Alal hakika, irin azabtarwar da wadansu Musulmi suka fuskanta a farkon lokacin kira ba ya iya misaltuwa. Daga cikin wadanda suka fuskanci kalubale akwai masu rauni wadanda suke bayi ne ba ’yantattu ba. Na gaba-gabansu shi ne Bilal bin Rabah wanda bawa ne na Umayyatu bin Rabi’ah, akwai Yasir da kuma Sumayyah. Malaman tarihi sun ce Sumayyah ita ce wadda ta fara shahada a Musulunci tare da mijinta. Manzon Allah (SAW) wata rana ya zo wucewa sai ya ga ana azabtar da su, sai ya ce: “Ku yi hakuri iyalan gidan Yasir, lallai Aljannah ce makomarku.” (Imam Ahmad). Haka nan Khabbabu bin Arsu da makamantansu duk sun sha wahala iri-iri amma duk da haka ba su bar addinin Allah ba.
A yayin da da’awar Musulunci ta fara nisa sai Kuraishawa suka tura tawagar manyan mutane daga cikinsu zuwa ga Baffan Annabi (SAW), wato Abu Dalib. Suka fara da nuna wa Abu Dalib irin matsayinsa a cikinsu; suka ce kai Abu Dalib hakika mutum ne mai daraja da kuma shekaru, muna so ka hana dan dan uwanka kiran da yake yi, kuma ya daina zagin allolinmu. Abu Dalib nan take ya isar da sakonsu zuwa ga Manzon Allah (SAW). Sai Annabi (SAW) ya amsa musu da cewa ko da za su dora rana a hunnunsa na dama da hagu (don azabtarwa) ba zai daina wannan aiki na kira zuwa ga Allah ba, ko da kuwa za a hallaka shi. Abu Dalib ya karfafa shi ya kwantar masa da hankali ya kuma ba shi tabbacin goyon baya. Bayan wani lokaci suka sake dawowa da wata bukatar mai nauyi cewa za su bai wa Abu Dalib wani matashi mai suna Ammaratu bin Walid bin Mughira a matsayin fansa don shi kuma ya ba su Annabi (SAW). Sai Abu Dalib ya ce, “Kaitonku! Abin da kuke so ke nan, ta yaya zan rike muku da in ciyar muku da shi ku kuma ku kashe mini nawa dan?”
Haka dai aka yi ta gwagwarmaya a tsakanin Musulmi wadanda suka amsa kiran Annabi (SAW) da kafiran Makka wadanda suka daura damarar sai sun dakile wannan kira ta hanyar musgunawa da kokarin hallakar da masu imani. Kuma duk da wannan tsattsauran mataki da suka dauka hakan bai hana wadansu baki da suka samu labarin abin da ke faruwa a garin Makka su taho don gani da idonsu da kuma sauraron irin sakon da Annabi (SAW) yake tafe da shi ba. Daga cikinsu akwai irin su Abu Zarri Al-Ghifari da Abu Musa Al-Ash’ari da makamantansu da suka taho daga garuruwansu don su ji irin sakon Annabi (SAW), kuma ba su gushe ba sai da suka karbi Musulunci.
Alal hakika, ganin irin karbuwar da Musulunci yake yi a tsakanin mutane, cikinsu har da baki, ya sanya hankalin kafiran Makka ya kara tashi, kuma suka kara kaimi wajen tsangwama da musguna wa Musulmi da kuma kokarin aika wakilai wajen garin Makka don bata addinin Musulunci da hana shi yaduwa a waje. Su ma Musulmi a nasu bangaren sai suka fara tunanin yadda za su samar wa kansu mafita daga ci gaba da azabta su da ake yi da kokarin a katse hanzarin mutanen da ke wajen Makka don kada su fahimci sakon da Annabi (SAW) ya zo da shi.
DARASI NA SHA HUDU
MUSHIRIKAI SUN NEMI ANNABI (SAW) YA KAWO MUSU AYA
Wata rana sai suka taru suka aika a nemo Annabi (SAW). Annabi (SAW) ya zo da saurinsa a kan kiran da suka yi masa a zatonsa ko shiryuwarsu ta zo ne, ya samu manyan masu adawa da kiransa suna zaune kusa da Ka’aba majalisinsu na manyan Kuraishawa sai suka ce masa: “Lallai Kai ne ka ba mu labarin Annabawa suna zuwa da aya, ka ce Annabi Musa ya zo da sanda, ga Samud kuma taguwa, Isah kuma yana tayar da matattu, to kai ma yanzu muna so mu ga taka ayar in dai kai Manzo ne.”
