✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan ’yan siyasar da suka karya alkawarin sauya sheka

Yadda manya 11 suka yi alkawarin da kuma yadda suka lashe amansu.

Akalla manyan ’yan siyasar kasar nan 11 ne ciki har da gwamnoni masu ci da wani tsohon Mataimakin Shugaban Kasa da ’yan majalisar dokoki da sauransu suka karya alkawarin da suka yi kan ba za su sauya sheka ba, kamar yadda binciken Aminiya ya gano:

Duk da cewa ba dokar ta hana ’yan siyasa canja sheka, amma masu sharhi suna bayyana hakan da karuwancin siyasa, inda suka ce hakan yana nuna rashin akida a tsakanin ’yan siyasar Najeriya.

Bayan ’yan siyasar 11 akwai daruruwan da suka canja shekar daga jam’iyyunsu. Sai dai alkawari a bainar jama’a ne ya bambanta ’yan siyasar 11 da sauran.

Atiku Abubakar

Kan gaba a cikin masu karya alkawarin shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar –Mutumin da ya rika tsayawa takarar Shugaban Kasa.

A shekarar 2015 Atiku wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafuwar jam’iyyar APC, ya ce, “Lokacin da na zagaya kasarmu kuma na saurari fata da tsoro da abin da ’yan Najeriya daga kowane bangare suke yi, sai na ce APC ce tashar karshe, ita ce karshen tafiya.”

Amma lokacin da ya canja sheka zuwa Jam’iyyar PDP a shekarar 2019, sai ya rera wata wakar yana cewa: “Jam’iyyar da muka kafa ta kunyata kuma tana ci gaba da kunyata matasanmu.

“Ta yaya za a nada ministoci amma babu matashi ko daya? Jam’iyyar da ba ta damu da matasa ba, matacciyar jam’iyya ce. Matasa ne manyan gobe.”

Aminu Waziri Tambuwal

Kamar Atiku, Gwamnan Jihar Sakwwato, Aminu Waziri Tambuwal, a shekarar 2014, lokacin da yake ficewa daga APC zuwa PDP, ya ce, “Bisa dogaro da tsarin mulkin 1999 da kuma halin da PDP take ciki a jihata, Sakkwato, ina bayyana komawata Jam’iyyar APC.”

Sai dai a lokacin da aka tunkari zaben 2019, sakamakon takaddama da ubangidansa Aliyu Wamakko, Gwamna Tambuwal, ya ce ya fice daga Jam’iyyar APC ce, “Saboda na gamsu cewa babu wata kasa da za ta bunkasa matukar akwai rashin adalci da mummunan shugabanci; saboda haka ina bakin cikin rashin katabus da gazawa da rashin ganin kura-kuran da shugabanni suke tafkawa da suka zamo ruwan dare kan yadda ake tafiyar da Najeriya a yau.”

Rabi’u Musa Kwankwaso

Kwankwaso a jigo ne a Jam’iyyar PDP shekara da shekaru. An zabe shi Gwamnan Jihar Kano a karkashinta sau biyu a 1999 da kuma shekarar 2011. A shekarar 2014, ya bar jam’iyyar zuwa APC.

Lokacin da aka rika yada jitajita cewa yana shirin barin APC a shekarar 2017, Kwankwaso ya bayyana jita-jitar da “cin fuska.”

Shugaban Ma’aikatansa Kwamared Aminu Abdussalam a lokacin ya ce, “Babu lokacin da muka taba tunanin barin APC. Mun ji mamaki tare da matukar kaduwa lokacin da muka karanta labarin.”

Sai dai daga baya ya koma PDP. Kuma da yake bayani kan komawar ya ce, “Ni ’yantacce ne a yanzu kuma zan iya gwada sa’ata a wani wajen.

“Na san PDP ita ce babbar jam’iyya, kuma matukar suka bi dokokin dimokuradiyya, za a iya kayar da Buhari a cikin sauki, amma idan suka yi dauki-dora, suka tilasta wani dan takara a kan jam’iyyar za su fadi.”

Samuel Ortom

Gwamnan Jihar Binuwai Samuel Ortom, ya shiga Jam’iyyar APC jim kadan kafin zaben 2015 kuma ya lashe zaben Gwamna a karkashinta.

A lokacin ya ce, “A fili yake daukacin hanyoyin da aka bi wajen zabo ’yan takara cike suke da rashin adalci tun daga farko, lokacin da ya bayyana cewa an yanke shawarar a danne mafiya rinjayen ’ya’yan jam’iyyar (PDP) a zaben shugabannin unguwanni, bayan na bi duk hanyoyi da suka kamata a PDP, ya zama tilas in koma wata jam’iyyar.”

Sai dai da tafiyar ta baci, Ortom ya lashe amansa, inda ya ce, “Ina da matsaloli kuma shugabannin APC na kasa suna sane.

“Na tuntubi mazabuna ciki har da kansiloli 276 da suke nan. Baya ga Shugabar yankin Tarka da ta ce za ta je ta yi tuntuba, sauran duk sun ce ba su amince da ci gaba da zamata a APC ba.”

Godswill Akpabio

Wannan ‘nadirin’ dan siyasa ya bar PDP ce ta wata hanya da ba saban ba a lokacin da yake Shugaban Marasa Rijnaye na jam’iyyar a Majalisar Dattawa a shekarar 2018.

A lokacin da yake PDP, Akpabio, wanda ya yi Gwamnan Jihar Akwa Ibom har sau biyu ya ce, “Wannan jam’iyya (PDP) ta ’yan Najeriya ne. Don haka idan dan Najeriya daya ya bar jam’iyyar, wani dan Najeriyar zai zo, jam’iyyar ta ci gaba.”

