✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maraba da shekarar 2020 Miladiyya

Allah cikin ikonSa, kamar jiya ake zumudin shigowar sabuwar shekarar  2019, shekarar  da wannan fili ya yi fatar Allah Ya sa ta fi ta 2018…

Allah cikin ikonSa, kamar jiya ake zumudin shigowar sabuwar shekarar  2019, shekarar  da wannan fili ya yi fatar Allah Ya sa ta fi ta 2018 da aka yi ban-kwana da ita ta kowane fanni, zaman lafiya da karuwar arziki  ne, a kan siyasa ko zamantakewa ne da sauran batutuwan da za su kawo ci gaban al’umma. Sai ga shi har waccan shekara ta kare, sabuwar shekarar 2020, ta kama har an yi kwana 3 a cikinta yau. Allah Ka rabautar   da   mu   don   ganin   karshen   wannan   shekara  cikin   imani   da koshin lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadatar zuci, amin summa amin.

A bisa  al’ada idan irin wannan lokaci ya zagayo, mahukunta da ’yan   kasa   kan   yi   waiwaye   adon   tafiya   a kan   shekarar   da   ta   gabata, sannan su yi hasashen me sabuwar shekarar za ta zo da su, wane irin sauki ko matsi za a samu a cikin rayuwar ’yan kasa a kan tattalin arziki da rigingimu iri daban-dabam da kasar ta dade tana fama da su da sauran matsaloli?

Shekarar da ta gabata (2019) ta kasance mai cike da ruguntsumi iri-iri, masu dadi  da marasa dadi, ga zaben da ya ba Jam’iyyar APC mai mulki sake komawa kan karagar mulki a karon farko a zaben kasar da aka yi a bara. Batun rashin tsaro irin na garkuwa  da mutane don neman kudin fansa da   hare-haren ’yan bindiga da rikicin Boko Haram da a bara aka samu shekara goma cif ana fama da shi musamman a jihohin Arewa maso Gabas da yaki  da cin hanci  da  rashawa  da rashin  ayyukan yi musamman a tsakanin matasa da matsin tattalin arziki, duk sun ci gaba a barar. Kodayake alhamdulillah, dukkan wadannan batutuwa da na anbata a sama, musamman matsalar tsaro ana samun saukin aukuwarsu, amma ba cewa na yi an kawo karshensu ba.

Kasancewar a barar, kasar nan ta cika shekara 20 ana mulkin dimokuradiyya ba kakkautawa, kuma kamar yadda na fadi tun farko cewa a barar ce aka yi babban   zaben kasar nan, amma zabubbukan duk da aka yi ba wanda za ka ce an yi shi cikin kyakykyawan tsari irin wanda mulkin dimokuradiyya ya shimfida, idan aka yi la’akari da irin yadda kowace jam’iyya daga cikin manyan jam’iyyun kasar nan biyu, wato APC mai  mulki da babbar jam’iyyar adawa wato PDP, kowace ta yi abin da take so bisa ga damar da take da ita. Kada ka yi batun irin ta’asar kashe-kashen rayuka da zubar da jini da lalata dukiyoyin al’umma da aka aikata a zabubbukan jihohin Bayelsa da Kogi da aka yi ranar 16 ga Nuwamban bara, kuma duk da irin ta’asar da aka yi, sai  ga shi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana taya gwamnoninsa da aka ce sun ci zabubbukan murna.

A barar fadar Shugaban Kasa ta shiga rudani daga irin yadda wadansu da ake kira kabarl (Cabal) ko mu ce masu-hana-ruwa -gudu,  walau  a tsakanin Shugaban  Kasar   da  Mataimakinsa,  ko  tsakanin Shugaban Kasar da Uwargidansa, Hajiya A’isha Buhari. Kabal din sun ci nasarar yadda aka cire wadansu daga cikin masu taimaka wa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi   Osinbajo, ta hanyar  dauke  wadansu daga cikin hukumomi da cibiyoyi da suke karkashin kulawar mai riko da ofishi irin nasa, baya ga wadanda aka ce kafin ya zartar da wani abu sai ya nemi izinin Shugaban Kasar.

An yi   zargin wadancan  kabal  din, sun dukufa a kan yin abin da suke yi, don kawo kancal a kan burin da ake zargin Mataimakin Shugaban Kasar yake da shi na neman takarar Shugabancin Kasar nan a shekarar 2023, in Allah Ya kai mu.

Haka kuma dimokuradiyya a kasar nan ta dauko asali ne tun daga irin ja-in-jar da Gwamnan   Jihar  Zamfara na  wancan   lokaci   Alhaji   Abdul’aziz   Yari  ya  yi  uwa,   ya yi makarbiya ya hana sauran ’yan takarar   Gwamnan Jihar da mabiyansu sakat cikin zabubbukan fitar-da-gwanin da za su tsaya   wa jam’iyyarsu  ta  APC takara a zaben bara a jihar.

Shari’ar da aka yi ta tafkawa tun daga kotunan Jihar Zamfara, har zuwa Kotun Koli shi ya kawo Jam’iyyar PDP ta tsinci dame a kala, inda Jam’iyyar APC ta tashi a tutar babu.

A barar an samu amincewa da kasafin kudin bana na Gwamnatin Tarayya da ya  fara  aiki a farkon bana bisa ga jajircewar   Majalisar Dokoki ta Kasa, abin da aka dade ba a samu ba.

Kodayake an shigo sabuwar shekarar da   sauran matsaloli irin na batun tsaro da na matsin tattalin arzikin kasa, babban fatar da ’yan kasa suke da ita a sabuwar shekarar, musamman na jihohin Arewa shi ne su gani a kasa, duk kuwa da tashin farashin kayayyaki da aka fara samu a sabuwar  shekarar a  dalilin karin harajin kayayyakin bukatu (BAT) da karin albashin da ake sa ran zai kankama a cikin wannan sabuwar shekara. Allah Ya maimaita mana.