✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manyan shari’o’i 5 da aka ‘kwanta’ kansu a Najeriya

Lamarin ya fara sanya damuwa a zukatan dangin wadanda abin ya shafa.

Tafiyar hawainiyar da ake yi a kan wasu manyan shari’o’i masu daukar hankali a kotuna daban-daban a Najeriya ta fara sanya damuwa a zukatan dangin wadanda abin ya shafa da kuma masu bibiyar lamarin.

Biyar daga cikin irin wadannan shari’o’i sun hada da na Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans; sai na Hamisu Bala da aka fi sani da Wadume da ake zarginsu da garkuwa da mutane.

Sai na Abdulmumin Danga, wani Kwamishina a Jihar Kogi da ake zargi da cin zarafin budurwa; da na Andrew Ogbuja, wanda ake tuhuma bisa zargin cin zarafi da kisan wata budurwa mai suna Ochanya Ogbanje; yayin da shi kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ake tuhumarsa da laifin almundahana.

Masu amfani da kafofin sadarwar zamani a Najeriya da dama suna bibiyar yadda shari’o’in za su kaya.

Abin da jama’a suke tsammani daga wadannan shari’o’i shi ne a yi maza a yanke hukunci don kawar da tunanin mutanen kasa game da zargin tafiyar hawainiya a fannin shari’a tare da magance tuhumomin manyan laifuffuka a kasar nan.

Bincike ya nuna dalilai da dama ne suka jawo jinkiri da tafiyar hawainiya a shari’o’in da wasu an faro su ne tun shekarar 2017, duk da irin bibiyar da ’yan Najeriya suke yi wa shari’o’in a kafofin sadarwa.

Daga cikin matsalolin da suka haifar wa sashin shari’a tarnaki akwai cutar Coronavirus, wasu kuma daga bangaren lauyoyi, wasu daga zanga-zangar #EndSars, yayin da wasu kalubalen suka fito bisa dalilin yajin aikin ma’aikatan shari’a da kungiyarsu ta kasa ta gudanar.

Evans

Chukwudumeme Onwuamadike

Duk da irin tayar da jijiyar wuya da aka yi ta yi, sakamakon kama shi da aka yi a shekarar 2017 da kuma gabatar da shi a gaban shari’a, har zuwa yau (2021) ba a kammala shari’arsa ba.

Fitaccen wanda ake zargi da garkuwa da mutane, Evans, wanda ake yi wa lakabi da ‘Biloniyan Mai Garkuwa da Mutane’ an gabatar da shi a gaban kotuna biyu; daya a Kotun Jihar Lagos da ke Ikeja, daya kuma a Igbosere, bisa tuhumomin da suka hada da yin garkuwa da kisan kai da kuma yunkurin kisa.

Sauran wadanda ake tuhuma tare da Evans akwai Uche Amadi da Ogechi Uchechukwu da Chilaka Ifeanyi da Okwuchukwu Nwachukwu da kuma Bictor Aduba.

Dukkansu suna fuskantar shari’a ne bisa tuhumar sace Shugaban Kamfanin Harhada Magunguna na Maydon Pharmaceutical Limited ne mai suna Donatus Dunu, a shekarar 2017.

Kamar sauran shari’o’i, cutar Kwarona ta haifar da jinkiri a kansu a bara, inda a watan Agustan bara aka fara yada jita-jitar yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan amsa laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa.

Sai dai bincike ya tabbatar ba a yanke masa hukunci ba, maimakon haka ma; alkalin kotun, Mai shari’a Hakeem Oshodi na Babbar Kotun Jihar Legas, ya yi watsi ne da bukatar da lauyoyinsa suka mika na wanke shi da wadanda ake tuhumarsu tare.

Majiyoyi da dama sun ce kone wasu kayayyakin kotu, ciki har da takardu da wasu hujjoji a lokacin zanga-zangar #EndSars sun shafi shari’ar Evans, wanda hakan yake nuna maido da shari’ar sabuwa fil, da ta kunshi sake gabatar da wasu takardun.

Shari’ar da aka fara a Kotun Ikeja a watan Yuni, an dakatar da ita ce sakamakon rashin halartar shaidar wanda ake tuhuma, wanda lauyan wanda ake tuhuma, Oyekunle Falabi, ya shaida wa kotu cewa ba a samunsa ta tarho.

Hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da Evans yake musanta cewa shi mai sata da yin garkuwa da mutane ne, face dan kasuwa mai gudanar da halattaccen kasuwanci wanda aka tilasta masa aikata laifuffuka.

Ana sa ran ci gaba da shari’arsa ce a watan Satumba.

