Godiya ta tabbata ga Allah Mai jujjuya zamani Wanda Ya kaddari rayuwarmu ta kawo yau. Idan za a tuna a ranar 1 ga Fabrairun bana ne muka jingine wannan darasi na tarihin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), don tabo wasu batutuwa da suka shafi wannan addini da Manzon Allah (SAW) ya zo da su. Ganin mun tabo abubuwa da dama a wannan tsakani yau cikin yardar Allah za mu koma ga wannan darasi zuwa abin da ya sawwaka. Muna fata za mu dauki darasin da ke cikin wannan littafi na Malam Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa game da rayuwar Manzon Allah (SAW), wadda ta kunshi kowane abu da ya shafi rayuwar dan Adam:
Littafi na Biyu
Darasi na Ashirin da Takwas
Hijirar Manzon Allah (SAW) zuwa Madina
A lokacin da al’amura suka yi nisa wajen kulla alaka a tsakanin Annabi (SAW) da mutanen Madina, har ya kai Manzon Allah (SAW) ya tura wadansu sahabbai zuwa Madina don su koyar musu da addinin Musulunci kuma an kulla yarjejeniya tsakaninsa da mutanen Madina, sai hankalin mutanen Makka ya tashi game da take-taken samun nasara na Annabi (SAW). Don haka suka fara yin tarurruka don neman hanyoyin da za su bullo wa wadannan al’amura, musamman don dakile wannan guguwa da take tasowa. A daya daga cikin tarurrukan da suka shirya a Darun Nadwa, shugabannin Kuraishawa sun amince cewa kowace kabila da ke garin Makka ta ba da wakili daya da za a hada guiwa don a taru a kashe Manzon Allah (SAW). Bayan sun gama yanke shawarar kashe Manzon Allah (SAW), sai Allah (SWT) Ya sanar da shi labarin abin da suke kullawa, sannan Ya ba shi umarnin ya yi hijira ya bar Makka zuwa garin Madina. Allah (SWT) Yana fadi a cikin Alkur’ani Mai girma cewa:
“Kuma a lokacin da wadanda suka kafirta suke yin makirci game da kai, domin su tabbatar da kai (daure ka), ko su kashe ka, ko kuma su fitar da kai (su kore ka daga Makka), suna makirci kuma Allah Yana mayar musu da makirci, kuma Allah ne mafificin masu makirci.” (Anfal:30).
Da samun wannan umarni sai Manzon Allah (SAW) ya nufi wurin babban abokinsa Abubakar Siddik (RA) don sanar da shi umarnin Allah gare shi. Nan take Abubakar Siddik ya nuna bukatar bin sa su yi wannan hijira tare. Daga nan sai suka fara shiri, suka nemi abin hawa, suka nemi wanda zai nuna musu hanya sannan suka yi tanadin guzuri. Sun shirya fita washegari da asubahi, sannan sai Annabi (SAW) ya yanke shawarar sanya Aliyu bin Abu Dalib (RA) ya je gidansa ya kwanta a kan shimfidarsa don badda sawu. Daga nan Annabi (SAW) ya maida dukkan kayan ajiyar da ke hannunsa. Da jijjifin asubahi, bayan shekara 13 yana gwagwarmaya da Kuraishawa , sai Annabi (SAW) tare da abokinsa Abubakar suka fita don barin garin Makka don samun mafaka a birnin Madina. Amma yana shirin fita, sai ga wadansu mutane daga Kuraishawan Makka sun tafo gidan Annabi (SAW) don aiwatar da niyyarsu ta kashe shi. A nan sai Allah (SWT) Ya boye ManzonSa (SAW), har ya samu ya zare jikinsa ya bar su cikin dimuwa da magagi. Sai bayan ya fita suka leka shimfidarsa suka ga ashe Aliyu bin Abu Dalib ne a kwance ba Annabi (SAW) ba.
Manzon Allah (SAW) ya bar garin Makka a ranar Litinin cikin watan Rabi’ul Awwal shekara 13 bayan aiko shi da sako. Ya fita ne da jijjifin asuba tare da Abubakar Siddik da mai yi musu jagora Abdullahi bin Uraikid. Ba su zame ko’ina ba sai Dutsen Saur, inda suka shige cikin kogon dutsen suka fake.
