✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (13)

An yi wannan zalunci na yanke mu’amala ce ga dangin Annabi (SAW) a shekara ta bakwai da aiko Annabi (SAW), a haka suka shafe tsawon…

An yi wannan zalunci na yanke mu’amala ce ga dangin Annabi (SAW) a shekara ta bakwai da aiko Annabi (SAW), a haka suka shafe tsawon shekara uku a cikin halin kunci da wahala mai tsanani domin kuwa bayan abin da suke da shi ya kare sun fada mawuyacin hali wanda ya kai su har suka rika cin ganyen itatuwa da fatun dabbobi, har ta kai ana jin kukan mata da yara saboda tsabar yunwa. Daga shekara sai shekara kawai suke fita a watannin da aka haramta yaki a cikinsu, lokacin aikin Hajji, suna sayen abinci a wurin mahajjata baki masu shigowa daga garuruwan Larabawa don yin bauta ga gumakansu. Kuraishawa na tsuga musu kudi har su kasa saye, mace har takan sayar da maganin mijinta marar lafiya don danta ya ci abinci.

Khadija (Allah Ya kara mata yarda) ta ciyar da dukan dukiyarta har sai da ta rasa komai! Ya kasance Hakim dan Hazam dan dan uwanta yana satar hanya ya kawo mata abinci. Babu wani abu da ke shigar musu sai a asirce.

Manzon Allah (SAW) kuma duk halin da suke ciki bai sa ya yi kasa a gwiwa ba domin kuwa yana fita ya yi kira ga bakin da suka shigo ziyara.

Bayan shekara uku a wannan hali wato a shekara ta 10 da aike, Allah Ya kaddara karshen wannan wahala, sai ya hukunta gara ta cinye takardar da aka yi kullin alkawari da rantsuwa a cikinta, sai fa inda sunan Allah Yake ne kawai ba ta ci ba.

Kuma ya jefa a zukatan wadansu manya kuma madaukakan mutane a Kuraishawa su biyar suka warware alkawarin wannan takarda, bayan sun tuna wata dangantaka ta zumunci da kowanensu yake da ita da Annnabi (SAW), wadannan mutane su ne:

Hisham dan Amru daga Bani Amir dan Lu’ayyu da Zuhair dan Abu Umayya Almakhzumi dan goggon Annabi (SAW) Atika ’yar Abdulmudallibda Almud’imu dan Adiyyu da Abu Bukhtary dan Hisham da Zam’a dan Al’aswad.

Hisham dan Amru shi ne ya fara jin damuwa a kan abin da ake yi wa danginsu na zumunci na zama da yunwa musamman kananan yara, daga nan ya nemi taimakon Zuhair saboda kabilarsu babba ce mai karfi a tsakanin Kuraishawa. A haka cikin sirri har wadannan mutane suka hadu.

Tunda asuba lokacin da masu bauta ke haduwa a wurin bautar suka hadu, dama sun tattauna maganar a jiya sai kawai Zuhair bayan ya yi dawafi ya fuskanci mutane yana cewa: “Mu fa muna ci muna sha kuma muna sanya sutura amma ga Banu Hashim da Banul Muddalib sun hallaka. Ba zan zauna ba har sai wannan takardar ta yage.” Sai Abu Jahil ya ce “Karya kake wallahi ba za ta yage ba.” Sai Zam’a ya ce: “Kai ne dai makaryacin! Mu fa da ma ba mu yarda a yi wannan rubutun ba.”

Sai Abu Bukhtary ya ce: “Kaskiya ce ba mu yarda ba, kuma ba ma kusantarsa.” Shi ma Al’mud’imu ya ce: “Gaskiya ce duk wanda ya fadi haka, mun barranta da ita.” Sai Hisham ya kara gaskata haka.

Abu Jahil ya ce kun dai yanke hukunci da dare a wani wuri da ba wannan ba. Duk da cewa Abu Jahil shi ne shugaban Makka, a nan an fi karfinsa.

Ya kasance an yi wa Annabi (SAW) wahayi a kan takardar Annabi (SAW) ya ba su labari cewa: “Gara ta cinye takardar sai sunan Allah kawai ya rage, ya ce idan karya ce mu bar shi da ku, idan gaskiya ce ku janye zaluncinku.”

Sai kuwa suka shiga suna zuwa suka tarar takarda an ciye ta kamar yadda Annabi (SAW) ya fada.

