✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manzon Allah (SAW): Malamin tarbiyya da babu kamarsa

Allah ba Ya tozarta ladan wanda ya kyautata aiki.

Hudubar Imam Khalid Alkarra Alawi, Masallacin Abu Musa Al-Ash’ari, Kusaim – Unaizah, Saudiyya Fassarar Salihu Makera

Huduba ta farko Hamdala da mukaddima.

Bayan haka, ku bi Allah da takawa ya ku bayin Allah! Domin ku samu ilimi da fahimta da gyaruwan al’amura da kuma tsarkakake ayyuka.

“Ya ku wadanda suka yi imani! Idan kun bi Allah da takawa, Zai sanya muku mararraba (da tsaro) kuma Ya kankare kananan zunubanku daga barinku.

“Kuma Ya gafarta muku. Kuma Allah ne Ma’abucin falala mai girma.” (Anfal:29).

Ya ku Musulmi! Ku biyo mu, zuwa zauren malami na farko, mafi iya tarbiyya, Annabin rahama da shiriya, domin mu koyi wani abu kan manhajarsa wajen yin tarbiyya da koyarwa da kusantarwa da fahimatrwa.

Wannan malami da Allah Ya sanya sonsa a zukatan mutane, Ya haskaka zukata da shi, shi ne Ya fitar da mu daga duffan zalunci zuwa ga hasken imani.

Shi ne malamin da Allah Ya aiko shi a matsayin rahama da amana ga dukkan halitta, kuma hujja abin koyi ga halitta baki daya (Sallallahu Alaihi Wasallam).

“Lallai ne hakika, Allah Ya yi babbar falala a kan muminai, domin Ya aika a cikinsu Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinSa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su Littafi da hikima, kuma lallai, sun kasance daga gabani, hakika suna cikin bata bayyananniya.” (Al-Imrana: 164).

Shi ne abin koyinmu, musamman a wannan lokaci da mutane suke ruduwa da tarbiyyar ’yan Falsafar Turai ta Yamma, suke gafala daga kyakkyawan koyi na hakika!

Me ya fi kyau daga maganar Mu’awiyya bin Alhakam (RA): “Ban taba ganin malami (mai koyar da mutane kyawawan halaye) a gabaninsa da bayansa da ya fi iya koyarwa daga gare shi (SAW) ba.”

Ya bayin Allah! Wanda ya yi zaton zai sha ruwan tarbiyya da ilimantarwa ba daga tafkinsa ba, hakika ya kauce hanya!

Don haka babu abin da ya fi dacewa da mu face mu nemi sanin shiryarwarsa da bibiyar Sunnarsa (SAW).

Ga wasu misalai na Malamin Shiriya (SAW) gare ku wajen yin tarbiyya da kusato da mutane da fahimtar da su.

Daga ciki akwai cewa shi (SAW) yana cusa wa mutane son ilimi, yana mai bayyana musu falalar ilimi da nemansa ta yadda mai neman ilimin zai ji a jikinsa cewa yana tsananin bukatar ilimin.

An karbo daga Abu Huraira (RA) cewa: “Wani mutum ya shiga masallaci ya yi Sallah, sannan ya zo ya yi sallama ga Manzon Allah (SAW).

“Sai Manzon Allah (SAW) ya amsa masa sallamar, sannan ya ce: “Ka koma ka yi Sallah, domin ba ka yi Sallah ba.”

Sai mutumin ya koma ya sake Sallah kamar yadda ya yi Sallar a baya, sannan ya dawo ga Annabi (SAW). Sai ya ce: “Ka koma ka yi Sallah, domin kai ba ka yi Sallah ba.”

Har mutumin ya yi haka sau uku. Sai ya ce: “Na rantse da Wanda Ya aiko ka da gaskiya ban iya fiye da yadda na yi ba. Don haka ka koyar da ni!”

Sai Manzon Allah (SAW) ya koyar da shi siffar Sallar gaba dayanta. Ya bambance wajen koyar da shi tun daga farko har sai da shi kansa mutumin ya ji yana bukatar haka.

Me zai hana mu rika amfani da wannan salo wajen koyar da dalibanmu ko da ta hanyar jefa musu tambayoyi ne?

