashin ‘yan kwangila da ya kai Naira biliyan 251.

Mai taimakawa tsohon Gwamnan akan watsa labarai Alhaji Ibrahim Dosara, ya musanta wannan rahoton kuma wannan zargi ne wanda babu gaskiya a ciki.

Abdulaziz Yari, ya ce ya bar wa sabuwar gwamnatin kudi da ya kai Naira biliyan 7, amma ya yi mamakin yadda sabon Gwamnan ya gaza tantance ayyukan da aka kaddamar da bashin da ake bin jihar, duk da yake ya rike ya manyan mukamai a jihar.