Yakin Sulasil
Bayan gama wannan yaki Manzon Allah (SAW) ya yi wata hikima ya aike wa Larabawan Sham runduna don ya hana su kada su zama mataimaka ga Rumawa su tsaya bangarensu. Ya aika musu Amru dan Al’as tare da sahabbai 300 da mahaya 30. Dama kakarsa (Amru) ’yar daya daga kabilunsu ce, idan kuma sun ki ya koyar da su darasi a kan tsayawa bayan Rum. Da ya kusa kaiwa ya samu labarin suna da jama’a masu dimbin yawa don haka sai ya aike wa Manzon Allah (SAW) yana neman a karo masa mutane, an kara masa mutum 200 a karkashin jagorancin Abu Ubaida Amir dan Jarrah (RA), amma shi Amru ne shugaba na game, shi yake jan Sallah, sun isa garuruwan suka kai hari sai mutanen suka gudu suka warwatsu.
Wannan yaki ya faru a wata daya bayan na Mu’uta ne.
Darasi na Arba’in da Uku
Bude Makka
A cikin watan Sha’aban shekara ta 8 Bayan Hijira, Kuraishawa da Banu Bakri da suke karkashin kariyarsu sun karya yarjejeniyar aminci da aka yi a Hudaibiyya, dalili shi ne Banu Bakri sun kai hari da dare ga Banu Khuza’a wadanda suka shiga karkashin kariyar Musulmi a lokacin yarjejeniyar Hudaibiyya, sun kashe mutum 20 suka kwashe ganima kuma suka kora su har cikin Makka suka yake su. Kuraishawa sun taimaka musu da mayakansu da makamai a asirce.
Ya kasance a Jahiliyya akwai daukar fansa na zubar da jinin junansu a can baya. Jinanai a tsakanin Bakri da Khuza’a. Da Musulunci ya zo wutar ta mutu, mutane masu yawa ne suka shiga Musulunci daga banu Khuza’a.
Wannan labari ya kai wa Manzon Allah (SAW), sai ya ce “Wallahi sai na hana muku daga abin da na hana kaina.”
Mugun aikin da Kuraishawa suka aikata ya dame su sai suka tura Abu Sufyan ya je ya sake jaddada yarjejeniyar wurin Manzon Allah (SAW) ya kuma kara mata lokaci. Da ya isa ya sauka wurin ’yarsa Ummu Habiba ya nufi shimfidar Annabi (SAW) zai zauna, sai ta yi maza ta nade. Sai ya ce ba ki son in zauna a shimfidar ce ko ni ne ba ki bukatar gani? Sai ta ce wannan shimfidar Manzon Allah (SAW) ce kai kuma mushiriki ne najasa, ya ce wallahi sharri ya same ki a bayana.”
Manzon Allah (SAW) ya shigo, sai Abu Sufyan ya yi masa magana ya yi shiru. Sai ya tafi wurin Abubakar (RA) ya nemi ya je ya yi wa Annabi (SAW) magana. Ya ce ba zai yi ba. Sai ya tafi wurin Umar (RA) shi ma ya ki, kuma ya kausasa masa magana daga nan ya wuce wurin Aliyyu (RA) shi ma ya yi uzuri ya ce ya nemi mutane. A wurin mutane ma babu mashiga domin sun gane kafiri ba abin amincewa ba ne, wannan kin karbar hanzari da Musulmi suka yi nasara ce ga Musulunci.
Manzon Allah (SAW) ya yi shirin fita zuwa Makka don ya bude ta, amma sahabbansa na kusa da manyansu kadai suka san da wannan, sun yi taka-tsantsan suka boye wannan sirri don kada Kuraishawa su san da zuwansu, don ma ya kara juya tunanin masu zato sai ya aiki Abu Kattada a farko farkon Ramadan wani gari Idum don a zaci can ya nufa. Manzon Allah (SAW) ya wakilta Abu Zarri a Madina kuma ya nemi sahabbai da Musulmin da suke kewaye da Madina su shirya, ya hada runduna ta mutum dubu 10, suka fita zuwa Makka, ya yi addu’a ya ce “Ya Allah! Ka rike ’yan leke da masu ba da labarai har sai mun tumbatsa garuruwanta (Makka). Suka nufi Makka ranar 10 ga Ramadan shekara ta 8 Bayan Hijira.
