✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maradona ya juya wa Ajantina baya a gasar cin kofin duniya na matasa

Shahararren dan kwallon Ajantina, Diego Maradona ya ce ya yanke shawarar ba zai goyi bayan kasar haihuwarsa Ajantina a gasar cin kofin duniya na ’yan…

 Diego MaradonaShahararren dan kwallon Ajantina, Diego Maradona ya ce ya yanke shawarar ba zai goyi bayan kasar haihuwarsa Ajantina a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da aka fara jiya Alhamis a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ba.
Maradona, wanda yanzu haka shi ne jakadan Dubai a wasan kwallon kafa, ya shiga yin gaba Ajantina ne tun bayan korar karen da ta yi masa a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar a watan Yulin shekarar 2010 saboda rashin tabuka abin-a-zo-a-gani a wancan lokaci.
dan kimanin shekara 52, Maradona ya taba taimakawa Ajantina wajen lashe kofin duniya a shekarar 1986.
Haka kuma a watan Yulin shekarar 2012 ce kungiyar kwallon kafa ta Al-Wasl da ke Dubai ta yi hannun riga da shi bayan ta sallame shi a matsayin kocinta.
“Zan goyi bayan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ne a gasar amma ba Ajantina ba saboda sabanin da ke tsakanina da ita”, inji Maradona a lokacin da yake hira da manema labarai.
A jiya Alhamis ne aka fara gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 17 inda Brazil ta fara kece raini da Slobakia  a wasan farko.