✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (33)

Warware Umarar Musulmi da bakin cikin da suka ji na hukuncin sulhu Bayan gama rubuta Sulhun Hudaibiyya sai Manzon Allah (SAW) ya umarci sahabbai su…

Warware Umarar Musulmi da bakin cikin da suka ji na hukuncin sulhu

Bayan gama rubuta Sulhun Hudaibiyya sai Manzon Allah (SAW) ya umarci sahabbai su tashi su yanka hadayarsu, amma babu wanda ya tashi. Ya maimaita fadin haka sau uku shiru ba wanda ya yi magana. Sai Manzon Allah (SAW) ya shiga wurin Ummu Salma ya gaya mata. Sai ta ce da kai ka fara yi ba tare da ka yi wa kowa magana ba. Sai ya fito ya yanka hadayarsa kuma ya yi aski nan da nan sahabbai suka mike suka yi yanka suka askin. Manzon Allah (SAW) ya yanka wani rakumi ne da asalinsa na Abu Jahil ne yana da azurfa a hancinsa don ya bakanta wa kafirai, su ma mutane wadansu suka rika yanka rakuma da shanu kowane daya mutum bakwai.

Musulmi sun yi bakin ciki kan abu biyu ne, na farko komawa ba tare da yin Umara ba. Na biyu rashin daidaito wurin hukuncin maido mushirikan da suka gudo wurinsu ba tare da izinin waliyansu ba amma kuma na Musulmi ba za a maido su ba idan sun je wurin mushirikan.

Manzon Allah (SAW) ya kwantar musu da hankali cewa za su yi Umara a shekara mai zuwa mafarkinsa gaskiya ne kuma duk wanda ya je wurin mushirikai daga cikin Musulmi hakika Allah Ya nisantar da shi, wanda kuma ya zo wurin Musulmi Allah zai kawo masa mafita.

Umar (RA) ya samu Manzon Allah (SAW) yake cewa ashe ba mu ne muke a kan gaskiya ba su kuma suna kan bata? Annabi (SAW) ya ce haka ne. Ya ci gaba da tambaya har dai a karshe Annabi (SAW) ya ce masa lallai ni Annabi ne kuma ba zan sabi Allah ba, Shi ne Mai taimakona ba zai taba tozarta ni ba. Umar (RA) ya tafi cike da fushi zuwa wurin Abubakar (RA) ya fadi duk maganar da ya gaya wa Annabi (SAW) shi ma Abubakar (RA) ya mayar masa da martani irin na Annabi (SAW). Sai Allah Ya saukar da Suratul Fathi, Manzon Allah (SAW) ya aika aka kira Umar (RA) ya karanta masa ayar. Sai Umar ya ce budi ne ya Manzon Allah? Ya ce, na’am. Sannan Umar (RA) ransa ya yi masa dadi ya san mushirikai ba za su sha ba.

Bayan gama sulhu a nan Hudaibiyya sai ga Suba’ah ’yar Alharis Al’aslamiyya ta zo wurin Manzon Allah (SAW) sai mijinta ya biyo ta ya nemi a dawo masa da ita tunda an yi yarjejeniya a kan haka, sai aka hana tunda ba da su aka kulla alkawari ba, sai Allah Ya saukar da wannan aya a kan haka:

“Ya ku wadanda suka yi imani! Idan mata muminai suka zo muku suna masu hijira ku jarraba su. Allah ne Mafi sani game da imaninsu. Kuma idan kuka fahimci su muminai ne to kada ku mayar da su zuwa ga kafirai…. Har zuwa inda Yake cewa: Kuma Allah Masani ne Mai hikima.” (Mumtahanna: 10).

Bayan saukar wannan aya Dan Abbas (RA) ya ce: “An nemi Subaiha ta rantse cewa ba ta fito ba ne don kin mijinta ko kwadayin yawo zuwa wani gari ko samun duniya, sai dai ta fito ne don son Allah kawai da ManzonSa (SAW). Sai Annabi (SAW) ya nemi ta rantse, ta rantse a kan ba ta fito don kin mijinta ba ko kaunar wani mutum cikinmu, ta fito ne don kwadayin Musulunci kawai, ta rantse da Allah wanda babu wani abin bauta sai Shi. Daga nan Annabi (SAW) ya mayar wa mijinta da sadakinta da abin da ya ciyar da ita”.