Sai dai lokacin da yake barin jam’iyyar a shekarar 2018, Akpabio ya ce, “PDP ta yau ba ta da alkibla, kuma shugabanninta cike suke da girman kai.”

Femi Fani-Kayode

Masoyin APC na bayan nan shi ne Femi Fani-Kayode, wanda jigo ne lokacin kafa ta. Ya koma PDP jim kadan kafin zaben 2015.

Ya shafe shekara shida yana caccakar jam’iyyar, yana cewa, “Bisa abubuwan da muke gani, zan gwammace in mutu da in shiga mummuna kuma wadda bera ya harba da guba, sannan jirgin da yake kokarin nutsewa kamar Jam’iyyar Almajirai, (Almajiri Peoples’ Congress -APC).”

Sai dai da yake komawa APC a watan jiya ya ce, “Ba koyaushe ake cikin kuskure ba, don haka duk lokacin da kida ya canja sai rawa ta canja mu hada hannu mu kai kasar tudun mun tsira.”

Bello Matawalle

Matawalle ya zama Gwamnan Jihar Zamfara ne bayan ya fadi a zaben 2019, amma hukuncin Kotun Koli kan rikicin cikin-gida a APC ya ba shi damar zama gwamnan.

A shekarar 2019 ya yi alkwarin ba zai bar PDP ba, yana mai cewa: “Idan har na ci amanar PDP, kada Allah Ya sa in samu kwanciyar hankali a sauran rayuwata, na rantse da Allah. Idan zan iya barin PDP ko in cuci wadansu mambobinmu, Allah Ya kama ni.”

Amma tuni ya koma APC. Kuma lokacin da Matwalle ya koma APC a watan Yunin bana ya ce, “Siyasa aba ce ta bukata da amana.

“’Yan siyasa da dama sun canja jam’iyya. Don haka ba sabon abu ba ne. Na yanke shawarar canjawa ce don kawo karin zaman lafiya ga jihata.”

Ben Ayade

Ayade shi ne Gwamnan Jihar Kuros Riba. A watan Oktoban 2019 bayan ya lashe zabensa na gwamna ya ce, “Jam’iyyar (APC) a jihar ta yi kaurin suna wajen yin karairayi.

“Mafi ban dariya, jam’iyya kamar APC wadda take nuna kanta da babbar jam’iyyar adawa, ba za ta iya muhawara da gwamna a kan harkar shugabanci ba, sai ta zabi yin karya don samun tagomashin siyasa.”

Sai dai da yake komawa APC a watan Mayun bana, ya ce, “Saboda gani da sanin Shugaban Kasa da sadaukarwarsa ga kasar nan, kishin kasarsa da duk kokarin da yake yi wajen kai kasar nan matsayin da muke a yau, ya bayyana a wannan lokaci akwai bukatar mu hada hannu da shi domin gina Najeriyar da za mu iya alfahari da ita.”

Dave Umahi

Umahi shi ne Gwamnan Jihar Ebonyi, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas.

A shekarar 2018, ya ce, “Mutanen da suke canja sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, ya kamata su auna halayensu matukar ba akwai matsala a jam’iyyarsu ba ce.

“Zuwa yau da kuma gobe har zuwa dawowar Almasihu, ba za a samu rikici a PDP ba, domin haka babu dalilin da zan bar ta.”

Kamar sauran da suka karya alkwarinsu, Umahi, a watan Nuwamban bara ya ce, “Cin fuska ne a ce tun 1999 zuwa 2023, PDP ba ta ba Kudu maso Gabas damar tsayar da dan takarar Shugaban Kasa ba.

“Wannan shi ne matsayina kuma zan ci gaba da tsayawa a kan matsayina. Abin ba ya shafe ni ko ya shafi burina ba ne.”

Godwin Obaseki

Jim kadan da zama Gwamnan Jihar Edo, Obaseki ya samu matsala da magabacinsa, Adams Oshiomhole.

Daukacin zangonsa na farko daga wannan rikicin sai wancan.

A Oktoban 2019, Obaseki ya ce, “Idan wani rukunin mutane suka fara halayen da ba su kamata ba, kuma suka dauka za mu bar musu jam’iyyar; to su ne za su bar ta.”

A Yulin, 2021, Obaseki, wanda ya lashe zabensa zango na biyu a karkashin PDP, ya ce, “Daga dukkan alamu, ya bayyana PDP ce jam’iyyar da take bayar da dama ga jama’a take da alkibla da hangen da za ta mayar da kasarmu abar alfahari a tsakanin kasashen duniya.”

Peter Obi

Obi shi ne Gwamnan Jihar Anambra a karkashin Jam’iyyar APGA.

A Maris din 2013 ya ce, “Idan za ka kirga wadanda suka sadaukar da kansu ga APGA, babu yadda za ka yi haka ba tare da ambata ta ba.

“Ba ina da’awar ni na kafa APGA ba, amma na sadaukar da kai domin ta. Idan na bar ta, to na bar siyasa.”

A shekarar 2014, sai ya ce, “Kowa ya san a yau ba APGA din da muka sani ba ce. Tabbacin da na ba babban shugabanmu ba yana nufin zan yi biyayya ga jam’iyyar da wadansu mutane suka yanke shawarar mayar da ita makahon kare ba ne marar amfani.”

Obi shi ne Mataimakin Atiku Abubakar da ya tsaya takara Shugaban Kasa wa Jam’iyyar PDP a zaben 2019.