✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (30)

A ci gaba da kawo tarihin Shugaban fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) yau za mu kawo ci gaban yake-yakensa: Yakin Ahzab (Rundunoni) Tunda aka kori…

A ci gaba da kawo tarihin Shugaban fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) yau za mu kawo ci gaban yake-yakensa:

Yakin Ahzab (Rundunoni)

Tunda aka kori Yahudawan Banu Nadir sauran ’yan uwansu Banu Kuraiza suka kara kullatar Musulunci. Musulmi sun kusa kare yada da’awa da gyara halayensu bayan samun natsuwa ta dalilin matakan da Annabi (SAW) ya dauka. An samu akalla shekara daya da rabi babu wata babbar fitina da za a ce ta faru.

Yahudawan Khaibara ba su huta ba domin sun rika boyewa suna kulla makircinsu har suka yi nasarar jawo ra’ayin Uramram wata kabilar Larabawa da take kishin Madina. Mutum ashirin sun fita  daga shugabanninsu da madaukakansu zuwa wurin Kuraishawa suka kwadaitar da su, su yaki Madina kuma suka yi alkawarin taimaka musu, sai Kuraishawa suka amsa musu sannan Kuraishawan nan suka je wurin kabilar Gidfan neman su hadu su yi karfi don su kai wannan hari. Daga nan suka shiga wuraren sauran kabilun Larabawa suka gayyato su wadanda da yawansu sun amsa wannan gayya, shi ya sa ma ake kiran wannan yaki da yakin rundunoni.

Wannan labari ya isa Madina sai Manzon Allah (SAW) ya shawarci sahabbansa, inda Salmanul Farisi (RA) ya bada shawarar a haka rami a kewaye Madina da rami ta hanyar da za a iya shigowa ta cikinta, kuma an hadu kan wannan shawara tasa wadda dabarar yaki ce da ya gani a can garinsu Farisa.

Da yake Madina zagaye take da manyan duwatsu ta bangaren Gabas da Yamma da kuma Kudu amma ban da Arewacinta don haka ta nan Manzon Allah (SAW) ya zaba mafi kuncin wuri mai tsawon kwatankwacin mil daya, ya wakilta kowane mutum goma su haka zira’i arba’in, ya yi tarayya da su a cikin wannan aiki kuma yana sarar kasa, yana tona rami da kansa (SAW).

Hakika sun gamu da nau’o’in wahala a cikin wannan aiki musamman tsananin sanyin da ake kwararawa ga tsananin yunwar da take damunsu. Ya kasance ana kawo musu cikin tafi na sha’ir, saboda tsananin yunwa har suna dora dutse a kan cikinsu don su ji dan nauyi-nauyi ya kasance har iska na kada su, shi kuma Manzon Allah (SAW) tasa yunwar ta fi tasu. Kamar yadda ake ninka masa radadin ciwo rubi biyu a kan na mutane, to, haka ma yunwa saboda nauyin da ke kansa, don haka shi dutse biyu ya dora.

An ga mu’ujiza a lokacin wannan aiki, Jabir (RA) ya ga irin tsananin yunwar da Annabi (SAW) yake ji sai ya kasa hakurin ganinsa a wannan hali, don haka ya je ta yanka wata dabba da yake da ita, ya sa matarsa ta shirya abinci sa’i daya na sha’ir ta gyara ta gasa sannan ya je ya kira Manzon  Allah (SAW) a asirce a cikin wasu sahabbansa, sai Manzon Allah (SAW) ya taho tare da dukkan mutanen Khandak wadanda yawansu su 1000 ne, dukkansu suka ci har suka koshi bai gushe ba yana karuwa, ’yar uwar Nu’uman dan Bashir ita ma ta kai wa Abiyya da kawunsa dabino sai Manzon Allah (SAW) ya watsa shi a kan mayafinsa dukkan masu haka Khandak suka yi ta ci bai kare ba yana zubowa daga gefen tufafin nasa.

Ana cikin haka ramin ne Barra’u da sahabbai suka ci karo da dutse wanda ya gagari fasawa, sai Manzon Allah (SAW) ya sauka ya ce: Bismillahi ya buge shi bugu daya sai ya gutsure ya balle daga gare shi sai wani haske ya fito. Manzon Allah (SAW) ya yi kabbara ya ce: An ba ni mabudan Sham hakika lallai ina kallon jajayen benayenta a wannan sa’ar. Sannan ya kai bugu na biyu ya yi bushara da bude Farisa, ya sake na uku ya yi bushara da bude Yemen sannan dutsen ya fashe.

Sahabbai sun yi ta aikin haka ramin ba ji ba gani har ya kai yadda ke bukata inda aka fara shi ta Yamma ya datse Gabas daidai kan dutsen ta bangaren Arewa.

Kuraishawa sun gabato su 4000, Abu Sufyan yana jagorantarsu. Usman dan Dalha yana dauke da tutarsu, su ma kabilar Gidfan sun halarto tare da wadanda suka bi su na mutanen Najad yawansu ya zama 6000, sun sauka a Zanbun Nakmai zuwa sashen Uhud.

Manzon Allah (SAW) ya halifantar da Ibn Ummu Maktum a Madina sannan ya fita tare da mutum 3000 na Musulmi. Dutsen Sal’a yana kange da bayansu. Kuraishawa sun iso da sauran rundunonin da suka gayyato sai dai sun sha mamaki da haushi ganin ramin da aka haka.

Da suka ga abin takaicin da ya fusatar da su ga Musulmi ga su amma rami ya raba tsakaninsu, sai Abu Sufyan ya ce wannan makidar Larabawa ba su santa ba.

Sun yi iya kokarin su dan tsallaka amma ya gagare su ga Musulmi na ta harbinsu da baka, har ta kai ba su iya kusantar ramin balle su gina wata gadar da za su tsallaka, don haka suka ga bukatar su mamaye Madina su tsare ta, sai dai ba su zo da shirin haka ba.  Sai suka rika fitowa da rana suna kokarin yadda za su ketara ramin, sun yi duk iya kokarinsu haka bai yiwu ba.

Su kuma Musulmi ba su huta ba wurin fadi-tashi suna karewa da hana su tsallakowa ta hanyar jifarsu da duwatsu tsawon yini wanda haka ya ja salloli suka kubuce musu ba su samu yinsu ba sai bayan faduwar rana suka rama su, da yake a lokacin ba a shar’anta Sallar Tsoro ba.

Mushirikai da abin ya ishe su sai wadansu suka fita a wata rana, a cikinsu akwai Amru dan Abdulwudda da Ikrama dan Abu Jahil da Dirarah dan Khaddabi da wasunsu suka samu wani wuri da ya fi kunci suka kutsa da karfinsu suka ketara filin wanda yake tsakanin ramin da Dutsen Sal’a. Sai Amru ya kira a zo a yi mubaraza, da yake shi mutum ne mai karfi, Aliyu (RA) ya fito sai haka ya fusatar da shi har ya sauko daga kan dokinsa. Suka hadu suka kara ba da dadewa ba Allah ya ba Aliyu (RA) sa’a ya kashe shi, shi ma dai jarumi ne matashi. Sauran sai suka karaya tsoro ya cika zukatansu, har Ikrama ya manta kibau dinsa, shi kuma Naufal ya fada ramin Musulmi suka kashe shi. A jefe jefen da aka yi Mushirikai 10 suka mutu, yayin da Musulmi 6 suka yi shahada.