Marayun da aka yi garkuwa da su tare sa wasu mutum hudu a Abuja sun kubuta bayan shafe kwana tara a hannun ’yan bindigar.
Majiyarmu ta shaida mana cewa an sako marayun ne da almuru a kauyen Kpareke da ke Karamar Hukumar Koton-Karfe, a Jihar Kogi.
- Magidancin da ya nemi yada hoton tsiraicin matarsa ya shiga hannu
- Kotu ta raba auren shekaru 12 saboda saurin fushin mata
- Mutum 994 ne suka rasu a hadura a Abuja a 2020 —FRSC
Majiyar ta tabbatar wa Aminiya cewa an biya kudin fansa kafin a sako yaran, ta ce “Ba zan iya bayyana yawan kudin da aka ba su ba, amma bayan biyan kudin sun sako marayun da sauran mutanen.”
Wani daga cikin iyalan wanda aka yi garkuwa da su ya ce tabbas sai da aka biya kudi sannan aka saki ’yan uwan nasu, amma bai bayyana nawa aka bayar ba saboda dalilan tsaro.
“Sayar da kadarorinmu muka yi sannan muka aro kudi saboda sun ce idan muka wuce ranar Lahadi kashe su za su yi,” inji shi.
Kakakin ’Yan Sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar wa wakilinmu cewa an sako marayun tare da wasu mutum hudu.
Aminiya ta rawaito a kwanaki baya cewa ’yan bindiga sun kutsa gidan marayu na Racheals da ke kusa da Makarantar Sakandare ta Naharati a yankin Abaji, suka tisa keyar marayu da mai gadi da kuma wasu mutum hudu.