Yana daga cikin al’adar Manzon Allah (SAW) ya yi barci farkon dare bayan ya yi Sallar Isha’i, a yankin dare na karshe sai ya tashi ya tafi masallaci ya yi Tahajjud. A wannan daren sai ya umarci Aliyu (Allah Ya kara masa yarda) kan ya kwanta a kan shimfidarsa bayan ya sanar da shi babu abin da zai same shi, bayan mutane sun nutsa cikin barci cikin dare sai wadanda aka umarta su kashe Annabi (SAW) suka shiga gidansa a asirce suka nufi shimfidarsa suna zaton Annabi (SAW) ne. Har sun kewaye shi sai suka duba da kyau sai suka ga Aliyu (RA) ne yake barci, sai ya tashi ya fita.
Wannan shi ne abin da ke cikin fadar Allah:
“Kuma a lokacin da wadanda suka kafirta suke yin makirci game da kai, domin su tabbatar da kai (daure ka), ko su kashe ka, ko kuma su fitar da kai (su kore ka daga Makka), suna makirci kuma Allah Yana mayar musu da makirci, kuma Allah ne mafificin masu makirci.” (Anfal:30).
Allah cikin ikonSa Ya ba Annabi (SAW) damar fita duk da suna kewaye da gidansa sai ya barbada kasa a kawunansu yana karanta fadar Allah:
“Waja’ala min baini aidihim saddan wa mi khalfihim saddan, fa’a gashainamum fahum la yubsiru.” (Yasin:9)
Allah Ya makantar da ganinsu don haka ba su ga fitarsa ba. Ya isa gidan Abubakar ya same shi suka fita har suka kai Dutsen Saur wanda ke da nisan mil biyar ta bangaren Yamen, fitarsu alfijir bai keto ba. Lokacin da suka kai bakin dutsen sai Abubakar (RA) ya fara shiga ciki don kada Annabi (SAW) ya shiga wani abu ya cutar da shi, gara shi ya same shi. A cikin kogon akwai ramuka don haka sai ya keta mayafinsa ya tottoshe su sai daya ne ko biyu bai samu abin da zai toshe su ba sai ya sanya kafafunsa ya toshe da su. Da Annabi (SAW) ya shigo sai ya kwanta ya yi barci kansa a kan kafar Abubakar (RA). Can sai maciji ya sari Abubakar a kafar da ya rufe ramin da ita, duk da tsananin zafin da yake ji bai motsa ba, don kada ya katse Annabi (SAW) daga barcin da yake yi. Sai dai hawayensa ya kwarara ne da Annabi (SAW) ya ji hawaye na zuba jikinsa ya farka ya ce an sare ka, mahaifina da mahaifiyata fansa ne gare ka. Daga nan ya yi masa tofi radadin ya tafi.
Kwanansu uku a kogon Dutsen Saur, Abdullahi dan Abubakar yana zuwa ya kwana tare da su, ya kasance matashi ne mai hazaka yana wawantar da mutanen Makka ya nuna kamar a cikinsu ya kwana kuma yana jin duk makidar da Kuraishawa suke kullawa. Amir bawan Abubakar da yake kiwata masa dabbobi idan dare ya yi sai ya zo musu da su, su sha nono har safe.
Su kuwa ’yan ta’addan da suka zo kashe Annabi (SAW) sun jira su ga tashin Annabi (SAW) da fitowarsa har asuba. Sai Aliyu (RA) ya tashi daga shimfidar sai ya yi kicibis da su, sai suke tambayarsa ina (Annabi) Muhammad? Sai ya ce bai san inda yake ba, sai suka dake shi suka kai shi Ka’aba suka daure na tsawon sa’a. Da suka ga ba wani ci gaba sai suka je gidan Abubakar suka tambayi ’yarsa Asma’u ina Abubakar? Ta ce ita ma ba ta sani ba, sai Abu Jahil ya yi mata mummunan mari har sai da dan kunnenta ya fice ya fadi.