Ikrama ya ruwaito cewa tabbas gara ta cinye takardar sai fa inda aka rubuta “Bi’ismikallahumma.” Allahu Akbar!

Da ma nufinsu ke nan kuma ga shi ba ma yagewa ba, an cinye ta, kuma a inda suke girmamawa suka aminta da komai nasu, har rantsuwa suka yi a gaban gumakansu suka rataye da nufin su cika musu alkawarin.

Wannan shi ya kawo karshen wannan tsanani da wariya, sai Annabi (SAW) da duk wanda yake tare da shi suka fito daga Shi’ib.

Darasi na Goma Sha Tara

Shekarar Bakin Ciki

Ba a jima da dawowar Banu Hashim cikin mu’amalolin jama’a ba, malaman tarihi suka ce a kasa da shekara guda, sai Allah (SWT) Ya dauki ran manyan makusanta kuma masu taimaka wa Annabi (SAW) wato Abu Dalib da kuma Khadijah matarsa. Wadannan bayin Allah duk sun rasu a shekara ta goma da fara kiran Annabi (SAW), kuma a bisa wani Kaulin tsakanin rasuwar Abu Dalib da Khadijah wata guda ne kawai.

Wannan abin da ya faru ya yi matukar jijjiga Annabi (SAW) don ya rasa masu kaunarsa kuma makusantansa, wadanda ba su taba nuna kosawa ko ja da baya ba wajen taimakonsa da ba shi shawarwari da karfafa masa gwiwa. A lokaci guda kuma, rasuwar Abu Dalib ta sanya rushewar babban bangon da yake bai wa Annabi (SAW) kariyar kabila da dangi, wadanda abubuwa ne masu matukar muhimmanci a tsarin rayuwarsu ta wancan lokaci. Wani babban al’amari kuma shi ne bayan rasuwar Abu Dalib sai jagorancin kabilar Banu Hashim ya dawo hannun babban makiyin Manzon Allah (SAW) wato Abu Lahabi. Wannan canji kuwa ya yi sanadiyar janye kariyar dangin Banu Hashim da Annabi (SAW) yake samu ta hannun Abu Dalib. Don haka sai al’amarin cutarwa da takurawa ya dawo sabo fil ga Ma’aikin Allah (SAW). Saboda yanzu babu mai tsaya masa a cikin danginsa daga kafiran Makka, kowa sai ya yi masa abin da ransa yake so.

Sai dai tun hijirar Musulmi ta farko zuwa Habasha, Annabi (SAW) da jama’arsa suka fara tunanin makomarsu a wajen Makka. Kuma a duk halin da suke ciki ba su gushe ba suna fadada kira zuwa ga mutanen da ke wajen Makka. Har ila yau ayoyin Alkur’ani da yawa sun koyar da su yadda za su fadada tunaninsu zuwa fadin duniyar da Allah Ya halitta baki daya. Saboda wadannan da kuma halin da Makka take ciki, sai Manzon Allah (SAW) ya fara yunkurin juya kiransa zuwa wajen garin Makka.

Bayan fitar Annabi (SAW) da danginsa daga takunkumin da mushirikai suka saka musu na tsawon wata shida, sai baffansa Abu Dalib wanda ya haura shekara 80 a duniya ya kwanta ciwo. Da Kuraishawa suka fahimci da kyar zai tashi daga wannan rashin lafiya sai suka sake taruwa suka ce mu je mu nemi ya ba mu Aliyu (RA) kafin ya rasu. Wadansu suka ce mu dai bari ya rasu sai mu dauke shi, sai kuma suka sake komawa wajen Abu Dalib suna gargadinsa a kan ya ja kunnen Annabi (SAW) ya rabu da abubuwan bautarsu. Sai Abu Dalib ya kira Annabi (SAW) ya bijirar masa da bukatarsu, shi kuma ya ce ni fa kalma daya kawai na nemi su fada wadda za ta addinantar da su, suka ce kalma daya? Ya ce Eh. Suka ce wace kalma ce?

Ya ce ‘La’ilaha illallah, sai suka mike suna kakkabe tufafinsu suka ce kamar yadda Allah Ya fada: “Ashe za a sanya abubuwan bauta abin bauta guda daya, lallai wannan wani abin al’ajabi ne.”

Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141

email:[email protected]