✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Martani: Ba jiharmu ce ta fi ko’ina talauci ba a Najeriya —Sakkwato

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ba ta yarda jihar ce ta fi ko'ina talauci a Najeriya ba.

Gwamnatin Jihar Sakkawato ta ce ba ta yarda da kididdigar da ta nuna jihar ce ta fi ko’ina talauci a Najeriya ba.

Jihar ta fadi hakan ne a matsayin martani ga rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta fitar kwanan nan, wanda ya nuna Sakkwato ce ta fi fama da talauci a kasar.

Gwamnatin jihar ta mayar da martanin ne ranar Laraba, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Jihar, Alhaji Arzika Bodinga.

Bodinga ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen wani taron kara wa juna sani na yini daya da aka shirya a jihar.

A makon da ya gaba ne Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa ‘yan Najieriya miliyan 133 ke fama da talauci.

Sannan daga cikin jihohin kasar nan, Jihar Sakkwato ta kere kowace jiha a fama da matsanancin talaucin.

(NAN)