Daga nan sai suka baza mutane su tafi neman Annabi (SAW) da Abubakar (RA) ta kowace nahiya kuma suka sanya kyautar taguwa 100 ga duk wanda ya kawo Annabi (SAW) da Abubakar (RA) a mace ko a raye. Sun fita nemansu, neman ya kai su har kofar Kogon Saur ta yadda da a ce dayansu ya kalli kasan kafafuwansu to da sun gansu haka ya sa Abubakar (RA) ya shiga damuwa. Sai Annabi (SAW) ya ce masa: “Ya Abubakar! Me kake zato ga biyu da na ukunsu Allah ne?
“Kada ka damu, hakika Allah Yana tare da mu.”
Ranar 1 ga watan Rabi’ul Awwal shekara ta 13 bayan aiko Annabi (SAW), sai mai yi musu jagora ya iso gare su da abin hawansu biyu kamar yadda suka yi alkawari haka nan Amir dan Fuhaira ya same su suka dauki hanya da su ta yankin Kudancin Yaman har suka yi nisa.
Kan hanyarsu ta zuwa Madina
Sun doshi yamma ta Bahar Ahmar (Jan Teku ko Maliya) sannan suka fuskanci Arewa suka bi hanyar da mutane ba su bin ta sai kadan, sun yi ta tafiya zuwa dare har suka kai rabin wani yini sannan suka huta. Annabi (SAW) ya zauna a karkashin inuwar yashin sahara har ya samu barci. Abubakar ya ga wani makiyayi ya nemi madara a wurinsa. Bayan Annabi (SAW) ya tashi sai ya ba shi ya sha daga nan suka kara hutawa sannan suka ci gaba da tafiya. A dare na biyu ne kan hanyarsu suka zo wajen wata hema ta wata mata Ummu Ma’abad kimanin kilomita 130 daga Makka, sun tambaye ta ko za a samu wani abu a wurinta? Sai ta yi musu uzuri babu, akwai wata akuya wadda ba ta da ruwan nono ko kadan kusa da su. Sai Annabi (SAW) ya nemi izininta kan ya tatsi madararta, ta yi musu izini. Sai Annabi (SAW) ya fara tatsa sai nan da nan nonuwan suka cicciko har sai da babbar kwarya ta cika. Ya shayar da Ummu Ma’abad, sannan abokinsa sannan ya sha, kuma ya kara cika mata kwaryar suka tafi. Mijinta da ya dawo ya yi mamaki kan haka.
A rana ta uku mutanen Makka sun ji wani sauti mai karfi na yabo ga Annabi (SAW) da abokinsa ga kadan daga ciki: Suraka dan Malik ya yi kwadayin kyautar da aka sa kan wanda ya samo Annabi (SAW) da abokinsa. Don haka ya bi su a kan wani dokinsa har sai da ya kai kusa da su. Annabi (SAW) a lokacin suna Sallah, sai dokinsa ya kayar da shi, ya sake hawa ya kusance su har yana jin karatun Annabi (SAW). Sai kafafuwan dokin suka nuste a kasa suka kafe har sai da suka yi raka’a biyu sannan da ya daka masa tsawa ya mike sawun ya zama kura ya tashi sama kamar hayaki. Wannan ya tabbatar masa tabbas al’amarin Annabi (SAW) sai ya bayyana. Don haka ya shafa wa kansa lafiya ya kira su da aminci, suka tsaya har ya iso gare su. Annabi (SAW) ya labarta masa ikirarin da Kuraishawa suke yi da nufin mutane a kansu shi da Abubakar. Ya bijiro masa da guzuri da abin hawa amma bai karbi komai ba. Annabi (SAW) ya nemi da ya boye wannan lamari ga mutane sannan ya nemi Amir dan Fuhairah ya yi rubutu na aminci. Sai ya rubuta a ganyen dabino. Daga nan Suraka ya koma kan hanya, duk wanda ya hadu da shi yakan ce hakika labari ya kubuce muku, sai ya juyar da su su koma. A hanya ya hadu da Buraida dan Hasib (RA) tare da mahaya 70 sai ya musulunta da wadanda ke tare da shi kuma suka yi Sallah a bayansa.