Yau ma cikin ikon Allah za mu ci gaba da kawo muku tarihin fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) wanda ya jagoranci kafa addini da daular da babu irinta, kuma babu wani dan Adam da ya yi irin haka a tarihin duniya. Rayuwarsa makaranta ce mafi girma a tarihin dan Adam.
Darasi na Talatin da Bakwai: Yake-Yaken da Annabi (SAW) ya je
Yakin Uhudu
Ya yin da Kuraishawa suke shirin ramuwar gayya a kan karya su da aka yi a Badar sai ga wani kari ya biyo baya, wannan ya kara fusatawa da tunzura rayukansu, sai suka kara shiri cikin sauri suka hada runduna wadda yawanta ya kai mutum 3, 000 haka yawan rakuma ma 3000, dawaki 200. Gwarazan Bani Abduddar suke dauke da tutar mushirikai a karkashin jagorancin Abu Sufyan. Sun sauka wajen garin Madina tsakanin Dutsen Ainayan da Dutsen Uhud, labarin ya riski Annabi (SAW) tun kafin mako daya da saukarsu.
Manzon Allah (SAW) ya tara rundunar Musulmi mai yawan mutum 1000. Mus’ab ya dauki tutar Muhajirun, Usaid dan Hadir ya dauki ta kabilar Awsu, sai Habbab dan Muzir ya dauki ta Khazraj.
A kan hanyarsu sun yi Sallar Magariba da Isha’i, sai suka kwana a nan mutane hamsin suka yi gadinsu, a nan ne Abdullahi dan Ubayyu shugaban munafukai ya yi tawaye ya juya da tawagarsa ta mutum 300. Sai yawan Musulmi ya dawo 700 kawai, har Bani Salma da Bani Harisa suka samu rudani da rauni suka yi nufin su ma su koma. Sai Allah Ya tabbatar da su ba su juya ba. Bayan isarsu sai Manzon Allah (SAW) ya kasa askarawa, ya zabi mutum hamsin wadanda aikinsu shi ne jifa, ya umarce su da su tsaya a saman Dutsen Uhudu suna komar da dawaki kuma su rika kare Musulmi ta bayansu, ya nanata musu cewa kada su bar wurin da suke koda an yi nasara ko ba a yi ba har sai ya ba su umarni. Ya bar su a karkashin jagorancin Abdullahi dan Jubair Ba’ansare.
Mushirikai sun gabato, mata na zuga su suna wake-wake suna kada mandiri. Mayakan bangarorin sun kusanci juna, Dalha dan Abu Dalha yana kan rakumi rike da tutar mushirikai sai Zubair dan Awwam (RA) ya gabato gare shi, suka hadu suna gwabzawa sai Zubair ya jawo shi ya fadi kasa kuma ya yanka shi. Sai Annabi (SAW) ya yi kabbara, Musulmi ma suka yi kabbara. Sai yaki ya rincabe, Khalid dan Walid ya yi ta kokarin zuwa ta bayan Musulmi amma haka ta faskara saboda masu harbi na kan dutse sun hana yiwuwar haka da ruwan kibiyoyinsu. Musulmi kuma suka rika kai hari kan masu dauke da tutar mushirikai su 13 suka hallaka su ya zamo ba ko daya da take kadawa sai ga tutocinsu warwas a kasa.
Abu Dujana da Hamza dan Abu Dalib sun yi namijin kokari a wannan yaki, Wahashi dan Harb bawa kuma kwararre wurin iya saitin harbi, wanda uban gidansa Jubair dan Mud’imu ya rataya ’yancinsa idan ya kashe Hamza, daukar fansa ne a kan kashe baffansa Du’aima dan Adiyyu da ya yi a Yakin Badar. Wahshi ya yi ta bin sa har ya samu sa’ar sukarsa da kibiya a kirji a lokacin da Hamza yake sarar kan Siba’i dan Urfata wadda ta yi sanadiyar yin shahadarsa. Yakin ya yi zafi har ta kai mushirikai suna tserewa daga filin daga saboda yadda ake karya su.
Ganin wannan karya mushirikai da aka yi suna gudu ya sa Musulmi suka yi tunanin sun gama da su, don haka wadanda aka sa tsaro a saman dutse suka sauko suka shagaltu da kwasar ganima. Da Khalid dan Walid ya hango dutsen ba masu tsaro sai ya dauki wannan damar ya kira mushirikai da karfin murya suka yi sauri suka tattaru, mai yiwuwa sun fi kusa da shi, shi ya sa Musulmi ba su ji wannan kira ba.