A nasu bangaren kuma, bayan wadanda suka je kashe Manzon Allah (SAW) sun gane cewa Aliyu bin Abu Dalib ne ke kwance a shimfidar Annabi (SAW) kuma Manzon Allah (SAW) tuni ya bar garin Makka, sai suka bazama nemansa. Sakamakon matsa kaimin da masu neman Annabi (SAW) suka yi, har sai da suka kai dab da inda shi da Abubakar Siddik (RA) suke boye a cikin kogo. A lokacin da suka iso bakin kogon da Annabi (SAW) yake ciki, sai hankalin Sayyidina Abubakar (RA) ya tashi don yana ganin za su gano Manzon Allah (SAW), su kama shi su kashe shi. Amma sai Annabi (SAW) ya kwantar masa da hankali da cewa kada ya yi bakin ciki lallai Allah yana tare da su. Nan mushirikai suka yi ta dubawa amma ba su ga alamar kasancewar mutane a wurin ba. Manzon Allah (SAW) ya zauna cikin wannan kogo tare da abokin tafiyarsa na tsawon kwana uku, inda daga nan ne mai rakiyarsu ya zo ya ci gaba da nuna musu hanya. Sun yi tafiya na tsawon mako guda kafin su isa Kuba. Nan ya yi zango na tsawon kwana 24. Ya zauna a wurin ya gana da mutane, cikinsu har da Banu Amru bin Auf. Kuma a wadannan kwanaki ne Annabi (SAW) ya jagoranci gina masallaci a Kuba, wanda a yau ake zuwa ziyarar ganinsa a wajen garin Madina tare da yin nafila a cikinsa don irin falalar da yin Sallah a cikinsa ke da shi.
Bayan an yi Sallar Juma’a a Kuba, sai Annabi (SAW) da sahabbansa suka tashi suka nufi cikin garin Madina, inda aka yi musu gagarumar tarya. Ya fara sauka ne a gidan Abu Ayyubal-Ansari kafin a gina wa Manzon Allah (SAW) gidansa da kuma Masallaci. Daga nan ne aka bude wani sabon shafi a tarihin yaduwar addinin Musulunci. Musulmi da suka yi hijira suka biyo bayan Annabi (SAW), zuwa Madina sun samu sauki daga tsangwama, sun fita a kangin kaskanci sun shiga sabuwar rayuwa. Daga nan Musulmin da ke Makka suka ci gaba da yiwo hijira, sannan Annabi (SAW) ya rika kulla ’yan uwantaka a tsakaninsu da mutanen Madina. Muhajirun wato mutanen Makka suka samu matsuguni, suka samu jarin kasuwanci, suka samu matan da za su aura (saboda sun bar matansu a Makka) da dai cikakkiyar rayuwa. Masallacin Manzon Allah (SAW) ya zama cibiyar yada addini a duniya baki daya. Manzon Allah (SAW) ya kulla alkawarin zaman lafiya da Yahudawan Madina, ya hada kan kabilun garin da da ba sa ga maciji da juna. Al’ummomun Madina suka zauna cikin aminci da natsuwa da walwala.
Darasi na Ashirin da Tara:
Bayanin yadda Hijirar Annabi (SAW) ta kasance:
Manzo (SAW) ya fita ya je gidan Abubakar (Allah Ya kara masa yarda) da tsakar rana lokacin da mutane suka natsu a gidajensu suna hutawa, ya samu Abubakar suka tattauna kan lamuran hijira. Sai suka shirya abin hawa iya shiryawa, kuma suka dauki hayar Abdullahi dan Uraikit Allaisi, wanda ya kasance ya san hanya sosai kuma kwararre ne don ya yi musu jagora (zuwa Madina) amma yana kan addinin Kuraishawa ne, sun yi alkawarin haduwa a Dutsen Saur bayan kwana uku, daga nan Abdullahi Ibn Uraikit ya koma Makka ya ci gaba da hidimominsa na yau da kullum kamar yadda ya saba, tamkar ba wata tafiya a gabansa, ta yadda ba wanda zai iya ganewa.
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]