Wadume

Yadda aka kama Wadume a Kano
Wadume

Shari’a ta biyu ita ce ta Wadume, wanda yake fuskantar shari’a a Babbar Kotun Tarayya da take Abuja, tuhume-tuhume 13 da ake zarginsa a kansu da suka hada da zargin ayyukan ta’addanci da sata da garkuwa da mutane a Jihar Taraba.

Wadanda ake tuhuma tare da Wadume sun hada da Sufeta Aliyu Dadje, wani dan sanda da ofishinsu yake Ibi a Jihar Taraba da Auwalu Bala (Omo Razor) da Uba Bala (Uba Belu) da Waziri (Baba Runs) da Zubairu Abdullahi (Basho) da Hafizu Bala (Maiwalda) da Rayyanu Abdul da kuma wadansu sojoji bakwai.

Jami’an sojin da ake tuhumarsu tare sun hada da Kyaftin Tijjani Balarabe da David Isaiah da Ibrahim Mohammed da Bartholomew Obanye da Mohammed Nura da Okorozie Gideon da Marcus Michael da Nbenaweimoeimi Akpagra da Abdulahi Adamu da Ebele Emmanuel.

Kafin yajin aikin ma’aikatan kotun da ya yi sanadiyyar tsayar da shari’ar, an sa ran Wadume ya fara kare kansa ne a ranar 8 ga Mayun bara, bayan kammala gabatar da zarge-zargen da ake yi masa tare da gabatar da shaidu shida a watan Maris.

’Yan sanda sun yi zargin cewa sojojin sun taimaka masa wajen kubucewa bayan ’yan sandan suka yi kama shi a kan hanyarsu ta maida shi Ibi daga Jalingo a watan Agustan 2019, abin da ya haddasa mutuwar ’yan sanda uku da wadansu fararen hula biyu.

Wadume ya gude ne a ranar 6 ga Agustan 2019 kafin a sake kama shi a Kano a ranar 19 ga Agustan 2019.

An samu ce-ce-ku-ce a shari’ar bayan ware sojojin da ake zargin sun taimaka masa, don yi musu shari’arsu daban.

Bayan cire sunayen sojoji da ake zargin, sai lauyan Gwamnatin Tarayya, Magaji Labaran ya shigo da zarge-zarge 13 ga ragowar fararen hular.

Wannan ce-ce-ku-ce ya tilasta wa Antoni Janar na Kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami yin karin haske cewa kotun sojoji za ta gudanar da shari’ar jami’anta kan halattaccen tsari, tare da tabbatar da aikata adalci a shari’ar.

Malami ya ce an fitar da sunayen sojojin ne don kariya ga hakkin dan Adam na sauran wadanda ake tuhuma kafin lokacin da hukumar soji za ta gabato da nata.

Tuni mutum shida suka ba da shaida a kotu kan yadda aka kama bindigogi shida a wajen Wadume da mutanensa.

Bayan Gwamnatin Tarayya ta kammala gabatar da karar da take yi, kotun ta sanya ranar 4 ga Nuwamba don fara sauraron wadanda ake tuhuma da kare kansu kan zargin da ake yi musu.

Lauya mai kare wadanda ake tuhuma, Mohammed Tola ya ce: “A shirye muke don ba da cikakkiyar kariya.”

Ogbuja

Andrew Ogbuja

Mutum na gaba da ake bibiyar shari’arsa shi ne Ogbuja, wanda ake zargi da aikata fyade da kisan wadansu mutum biyu.

Sai dai shari’ar kisan yarinya ’yar shekara 13 da ake kira Ochanya Ogbanje, wacce Babbar Kotun Tarayya da ke garin Makurdi ke gudanarwa ta hadu da cikas, bayan zama na karshe da aka yi a watan Yunin bara.

A watan Oktoban shekarar 2018 aka wayi gari da labarin da ya tayar wa jama’a hankali bayan samun Andrew Ogbuja, da dansa Victor wanda ya tsere bisa zargin hannunsu a mutuwar Ochanya bayan lakada mata dukan da ya zamo sanadiyyar ajalinta a ranar 17 ga Oktoban 2018.

Ogbuja, wanda ake zargi, malami ne a Kwalejin Kimiyya da Sana’a da ke garin Ugbokolo a Jihar Binuwai, yayin da dansa Victor da ake nema ruwa a jallo yake karatu a matakin karshe a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Makurdi, babban birnin jihar.

Matarsa, Felicia, mai shekara 43, Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce take tsare da ita bisa tuhumomi biyu da suka hada da bata yarinyar ta hanyar tilasta mata yin lalata da kuma nuna halin ko-inkula da ya kai ga sababin mutuwarta.

