A ranar 6 ga Oktoba, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da sanarwar amincewarta da samar da riga-kafin zazzabin cizon sauro.
Wannan babban abin tarihi ne, ganin cewa, zazzabin cizon sauro ya kasance daya daga cikin cututtukan da suka fi kamari a duniya, inda aka samu rahoton wadanda suka kamu da cutar sun kai miliyan 229 a duk duniya.
A cikin wannan adadi, a Afirka ce ke da kashi 94 cikin 100 na masu kamuwa da wannan cuta.
Babu shakka abin murna ne da aka samu wannan riga-kafi a yanzu.
Cizon sauro ne ke haifar da zazzabin mai yaduwa kuma a can baya an kasa samun riga-kafinsa, duk da cewa akwai nau’o’in zazzabi kusan 100 masu rikitarwa.
Wannan riga-kafin mai suna RTS, S/ASO1 (RTS, S), mai tambarin Moskuirid, an fara aikin samar da shi ne tun a shekarun 1980 kuma an shirya shi ne musamman domin ya yaki nau’in kwayar cutar mafi hadari ta plasmodium falciparum, wadda ta fi yawaita a Afirka.
Kamfanonin magunguna na PATH Malaria Baccine Initiatibe da GladoSmithKlinene suka samar da shi tare da tallafi daga Gidauniyar Bill and Melinda Gates, kuma shi ne na farko daga kusan gomman da wadansu masu neman samar da riga-kafin suke kokarin samarwa.
Dole ne a jinjina wa ayarin masana kimiyya wadanda suka yi gwagwarmayar gaske don habaka wannan riga-kafin, bayan aiwatar da gwaji ga mutum dubu 800 a kasashen Ghana da Kenya da Malawi kuma aka samu sakamakon ingancinsa da kashi 40 cikin 100.
Sun yi nasarar samar da riga-kafi mai rahusa kuma mai matukar inganci, idan aka yi la’akari da matsayin tattalin arzikin kasashen da cutar zazzabin cizon sauro ta fi kamari ke ciki.
Sun kuma samar da riga-kafi mai inganci kuma marar nakasu ko cutarwa ga wadanda za su yi amfani da shi.
Duk da cewa, wannan riga-kafi na iya magance cutar da kashi 4 cikin 10 na wadanda suka kamu da zazzabin cizon sauron, ko 3 cikin 10, abin alfahari ne kuma wannan zai bude hanyar samar da wasu nau’o’in rigakafin nan ba da jimawa ba.
A kowace shekara, zazzabin cizon sauro yana kashe kusan mutum dubu 400. A shekarar 2019 kadai, ya kashe mutum dubu 260 a Afirka.
Don haka ba abin mamaki ba ne cewa, labarin wannan riga-kafi da aka amince da shi ya saka mutane farin ciki a nahiyar.
Yayin da har yanzu wannan farin ciki ke ci gaba, dole ne hukumomin kiwon lafiya a Najeriya su yi dabarun yadda za a yi amfani da riga-kafin cikin hanzari a matsayin dabarun kula da zazzabin cizon sauro na kasa.
Bayan amincewa da wannan rigakafin, yanzu hukumomin kiwon lafiya na duniya za su yanke shawarar kudi don kaddamar da riga-kafin.
Wannan wani muhimmin mataki ne idan aka yi la’akari da cewa, kasashen da suke fama da cutar zazzabin cizon sauro a duniya galibi matalauta ne.
Dole ne Gwamnatin Tarayya ta sanya Najeriya cikin samun wannan rigakafi da zarar ta samu, ta tabbatar an rarraba ta cikin sauri a duk fadin kasar nan.
Kuma bayan wannan, ya kamata Najeriya ta binciko wasu hanyoyin sayen lasisin don ta iya samar da riga-kafin a cikin kasar nan. Wannan zai tabbatar da samun saukin allurar a gaba.
Misali, a Senegal tuni an dauki Kamfanin BioNTech a matsayin cibiyar samar da riga-kafin mRNA, ba don Coronavirus kawai ba, amma don zazzabin cizon sauro da tarin fuka.
Kasancewar cibiyar riga-kafin cutar a Senegal, ba shakka za ta taimaka wajen sanya wannan riga-kafin a nahiyar da sabuwar Cibiyar Magunguna ta Afirka.
Cibiyar za ta kasance a karkashin Tarayyar Afirka da za a kaddamar a watan Nuwamba tare da burin inganta samfurin magungunan a nahiyar, na iya zama wani muhimmin abu wanda zai taimaka wajen daidaita abubuwan da suka shafi kiwon lafiyar jama’a.
Amfanin irin wannan hadin gwiwar yana da yawa.
Ba wai kawai zai taimaka wajen sanya wannan riga-kafin ta zama mai araha ba, har ma zai samar da ayyukan yi da damar bincike ga kasar tare da habaka karfin masana kimiyya mazauna da masu nazari.
Haka nan zai habaka cibiyoyin bincike da yawa a cikin kasar.
Amma kafin hakan ya faru, dole ne kasar ta kasance cikin tsayayyen yanayi don jawo hankalin masu saka hannun jari.
Don haka, dole ne gwamnati ta samar da tsare-tsaren da za su taimaka kuma ta samar da yanayi mai kyau don wannan ci gaban.
Muna rokon Gwamnatin Tarayya ta shiga cikin irin wannan hadin gwiwa wanda zai habaka rayuwar ’yan Najeriya da samar da guraben ayyukan yi da habaka tattalin arziki da inganta cibiyoyin bincike na kasa don jagorantar ci gaban kasar nan wajen samar da wasu riga-kafin.
Duk wani abin da zai taimaka wajen kawar da cutar zazzabin cizon sauro dole ne a karfafa shi.