Kuma yana daga cikin yadda ya sha bamban wajen koyarwarsa (SAW), nuna kula da koyarwar: “An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Wani lokaci Annabi (SAW) yana zaune yana magana da mutane, sai wani Balaraben Kauye ya zo, sai ya ce: “Yaushe ne Sa’a (Tashin Kiyama) ?”

Sai Manzon Allah (SAW) ya ci gaba da magana. Wadansu mutane sun ce ya ji abin da ya ce, amma sai ya ki abin da ya fadi.

Wadansu suka ce: “A’a bai ji ba, har sai da ya kare maganarsa. Sai ya ce: “Ina wanda yake tambaya game da Sa’a?

Sai ya ce: “Ga ni ya Manzon Allah!” Ya ce: “Idan aka tozarta amana, to a jirayi Sa’a.

Sai ya ce: “Ta yaya za a tozarta ta?” Ya ce”

“Idan aka bayar da al’amari (shugabanci) ga wadanda ba su cancace shi ba, to a jira Sa’a.”

Annabi (SAW) bai mance ba kuma bai yi watsi da mai tambayar ba, a’a wani al’amari ne da yake son fito da hakikaninsa, wannan kuwa dabi’a ce madaukakiya ta Manzon Allah (SAW).

Akwai bambanci a tsakanin wannan da wanda ba ya bayar da kafa ta a yi wata tambaya.

Kuma daga cikin inda ya kebanta wajen koyarwarsa (SAW) akwai karfafa mai nema da yabo gare shi.

Misali a lokacin da Abu Huraira (RA) ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: “Wane ne wanda zai fi samun sa’adar cetonka a Ranar Kiyama?”

Sai Manzon Allah (SAW) ya ce masa: “Hakika ya Abu Huraira da ma na yi tsammanin babu wanda zai riga ka tambayata kan wannan Hadisi, saboda abin da na gani gare ka na kwadayinka a kan Hadisin: Wanda zai fi samun cetona a Ranar Kiyama shi ne wanda ya ce: “La ilaha illallahu yana mai ikhlasi a cikin zuciyarsa.”

Kuma Manzon Allah (SAW) ya tambayi Ubayyu bn Ka’ab (RA) ya ce: “Ya Abu Munzir wace aya ce a cikin Littafin Allah ta fi girma a wurinka?

Ya ce: “Sai na ce “Allahu la ilaha illahuwal hayyul kayyum.” Sai ya bugi kirjina ya ce: “Wallahi ilimi yana gaishe ka, ya Abu Munzir.”

Ya kai malamin tarbiyya mai girma! Zo mu dubi halin Abu Huraira da Abu Munzir a lokacin da suke jin wannan yabo mai dadi.

Wannan shaida ce ta koyarwar Annabi (SAW), kuma za ta ingiza su ga kara kwadayi da dada kula.

Hakika lallai al’amarin bai takaita ga kalmar yabo kadai ba, ko manuniya kan karfafa gwiwa, tana daukaka dalibi zuwa ga matsayi na kara kwadayi da ijtihadi.

Ya bayin Allah! Daga cikin koyarwarsa (SAW) akwai karfafa wa dalibansa su yi kokarin fito da hukunci ko gano wani abu ta hanyar sa su yi dogon tunani domin gano lamari.

Misali wata rana Annabi (SAW) ya tambayi sahabbansa ya ce: “Lallai daga cikin itatuwa akwai wata itaciya da ganyenta ba ya faduwa, lallai ita misalinta misalin Musulmi ne, ku ba ni labarin wecce ce ita.”

Sai mutane suka rika tunani kan itatuwan daji har sai da Ibn Umar (RA) ya ce: “Lallai ita ce dabino.”

Kuma a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya hana saya ko sayar da ’ya’yan itace har sai sun kosa kuma an bayyana mai kyau da marar kyau sai ya ce: “Da me dayanku zai karbi dukiyar dan uwansa?”

Kuma a lokacin da sahabbai suka ce ga Manzon Allah (SAW): “Shin dayanmu zai biya bukatar sha’awarsa kuma ya kasance yana da lada?”

Sai (SAW) ya ce: “Ba ku gani da zai sanya ta a haram, shin zai kasance akwai zunubi a kansa? To haka idan ya sanya ta a cikin halal sai ya samu lada!”