Sai Hatib ya rubuta ya aike wa Kuraishawa batun zuwan Annabi (SAW), sai dai Allah Ya sanar da shi (SAW), ya aiki Zubair da Aliyu da Mikdad suka riski matar da ya ba takardar a Khakh. Da farko ta musanta, amma da ta ga lallai suna da tabbas a kan haka, sai ta ciro ta ba su. Da aka nemi Hatib dalilin haka sai ya ba da uzirin iyalinsa da ’yan uwansa da ’ya’yansa suna cikin Makka, yana nufin su saka hannu wurin kare su don ba su da wani makusanci da zai kare su kuma ba ya yi ridda ba ne ko yarda da kafirci. Umar ya nemi izinin ya sare wuyansa don wannan yaudara ce da munafunci, sai Manzon Allah (SAW) ya ce ai ya halarci Badar me ya sanar da kai Allah Ya yi tsinkaye a kan ma’abuta Badar, Ya ce ku aikata abin da kuka so hakika an gafarta muku. A nan sai Umar ya ce Allah da ManzonSa su suka fi sani.
Lokacin da suka kai Juhfa a nan suka hadu da Abbas ya nufi hijira zuwa Madina, da suka kai Kudaid Manzon Allah (SAW) ya umarci Musulmi su ci abinci saboda wahalar da ya gani suna sha.
Sun sauka a Marruz-Zahraan ’yan kilomitoci daga Makka, a nan suka kafa sansani, sai can wurin yamma makiyaya suna dawowa suka gan su kwatsam! Su suka isar da labari a Makka, sai Abu Sufyan ya zo don ya tabbatar kuma ya ji me yake tafe da su. Ya hadu Abbas sai suka karasa wurin Annabi (SAW). Umar (RA) ya nemi a ba shi izini ya sare wuyansa. Sai Manzon Allah (SAW) ya yi shiru. Da Umar ya matsa sai ya umarci Abbas da ya tafi da shi ya kwana wurinsa ya dawo da shi washegari. Da asuba aka zo da shi sai Manzon Allah (SAW) ya ce kai har yanzu bai bayyana gare ka ka san cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba, kuma ni ManzonSa ne, a nan dai Allah Ya nufe shi da gane gaskiya sai ya yi shahada shahada ta gaskiya.
Abbas ya ce da Annabi (SAW) Abu Sufyan mutum ne mai son girma ka sanya masa wani abu sai ya ce na’am wanda ya shiga gidan Abu Sufyan ya tsira, wanda ya rufe kofarsa ya tsira, wanda ya shiga Masallacin Harami ya tsira. Ranar 20 ga watan Ramadan Manzon Allah (SAW) ya umarci Abbas ya tsaida Abu Sufyan saman dutse don ya ga Musulmi masu shiga Makka. Haka suka yi ta wucewa kabila-kabila kowace dauke da tutarta, kowace ta wuce sai ya tambayi Abbas kuma yana sanar da shi sunansu wanda hakan ya ba shi mamaki.
Kafin su shiga Makka Manzon Allah (SAW) ya umarci Khalid Bn Walid ya shigata Kuda’a can saman Makka, sai dai mutane biyu daga ayarinsa sun yi shahada a wannan rana, su ne: Hubaish dan Al’Ashar da Kurz dan Jabir Al-Fihiri.
Zubair kuma da tasa runduna su shiga ta Kuda’a Manzon Allah (SAW) shi ma ta nan ya shiga. Abu Ubaida da wadanda ba su rike da makami su bi ta cikin kwari, ya shiga Makka ba tare da wata turjiya daga Kuraishawa ba, mutanen da suka cutar da shi suka kore shi da mabiyansa zuwa wurin da ba su saba ba, yau ga shi sun dawo karkashinsa sai yadda ya yi da su.
Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]