Ya zagayo ta bayan Musulmi ya rika sararsu da takobinsa, kokarinsa ya kai ga Annabi (SAW) ya gama da shi kafin Musulmi su farga su iso gare shi. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wa zai mayar mana da su ya samu Aljanna ko ya zama abokina a Aljanna?” A lokacin yana tare da mutum bakwai ne biyu Muhajirai biyar Ansar, sai Ba’ansare ya je yana hana su yana yakarsu har aka kashe shi, haka nan mutanen nan bakwai suka rika tunkararsu suna yakarsu daya bayan daya har aka kashe su duka. Lokacin da cikon na bakwai ya fadi kasa ya rage babu kowa wajen Annabi (SAW) sai Dalha dan Ubaidullah da Sa’ad dan Abu Wakas.
Ubayyu dan Khalaf ya fuskanci Manzon Allah (SAW) da nufin kashe shi amma jarunta irin ta Annabi (SAW) ya yi masa bugun da ya yi sanadiyar hallakarsa, wanda bayan shi bai taba kashe wani rai ba.
Mushirikai sun afka masa (SAW) suka rika jifansa da dutse sanadin faduwarsa ta tsagin damansa. Ya fada rami wanda Abu Amir ya haka don Musulmi su fada, hakorinsa ruba’i na kasa ya karye, sanadin jifan dutsen da Utbatu dan Abu Wakkas ya yi masa, lebensa na kasa ya raunata da kumatunsa, an rotsa kansa da goshinsa. Sa’ad dan Abu Wakkas ya tsayu da ba da kariya ga Annabi (SAW) har Annabi (SAW) ya ba shi kwarinsa ya ce “Harba ya Sa’ad! Mahaifina da mahaifiyata fansa gare ka.”
Shi ma Dalha ganin an rufar wa Annabi (SAW) ya hangi kumatunsa na jini hankalinsa ya tashi, ya zaburo kamar ya fita hayyacinsa har sai da ya samu raunuka 35 ko 39, a wata ruwayar raunuka fiye da saba’in. Shi dai kokarinsa ya kai ga Annabi (SAW), a haka ya kai ya samu ya taimaka masa da hannun hagunsa ya fito daga ramin alhalin hannunsa na dama yana yakar mushirikai.
A wannan lokacin mala’ika Jibril da Mika’il (AS) suka sauko suna yakar mushirikai saboda Annabi (SAW), ga kuma cika alkawarin muminai na kare shi da rayukansu. Da Muslmi suka farga da halin da yake ciki sai suka rugo zuwa gare shi. Na farkonsu Abubakar (RA) tare da Abu Ubaida dan Jarrah, suka taimaka masa a rauninsa sannan Annabi (SAW) ya umarce su su ci gaba da kula da Dalha saboda yawan raunukansa.
Ana cikin haka Abu Dajana da Mus’ab dan Umar da Aliyu dan Abu Dalib da wasunsu suka iso suka ci gaba da raunata mushirikai. Gwarazan Musulmi wadansu na karewa wadansu na harbinsu wadansu na suka da mashi wadansu na yakarsu da takobi.
Tuta tana hannun Mus’ab na dama sai aka sare hannun, sai ya rike da hannunsa na hagu shi ma aka sare, sai ya makale ta a tsakanin kirjinsa da wuyansa bai bari ta fadi kasa ba har sai da aka kashe shi. Abdullahi dan Kum’a shi ne ya kashe shi kuma da shi aka rotsa Annabi (SAW).
A Lokacin da Mus’ab ya rasu sai Dan Kum’a ya zaci cewa Manzon Allah (SAW) ya kashe, ya kasance yana kama da shi. Sai ya fara kwarma kira yana cewa hakika an kashe Muhammad! Nan da nan labari ya yadu, wanda ya sa mushirikai suka dan sarara da yaki.
Musulmi sun yi da’ira a hanyar tabbata a inda suka tsaya suka ci gaba da yaki duk da ba wani jagora mai tsarawa, komai ya yamutse.
Ana wannan rudani har Musulmi suka kashe dan uwansu da hannunsu mahaifin Huzaifatul Yamani.
Wadansu na ganin a daina yakin tunda Annabi (SAW) a cewar mushirikai ya rasu, har wadansu sun daina, wadansu sun gudu yayin da wadansu kuma a lokacin suka kara samun karfi don su kare addininsu, har suna cewa ‘ku mutu a kan abin da Annabi (SAW) ya rasu.’
Sai Musulmi suka ji Ka’ab dan Malik yana musu albishir cewa Manzon Allah (SAW) yana raye, bayan an watsa mushirikai.
Sai ga Abu Sufyan da Khalid dan Walid sun jagoranci mushirikai sun zo wurin Musulmi, a sashen kololuwar Dutsen Uhud, sai Umar dan Khaddabi shi da wani mutumin Madina suka yake su, har suka kora su, a wata ruwayar Sa’ad dan Wakkas ya kashe mutum uku daga cikinsu.
Yawan mushirikai wadanda aka kashe su 24, kuma a wani fadin an ce su 37 ne, yayin da yawan Musulmin da aka kashe mutum 70.
Za a iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141, Email-aliyugamawa@gmail.