Su a zatonsu Annabawa suna da ikon yin mu’ujiza don karan kansu, ba su san Allah ne Yake hore musu ita ba, ma’ana sai da yardar Allah. Sun nemi ya sa dutse ya yi tafiya ko ya shimfida musu wani gari wanda yake cike da koramu da gonakai da lambu, Allah ya wadata shi ya zo da taskar zinare da azurfa don bai kamata a ce yana tafiya kasuwa (nema) ko sanya tufafi irin nasu ba tun da Allah ne Ya aiko shi, ko ya zo da Mala’iku su shaidar cewa shi Manzo ne, ko ya kifo musu sama a kansu shi ne fadar Allah:
Bayan sun nemi wadannan abubuwa hakika ya roki Allah kan a nuna musu aya wadda za ta sa su yi imani sai Allah Ya aiko Mala’ika Jibril (AS) ya tambayi Annabi (SAW) shin a nuna musu ayoyi ne amma da sharadin idan ba su yi imani ba za a halakar da su da wata azaba wadda ba a taba yi wa wata halitta ba gabaninsu ko kuma kar a nuna musu amma a bade musu kofofin tuba da rahama. Sai Manzo (SAW) ya zabi a bade musu dai kofofin tuba da rahamar.
Sun yi rantsuwa cewa idan ya zo musu da abin da suka nema za su yi imani, tun da ya yi musu zabi sai ya nuna nusu cewa shi fa mutum ne Manzo ba shi da ikon yin wata mu’ujiza sai abin da Allah Ya so, Shi kadai Ya kebanta da haka Shi ne fadar Allah Ta’ala yana karfafa maganarsa:
Allah Ya san ba za su yi imani ba a lokacin ko da an saukar da abin da suka nema shi ne fadarsa bayan sun nemi ya tayar da matattunsu ciki har da kakansu su da shi wato Ka’ab dan Lu’ay wai idan ya tashi duk abin da ya gaya musu za su yarda don shi mutum ne mai gaskiya.
Lallai wadannan mutane ba su ganin gaskiya sun manta irin gaskiyar da Annabi (SAW) yake da ita har suka shede shi a kan haka.
Allah ya tabbatar wa Annabi (SAW) da cewa ba za su yi imani ba a wannan lokacin ko da an aikata abin da suka nema na sauko da Mala’iku, da tayar da matattu da yi musu magana shi ne fadarsa:
Kuma shi ne fadarsa a suratur-Ra’adu aya ta 31.
Wannan abu da ya faru na rashin amsawar Annabi ga abin da suka nema don gudun azaba a kansu, sai su kuma suke ganin gazawa ce, haka ya kara musu kwarin guiwa na kara kaimi don su tabbatar wa mutane gazawarsa, sai a ki yin imani da shi. Don haka sai suka sake tunkarar sa suka ce, “To shin akwai wata aya wadda za ta tabbatar mana kai Manzon Allah ne?”
A nan sai Annabi (SAW) ya sake rokon Allah da Ya nuna musu aya, sai ko Allah Ya amsa masa Ya kuma nuna musu wata babbar aya shi ne tsagewar wata. Watan ya tsage biyu ne kuma ya rabu rabi a kan dutsen Abu Kubaisa rabin kuma na kan na bayansa, Kuraishawa sun ga wannan mu’ujiza baro-baro har sai da suka hango dutsen hira’i wanda yake wajen garin Makka don haske. Kuma Manzo (SAW) ya ce musu “KU SHAIDA’
Wannan abu karara yake kuma aka dauki wani lokaci mai tsawo a haka sannan ya hade ya koma yadda yake amma taurin kai da son zuciya ya rinjaye su suka ce ai wannan sihirin Abu Kabsha ne, Muhammad ya sihirce ku sai wani daga cikinsu mai tunani ya ce to idan ku ya sihirce ku shin ya sihirce dukkan mutane ne? Ga ayarin matafiya nan idan sun iso ku tambaye su, sai suka iso shi ne suka tambaye su ko sun gani? Matafiyan suka ce hakika sun gani. Sai dai kekashewar zuciya, girman kai, kafirci da son rai ya hana mushirikan Makka yin imani.
Ashe wannan shimfida ce a kan mu’ujizar da za ta faru a gaba kadan.
Za mu ci gaba insha Allah.