Haramcin auren muminai mata a kan kafirai da kafarai mata a kan muminai maza ya tabbata. Sai Umar ya auri Subai’ah ya kuma saki matansa biyu mushirikai da suke zaune a Makka, haka sauran sahabbai masu mata mushirikai suka rabu da su.

Manzon Allah (SAW) ya ci gaba da gwada duk mata muhajirai da suka zo yi masa mubaya’a idan sun cika sharuddan Aya ta 12 a Suratul Mumtahana ba ya mayar da su kuma an raba tsakanin Musulmi mata da kafirai.

Banu Khaza’a suka zabi shiga karkashin alkawarin Annabi (SAW) da ma su Khalifofin Banu Hashim ne a Jahiliyya. Su kuma Banu Bakrin suka zabi kasancewa tare da mushirikai.

Daga masu rauni sai Abu Basir ya gudu Madina mushirikai suka aiko mutum biyu suka tafi da shi sai ya kashe dayan ya gudu ya dawo Madina. Annabi (SAW) ya tsawatar masa, sai ya fahimci za a mayar da shi sai ya fita ya je har Saiful BahAr ya zauna daga nan sai masu rauni suka rika guduwa can da suka yi karfi suka rika tare masu fataucin Kuraishawa daga Sham suna kwace dukiyarsu, da abin ya ishi Kuraishawa sai suka aika wa Annabi (SAW) cewa duk wanda ya gudo Madina ya samu aminci. Daga nan duk sauran suka koma Madina Kuraishawa suka samu lafiya wannan matsalar ta gushe.

 

Tasirin Sulhun Hudaibiyya

Wannan sulhu ya kasance mai tasiri kwarai ta wurin tafiyar da da’awa da ci gabanta, domin Musulmi sun samu dama ta shiga sako da lungu don isar da sakon Musulunci a kasashen Larabawa da manyan kasashen duniya a cikin aminci. Suna tafiya suna dawowa babu wata barazana, mutane da yawa sun shiga Musulunci wadanda yawansu na shekara biyu kawai ya fi na shekara tara a baya. A wannan tsakani ne wadansu manyan Kuraishawa gwaraza suka zo Madina suka yi wa Manzon Allah (SAW) mubaya’a, mutanen su ne: Amru dan Al’as da Khalid bin Walid da Usman dan Dalha.

 

Darasi na Talatin da Tara

Sakonnin Annabi (SAW) zuwa ga sarakuna da shugabannin kasashe

Manzon Allah (SAW) ya yi amfani da wannan damar ya aike wa manyan sarakunan dauloli yana kiransu zuwa ga Musulunci, su koma bauta wa Allah Shi kadai, ya aika wa:

1- Najjashi Sarkin Habasha: Ya aika masa Amru dan Umayya Addamiri, an bude wasikar da cewa:

“Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Daga Muhammad zuwa ga Najjashi Aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya da shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, haka idan ya musulunta ya tsira, sannan aka biyo da wa’azi da ayar Alkur’ani kan kalma mai daidaito wurin bauta wa Allah Shi kadai, kuma lallai shi Muhammadu Manzon Allah ne, ya gargade shi a karshen wasikar cewa idan ya ki karbar Musulunci yana da zunubin mutanensa. Najjashi ya karbi Musulunci, da ma Manzon Allah (SAW) ya aiko masa neman auren Ummu Habiba, an aika mata wata baiwa da wannan albishir don murna ta cire gwala-gwalanta ta ba wa baiwar. Da ma ta yi mafarkin an kira ta Uwar Muminai, ta aika wa Sa’id dan Al’as ya zama wakilinta. Da yamma Najjashi ya tara mutane, Ja’afar dan Abu Dalib na jagorantarsu. Najjashi ya daura auren Annabi (SAW) da Ummu Habiba Ramlatu ’yar Abu Sufyan Shugaban Makka. Ya biya Dinari 400, aka ci abinci bayan daura auren. Ummu Habiba ta yi hijira Habasha ce tare da mijinta don ta tsira da imaninta, sai aka yi rashin sa’a ya zama Kirista a Habashar, ta yi iya kokarinta ya dawo Musulunci amma ya ki, sai ma ya nemi ta bar Musuluncin, amma ta jajirce ta ki. Ya shiga shan giya mai tsanani bayan ’yan kwanaki ya rasu sakamakon buguwa da giyar. Najjashi ya hada ta da Muhajirai cikin jiragen ruwa biyu zuwa Madina.

Za a iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141 ko [email protected]