Mai shari’a M. O. Olajunwa ya yi watsi da bukatar da wadanda ake zargi suka shigar na a yi watsi da shari’ar a bara, inda ya nuna gamsuwa da hujjojin da aka gabatar masa kuma ya ce dole su kare kansu daga zarge-zargen.

Ana sauraron ci gaba da shari’ar a kowane lokaci daga yanzu.

Danga

Abdulmumini Danga

Shari’a ta gaba da ake ci gaba da bibiya ita ce wacce ake tuhumar Kwamishinan Albarkatun Ruwa ta Jihar Kogi, Abdulmumini Danga, kan zargin cin zarafin wata da ake kira Elizabeth.

Babu wani cikakken bayani game da batun in ban da janyo hankalin jama’a da dama da suka yi tofin Allah tsine ga al’amarin.

An ruwaito cewa yarinyar ta bukaci taimakon kudi ne daga wajen Kwamishinan a kafar sada zumunta ta Facebook, inda shi kuma ya sa aka kamo ta tare da azabtar da ita.

Majiya mai tushe ta tabbatar da gayyatar da ’yan sanda suka yi wa Kwamishinan a kan batun a daidai lokacin da yake da dumi-dumi, amma tun daga nan ba a sake jin komai game da batun ba.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa an kai shari’ar ce zuwa wata Babbar Kotun da take Abuja inda ta bayar da belin wanda ake zargi, abin da ya sanya wadansu kungiyoyi masu zaman kansu da ba su gamsu da lamarin ba suka sanya alamar tambaya kan dacewar bayar da belin, inda suka ce tuhumar ba ta cancanci bayar da beli ba.

Babachir Lawal

Babachir Lawal

Shari’a ta karshe daga cikin shari’o’i 5 masu daukar hankali a kasa ita ce ta tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal kan zargin yin babakere da almundahana da kudin yankar ciyawa da suka kai Naira miliyan 544 kuma ake zargin ya bai wa kamfanonin da ake alakanta shi da su masu suna Rholavision Engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd.

An gurfanar da shi bisa tuhumomi 10 a watan Fabrairun shekarar 2019 a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sannan an sake gabatar da shi a gaban Mai shari’a Charles Agbaza a ranar 30 ga Nuwamban 2020 bayan rasuwar alkalin da yake jagorantar shari’ar, Mai shari’a Jude Okeke.

Sauran wadanda ake tuhuma tare da shi sun hada da kanensa mai suna Hamidu Lawal da Suleiman Abubakar da Apeh Monday da kamfanonin biyu.

An dage ci gaba da shari’arsa zuwa ranar 4 ga Yuni bayan kotu ta ki amsar rahoton binciken kwkwaf da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin ArzikiTu’annati (EFCC).

Sannan lauyansa ya ki yarda da takardun shaidar da aka gabatar wadanda aka samar daga kwamfuta bisa dalilin cewa sun saba wa dokar shekarar 2004 .

Ana sa ran ci gaba da shari’ar a watan Oktoban bana.

Dalilai da dama suka haifar da tafiyar hawaniyar – Lauyoyi

Yayin da yake bayyana matsayinsu kan dalilan tafiyar hawainiya a yawancin manyan shari’u a Najeriya, wani lauya mai suna Sunusi Musa, ya ce tsarin gudanar da shari’un manyan laifuffuka a Najeriya ya tanadi gabatar da manyan shari’a kullum ba tare da jan kafa ba har a kammala, amma shari’ar daidaiku ba za su rasa mabambanta dalilian da suka sa ake samun tsaiko a kai ba.

Shi ma Hameed Ajibola Jimoh, ya ce cinkoso a gidajen yari na wadanda ake sauraron shari’arsu suna da alaka da jan kafar da ake samu wajen kammala wasu shari’o’in.

“Muna da shari’u da dama a kotuna da matsalolin cutar Coronavirus da na zanga-zangar #EndSars da yajin aikin ma’aikatan kotu suka taimaka wajen rashin kammala su.

“Idan ka lura da mai kokarin kare kansa a kotu za ka ga yana damuwa tare da zakuwa wajen ganin an gaggauta shari’a, amma idan mai kare kansa yana da guntun kashi a tare da shi za ka ga ba ya so a ci gaba da shari’ar,” inji shi.

Daga John C. Azu (Abuja), Adelanwa Bamgboye (Legas), Adama John (Lakwaja) da Hope Abah (Makurdi) da Ahmed Ali