A ranar Asabar za a fafata a wasan Kwata Final tsakanin kasashen Maroko da Portugal a Gasar Cin Kofin Duniya da ke wakana a kasar Qatar.
Idan Maroko ta doke Portugal, za ta zama kasar farko a yankin Afirka da ma kasashen Larabawa da ta taba kaiwa Wasan Kusa da Karshe a tarihin Gasar Kofin Duniya.
- WAEC ta rufe cibiyoyin jarabawa a makarantu 61 a Kogi
- Qatar 2022: Argentina ta sha da kyar a hannun Netherlands
A makon jiya ne Maroko ta yi waje da kasar Spain daga gasar, ta shiga sahun kasashen Afirka da suka taba kaiwa wannan mataki na wasan Kwata Final, sai dai kashi! Babu kasar Afirka da ta taba tsallake matakin a tarihin gasar.
Kasashen da suka kai Kwata Final
Kasashen Afirka hudu ne kacal suka taba samun zuwa wasan Kwata Final a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya.
Kasashen su ne Kamaru, sai Senegal sai Ghana sai kuma Maroko yanzu.
Najeriya, Giwar Afirka, za a iya cewa girma ya fadi a nan, domin ba ta taba kaiwa matakin ba.
A Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 1990, Kamaru ta fafata wasan Kwata Final da kasar Ingila, inda Ingilar ta doke ta a birnin Naples bayan an barge gumi na minti 120.
Bayan shekara 12, Senegal ta samu wannan tagomashi a Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2002. Sai dai ita ma kasar Turkey ta yi waje daya da ita da ci daya mai ban haushi.
Daga nan babu wata kasar Afirka da ta kai wannan mataki sai bayan shekara 10 a gasar 2010, inda Ghana ta fafata da Uruguay.
Sai dai ta ma nan aka yi waje da ita a bugun fanareti bayan Suarez ya cire kwallo da hannu ana gab da tashi, inda aka samu bugun fanaretin ci mu tafi biki, wato ana gab da tashi, dan wasan Ghana, Gyan ya baras.
Maroko za ta iya cire wa Afirka kitse?
Duba da yadda wasannin gasar na bana suke zuwa da ba-zata, inda aka samu Saudiyya ta doke Ajantina, Japan ta ci Janus, sannan ita ma Marokon ta doke Spain, da kuma kasancewar ba cika sanin maci tuwo ba a wasan tamola, ake ganin sai an buga kawai.
Yadda ’yan wasan Maroko suka nuna kwarewa a wasansu da Spain ya zama abin misali.
Sai dai akwai alamar gajiya da kuma masu raunuka da za a iya cewa sun sadaukar da kansu domin buga wasan da Spain bakin rai bakin fama domin nemo suna.
A wasa hudu da suka gabata, kocin Maroko, Walid Regragui sau daya kawai ya canja dan wasa daga cikin ’yan wasa 11 da suke fara wasa, inda Abdelhamid Sabiri ya buga a wasansu na karshe na rukuni a madadin Selim Amallah.
Wannan na nuna rashin ’yan wasan kwararru da dama, wanda kuma ke kawo gajiya ga wadanda suke ta bugawa.
Ita Portugal kuwa, tana da zaratan ’yan wasa a benci, da ya sa ake samun sauyi domin samun hutu.
Haka kuma a wasannin rukuni na Maroko, sun yi ta fafafawa ne, kuma har zuwa yanzu wahala suke sha.
Ita kuma Portugal tun a wasa na biyu ta san ta tsallake wasannin rukuni, sannan wasanta na zagaye na biyu ya zo mata da sauki, inda fa lallasa Switzerland da ci shida da daya.
Babban taimakon kasar Maroko shi ne zuciya da ’yan wasanta ke sakawa wajen buga wasa, wanda a kwallo duk kwarewarka, idan ka hadu ’yan dagiya, sai an tashi za a san inda aka kwana.
An samu haka lokacin da Real Madrid da Barcelona suke tashe, amma kungiyar Atlerico Madrid ta tsaya musu a wuya.
Kasar Portugal dai tana da zaratan ’yan wasa. Duk da cewa Cristiano Ronaldo ya yi sanyi, amma ba a wasa da irin shi, domin yana iya canja wasa cikin minti daya kacal.
A bangaren Maroko, fitattun ’yan wasanta su ne Hakim Ziyech na kungiyar Chelsea da Achraf Hakimi na PSG.
Sai dai za a iya cewa an fi sanin biyun ne kawai, amma sauran ’yan wasan ma baya ba.
Idan za a kwatanta fitattun ’yan wasa da gogewa, za a iya cewa Portugal ta fi Maroko.
Amma wani abu da yake fili, duba da wasannin baya a gasar, za a iya cewa Maroko ba ta da tsoro, kuma ’yan wasanta suna fafatawa ne bakin rai bakin fama.
Hakan ya sa wasu suke sa ran yau kasar Afirka za ta iya zuwa wasan kusa da karshe a karon farko a tarihin Gasar Kofin Duniya.
Amma kuma, cire Brazil da nasarar Ajantina a jiya za su sa Portugal su kara kaimi, domin za a iya cewa sun fara hango lashe kofin.
Yanzu dai nan da awa 20 miyar za ta kare kaf, daga nan sai mu san maci tuwon.