Ka yi nazari – Allah Ya yi maka albarka- kan yadda Annabi (SAW) ya sanar da sahabbansa illlar hukunci da zato da muhimmancin kiyasi da kuma takribin abubuwa.

Ya Ubangiji! Ka ilimantar da mu abin da zai amfane mu, kuma Ka amfanar da mu abin da Ka ilimantar da mu.

Ka azurta mu da furta magana mai kyau da I’itikadi da aiki mai kyau. Ina fadin abin da kuke ji ina mai neman gafarar Allah a gare ni da ku da kuma sauran Musulmi daga kowane zunubi, lallai Shi Mai gafara ne Mai jin kai.

Huduba ta Biyu: Hamdala da mukaddima.

Ya bayin Allah! Maganarmu ba ta gushe ba tana dacewa kan shiriyar Annabi (SAW) a cikin tarbiyya da ilimantarwa.

Abu ne mai kyau mu kwaikwayi abin da ya bar mana gado, mu bi gwadaben da ya bi a cikin mu’amalolinmu da kula da ’ya’yanmu a gidajenmu da kuma dalibanmu a makarantu da jami’o’i.

Ya ku malamai da masu tarbiyya! Daga cikin koyarwarsa (SAW) akwai dabbaka aiki.

A gaban sahabbansa da yawa yakan yi alwala a gaban mutane idan ya gama, sai ya ce: “Wanda ya yi alwala irin wannan alwala tawa, sannan ya yi Salllah raka’a biyu bai yi tunanin duniya a cikin ransa ba, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.”

Kuma ya kasance yakan yi Sallah a kan mumbari yana mai cewa: “Ya ku mutane! Lallai ni na yi haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata.”

Me ya fi wannan kyan koyarwa, mai ya fi shi saukin fahimta? Bayin Allah daga cikin abin da ya kebanta da shi (SAW), akwai saninsa ga kudirorin dalibansa da kiyaye bambance-bambancen da ke tsakanin kowanensu.

Daga cikin cikar saninsa ne ya ce: “Mafi tausayin al’ummata ga al’ummata shi ne Abubakar, kuma mafi tsananinsu wajen kiyaye al’amarin Allah shi ne Umar, mafi kunya a cikinsu Usman, mafi sanin halal da haram Mu’azu bn Jabal, mafi sanin rabo gadonsu Zaid bn Sabit, mafi iya kira’arsu Ubayyu.

Kowace al’umma tana da amintaccenta, to, amintaccen wannan al’umma shi ne Abu Ubaida bin Jarrah.” Albani ya ce, Hadisi ne sahihi.

Kuma Mu’awiyya bn Hakam As-Sulami (RA) ya bayar da labari cewa: “Wani lokaci ina cikin yin Sallah tare da Manzon Allah (SAW), sai wani ya yi atishawa, sai na ce masa: “Yarhamukallahu” sai mutane suka rika harara ta, sai na ce don me kuke kallona, sai suka bubbuga hannuwansu a kan cinyoyinsu.

Da na ga suna nuna in yi shiru, sai na yi shiru. Da Manzon Allah (SAW) ya idar zai tafi sai ya kira ni.

Da Babana da Mahaifiyata, ban taba ganin malami irinsa a gaba ko a bayansa ba da yake kyautata koyarwa. Wallahi bai buge ni ba, bai tilasta ni ba, bai zage ni ko ya bace ni ba.

Iyaka ya ce: “Lallai sallarmu wannan ba ya dacewa a furta wani kalami na mutane. Sai dai a yi takbiri da tasbihi da karatun Alkur’ani.”

Ashe bai dace da mu ba mu kwaikwayi manhajarsa mu bi shiriyarsa (SAW)?

Ya ’yan uwana! Wannan kadan ne daga cikin dimbin abin da Sunnar Annabi (SAW) ta zo mana da su daga shiriyar Zababbe (SAW) da hanyarsa ta koyarwa, don haka ya ku iyaye da malamai, mu yi koyi da Annabinmu (SAW), mu bi duga-dugansa, kuma Allah ba Ya tozarta ladan wanda ya kyautata aiki.