Galibi masu bukata ta musamman a Najeriya musamman yara kanana ba su cika samun gata ko ma mayar da hankali wajen zuwa makaranta ba.
A mafi yawan lokuta an fi barinsu a gida, wasu iyayen kuma ma har bara suke tura yaran su yi a kan tituna da kasuwanni.
- Kotu ta ba da belin mai luwadi da karamin yaro a Kano
- Buhari ya kori Shugaban Hukumar Samar da Ayyuka
Sai dai Fatima Yusha’u, marainiya mai shekara 11, nakasar rashin kafafun da take fama da ita, nisa da zafin rana ba su hana ta zuwa makaranta ba.
Bincike ha nunua saboda tsabar son makarantarta, Fatima kan yi rarrafen akalla kilomita daya kullum daga gida zuwa makarantarsu ta firamare.
“Ta kan yi rarrafe a wasu lokutan har zuwa makarantar tasu ita kadai, wani lokacin kuma ’yan uwa ko kawayenta, wani lokacin kuma Hedimastan makarantar ne ke rage mata hanya”, inji kakarta.
Hedimastan makarantarsu, Ahmadu Ali ya ce duk rintsi marainiyar ba ta yarda ta yi fashin makaranta, duk da cewa ba ta da keken guragu.
Yadda Fatima ta samu nakasa
Kakar gurguwar marainiyar, wacce a wurinta take zama, ta ce yarinyar ta fara rashin lafiya ne tare da mahaifiyarta jim kadan bayan haihuwarta.
Ana cikin haka ne mahaifin yarinyar ya saki mahaifiyarta, yana mai cewa ba zai iya ci gaba da biyan kudin maganinta da na diyar tata ba.
Kakar ta ce mahaifiyar Fatima ta rasu kimanin wata takwas da suka gabata kuma yanzu a hannunta take zama a unguwar Karofin Yashi a garin na Dan Shayin.
Labarin Fatima mai cike da tausayi, darasi da karfafa gwiwa ya fara bazuwa ne bayan wata jaridar intanet mai suna Arewa Agenda ta zakulo tare da tattaunawa da ita.
Fatima Yusha’u ’yar asalin garin garin Dan Shayi a Karamar Hukumar Rimin Gado da ke Jihar Kano.
Makarantarsu na cikin mawuyacin hali
Sai dai ita kanta makarantar da Fatima ke zuwa tana cikin halin ni-’ya-su saboda da kadan azuzuwan makarantar suka dara zama kango.
Yawancin silin da azuzuwan sun bubburme, kofofi da tagogin sun karairaye, sannan babu kujeru, babu allon rubutu da sauran kayan koyo da koyarwa.
Sakamakon rahoton da aka yi a kanta, zuwa yanzu akalla mutum uku ne suka yi alkawarin ba ta kyautar keken guragu don tallafa mata ta cika burinta na yin karatu.