Ga jerin manyan ’yan siyasa da suka yi faduwar bakar tasa a rumfunan zabesnsu a zaben shugaban kasa da na Majalisun Tarayya da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban APC na Kasa
Cikin wadanda suka gaza kai banten nasu akwai shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, wanda a rumfar zabensa, Peter Obi na Jam’iyyar LP ya yi nasara da kuri’a 132.
Jam’iyyar ta sa dai ita ce ta zo ta biyu da kuri’a 85 a rumfar zaben da ke Angwarimu a Jihar Nassarawa.
A zaben majalisar dattijai kuma SDP ce ta yi nasara da kuri’a 159, sai APC 55, PDP 22, sannan LP 42.
A zaben majalisar Wakilai ma APC ta sha bugu a hannun SDP da kuri’a 159, yayin da APC ta samu 46.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na LP
Abokin takarar shugaban kasa na LP, Yusuf Datti Baba-Ahmed na cikin wadanda ba su kai labari ba a akwatinsu, inda Atiku na jam’iyyar PDP ya kayar da shi da kuri’a 102.
A rumfar zaben dan takarar ta kofar Gidan Iro Kaya da ke Tudun Wada a Zariya, LP ta samu kuri’a 54, yayin da APC ta bata kashi da 102.
Shugaban Majalisar Wakilai
A rumfar zaben Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gabjabiamila da ke Surulere a Legas, jam’iyyarsa ta APC ta sha kayi da kuri’a 59, a hannun LP wadda ta samu kuri’a 89.