✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani: Ashe maza bayin mata ne?

A kwanakin baya mun kawo muku wata mukala mai taken ‘Ashe maza bayin mata ne?’ Jama’a da dama sun turo martaninsu a kan mukalar, don…

A kwanakin baya mun kawo muku wata mukala mai taken ‘Ashe maza bayin mata ne?’ Jama’a da dama sun turo martaninsu a kan mukalar, don haka ne ma a wannan makon za mu sanya sakonnin nasu.
Za mu fara da wani sako da muka samu daga [email protected] wanda ya ce: “Ka ga na farko Allah (SWT) ne Ya umarce mu (maza) da yin hakan, ba wai mu ne muka ga ya dace da mu yi musu hakan ba. kin yin hakan kan iya jawo mana lalacewar imaninmu, Malam Abubakar ina ba ka shawara a kan ka cire wannan dabi’a a ranka cewa MAZA BAYIN MATA NE. Lokacin da nake karantawa na yi zaton mace ce ke wannan bayani, amma a karshe sai na ga Abu-Bakr Haruna ne. Na yi mamaki gaskiya, amma ka yi hakuri fa.”
Umma kuma cewa ta yi: “Gaskiya Malam Abubakar na ji dadin yadda ka fada wa maza gaskiya. Allah Ya sa su gane gaskiya. Kuma ina mai yi maka addu’ar Allah Ya saka maka da alheri Ya jikan iyayenka da kakaninka. Don Allah ka ci gaba da fadakar da maza hakkin da Ya rataya a kansu.”
Hajiya Salamatu ta ce: “Hakika mafi girman haske ilimi; mafi girman duhu jahilci; mafi girman kyawun zance gaskiya; mafi munin zance karya; mafi kusantowar al’amari tashin kiyama; mafi girman arziki wadatar zuci; mafi kyawun hali hankali; mafi kusanta ga Allah Ibada; mafi kusanta ga shaidan hassada da girman kai; mafi kusanta ga aljanna imani da Allah da ciyarwa; mafi kusanta ga wuta shirka da rowa.  Ya kai dan Adam mumini ka yi amfani da lafiyarka kafin rashinta; ka yi amfani da lokacinka kafin mutuwa ta riske ka. Hakika ka fadi gaskiya Allah Ya saka da alheri. Maza da mata sai a kiyaye.”
Maryam Jigawa: “Abubakar na karanta rubutun da ka yi mai taken Ashe Maza bayin mata ne? Hakika ka fadi gaskiya. Sai dai na ce Allah Ya saka da alheri. Allah Ya kara budi.”
Alhaji Sani Sulaiman: “Ka ji tsoron Allah. Gaskiya abin da ka fada ba gaskiya ba ne, kuma ba haka yake ba. Babu yadda za a yi maza su zama bayin mata. Allah ma Bai ce haka ba, kai ka kirkiro ka fada. Ya kamata ka rika sanin abin da za ka fada. Gaskiya ban ji dadin rubuntaka ba wannan karo. Da kana yin rubutun da yake faranta mini rai na karu sosai, amma yanzu ka koma soki-burutsu.”
Matar Faruk ta ce: “Assalamu alaikum, wannan bakon naka mai maganar Maza bayin mata ne ya yi magana ne daidai da fahimtarsa. A tawa fahimtar da cewa ya yi maza bayin Allah ne, to da hakan zai fi. Domin duk abin da ya zayyana suna yi wa matansu ai bautar Allah ce, don Shi za su yi. Duk matar da ta dauki mijinta a matsayin bawa, to ta halaka kanta, namiji ba bawanta ba ne. Hoton da kuka nuna bai dace da al’ada da addininmu ba, a nawa ganin ke nan.”
Hajara Ibrahim: “A gaskiya na kadu da na ji wani yana cewa wai maza bayin mata ne, ba haka ba ne, miji shugaba ne a wurin matarsa. Komai za ta yi sai da izininsa. Idan za ta fita sai ya yi mata izini, idan za ta yi azumin nafila sai da izininsa, aljannar mata tana (karkashin) kafar mijinta, idan haka ne ta ina miji ya zama bawan matarsa?”
Ibrahim Idris: “Da farko ban mayar da hankali wajen duba wanda ya rubuta makalar ba har sai da na kammala karantawa, amma ga mamakina sai na ga namiji ne, ko ina hankalinsa ya shiga oho, akwai hadisin da Manzon Allah ya ce da zai umarci wani ya yi wa wani sujuda a duniya, to da ya umarci mata su yi wa mazajensu sujuda. Don haka ina fata za ku daina birkita abubuwa don ra’ayinku. Ga mata kuma ina fata ba za su rudu da irin kururuwar daidaiku irin su Abubakar ba.”