Fatima da mijinta ya samu, Habbab dan Al’arat (Allah Ya kara musu yarda) yana karantar da su Alkur’ani amma da suka ji shigowarsa Habbab ya boye, Fatima ma ta boye littafin, da yake ya riga ya ji ya tambaye su me suke yi suka ce tattanauwa ce kawai, ya ce ko dai kun karkace? Sai mijin ya ce, me kake gani idan gaskiya tana a cikin addinin da ba naka ba? Sai ya hau surukinsa da duka har sai da Fatima ta ture Umar, ita ma ya yi mata mari har sai da jini ya fito a fuskarta. Sai ta ce, cikin fushi, “Idan kuma addinin da ba naka ba ne yake a kan gaskiya fa?” Wannan rashin jin nauyinsa da Fatima ta yi ya sa ya ji kunya kuma ya yi nadama, don a da tana girmama shi. Daga nan ya nemi ta ba shi Alkur’anin ya gani ta hana ta ce masa ai kai najasa ne kuma masu tsarki kadai suke taba shi.Allah cikin ikonSa sai Ya karya zuciyarsa; dama kuma ya taba labewa ya ji Annabi (SAW) na karatu a Sallah tun lokacin ya fara karaya da irin gaskiyar da ya ji, amma dai Allah bai nufe shi da sallamawa ba a wancan lokaci.
Daga nan ya yi wanka ya karba ya karanta suratu (Taha) ce daga farkonta har zuwa aya ta 14 inda Allah Yake cewa: “Lallai Ni ne Allah babu abin bauta sai Ni, ku bauta Mini ku tsai da Sallah don ambatoNa.”
Daga nan Habbab ya fito daga maboyarsa yana masa albishir da addu’ar Manzon Allah (SAW) ce Allah ya amsa. Babban dalilin musuluntar Umar a ruwaya mafi inganci shi ne addu’ar Manzon Allah (SAW).
Baya ga haka, Umar ya hadu da Ummu Abdullahi ’yar Abu Hasama, ta fito ita da mijinta za su yi hijira zuwa Habasha. Sai Umar ya ce: “Tafiya za ku yi?” Lokacin mijinta ba ya nan, ya tafi biya musu wasu bukatu. Sai ta amsa wa Umar da, “Eh, za mu fita zuwa kasar Allah. A nan kun cutar da mu, muna fatan Allah zai samar mana mafita.” Sai Umar ya ce: “Allah Ya kasance tare da ku.”
Karkashin wannan za mu fahimci cewa ga alama Allah Ya amsa addu’ar Manzonsa (SAW), zuciyar Umar ta fara karaya.
Umar ya tafi Darul Arkam ya buga kofa, wanda ya leka da ya gan shi da takobinsa sai aka fada wa Annabi (SAW) ya nemi su tattaru, da suka hadu wuri daya sai Hamza ya tambaye su me ya same ku? Suka ce masa Umar! Sai ya ce ku bude masa idan da alheri ya zo mu baje masa shi, idan kuma da sharri ne mu kashe shi da takobinsa. A lokacin Manzon Allah (SAW) yana can cikin gidan yana karbar wahayi, sai ga shi ya fito ya cakumi Umar da karfi yana cewa, “Ya Umar ashe ba za ka daina ba har sai Allah Ya aikata maka abin da ya yi ga Walid dan Mugira?” Umar karbar Musulunci ya kawo shi kawai sai suka ji yana kalmar shahada:
“Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma lallai kai ManzonSa ne.” Sai duk wadanda ke wurin suka dauka da kabbara.
Umar (RA) ya tafi ya sanar da wadansu manya a cikin kabilarsa wanda sakamakonsa ya juye wani dan karamin yaki suna yakarsa yana mai da martani har rana ta sauka a kansu, da ya koma gida suka bi shi don su kashe shi, sai dai Allah bai ba su iko ba suka koma.
Musulmi sun kara samun ’yanci da walwala ta dalilin musuluntar Umar, a da a boye suke yin ibada, suna so su fito fili su yi ba hali, amma yanzu har sun nemi izinin Annabi (SAW) su fara fita fili suna ibadar, sun yi sahu biyu suka fito Umar da Hamza (Allah Ya kara musu yarda) suka tsaya musu. Hamza da daya sahun, Umar da dayan har suka isa masallacin harami. A wannan rana Kuraishawa sun ji takaici da bakin cikin da ba su taba ji ba. Lallai mai rarrabewa ne Umar a kan wannan aka kira shi Al-Faruk.
Ibn Mas’ud ya ruwaito cewa: “Ba mu gushe ba muna samun daukaka tun da Umar ya musulunta.”
Darasi na Goma Sha Takwas
Katange Annabi (SAW) da danginsa Banu Hashim da Banu Muddalib a Shi’ibu Abi-Talib
Da Abu Talib da ya ga take-taken mushirikai na burin kashe Annabi (SAW) karara, sai ya tara danginsa kaf Musulmi da kafiransu ya nemi su ba Annabi (SAW) kariya ta dangantaka. Kuraishawa suna da hadin kai da kishin kabilarsu don haka sai suka amsa masa suka yi alkawarin ba shi kariya komai wahala, amma ban da Abu Lahab shi kadai ya ware ya rabu da su yana tare da sauran mushirikai.
An kulla wannan alkawari ne a Ka’aba a lokacin da mushirikai suke ta yin kokarinsu na hana kiran da Annabi (SAW) yake yi, amma bai amfana musu komai ba sai karin kaskanci da tozarci da hasara, Musulunci kuma sai kara daukaka yake yi tun musuluntar su Hamza da Umar a shekara ta shida da aiko Annabi (SAW). Kuma suka ga ba sauran wata hanya da ta rage musu illa guda daya ita ce takwabi, ko a da can ita ce hanyar warware matsala a tsakaninsu, abin da bai kai ya kawo ba sai a mayar da shi yaki balle kuma wannan babban lamari da suke ganin ya kawo musu cikas a addininsu da mu’amalarsu da zamantakewarsu da kasuwancinsu da kuma wayewarsu suna ganin komai ya ci baya ne.
Kwatsam sai makiya Annabi (SAW) suka samu labarin kariyar da dangin Annabi (SAW) suka dauki alkawari za su ba shi, su kiyaye shi daga dukan farmakinsu, sai suka taru a Bani Kinana suka fara shawarwari su kulla su kwance har suka cimma matsaya, suka sanya wasu tsauraran dokoki a kan Bani Abdulmudallib da Bani Hashim a siyasance.
Dokokin su ne:
1. Ba za a yi ciniki da su ba, wato su saya ko a saya a wajensu.
2. Ba za a aure su ba kuma ba za su aura ba.
3, Ba za a zauna wuri daya da su ba.
4. Ba za a yi cudanya da su ba.
5. Ba za a shiga gidajensu ba.
6. Ba za a rika magana da su ba.
7. Ba za a taba tausaya musu ba.
8. Ba za a yi sulhu da su ba har abada.
Wannan alkawari da yarjejeniya sun rubuta shi a takarda kuma suka rataya shi a cikin Ka’aba saboda muhimmancinta a wurinsu.
Dukan wadannan dokoki na kangi da aka sanya musu za a ci gaba da zartar da su har sai sun gaji sun sallama Annabi (SAW) gare su da kansu don a kashe shi. Wanda ya yi rubutun shi ne Bagid dan Amir dan Hashim a kan haka Annabi (SAW) ya yi addu’a hannunsa ya lalace.
Dukan dangin Annabi (SAW) sun bar gidajensu suka taru gaba dayansu a Shi’ibu Abi-Talib Musulminsu da kafiransu, wannan ya nuna cewa Annabi (SAW) danginsa suna kaunarsa, in ban da Abu Lahab shi ne kadai bai je ba.
Za iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141
email:[email protected]