✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manyan makaman ’yan sanda 178,459 sun yi batar dabo

An gano bindigogi kirar AK-47 guda 88,078 da kirar Pistol guda 3,907 sun yi batar dabo.

Majalisar Tarayya ta fara bincike kan bacewar bindigogi kirar AK-47 guda 88,078 daga rumbun ajiyar makaman Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.

Majalisar ta yi ittifakin gudanar da binciken ne bayan Ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya ya bankado bacewar manyan makaman ’yan sanda 178,459 a yayin binciken da ofishin ya gudanar kan Rundunar a shekarar 2019.

“Daga cikin makaman akwai bindigogi kirar AK-47 guda 88,078 da kuma manyan bindigogi da kirar pistol guda 3,907 da suka yi batar dabo zuwa watan Janairun 2020,” inji Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Hon. Toby Okechukwu.

Batun binciken ya taso ne bayan Hon. Okechukwu ya bayyana wa zauren Majalisar cewa rajistar makaman da ke rumbunan ajiyar makaman rundunar ya nuna cewa makamai 178,459 sun yi batar dabo zuwa watan Disamban 2018.

“Binciken ya kuma gano cewa hukumar ’yan sanda ta kasa adana bayanan makaman da wa’adin aikinsu ya kare da kuma wadanda ba za su gyaru ba, a sakamakon rashin bin ka’ida aiki da jami’an rundunar suke yi.

“Sun ki bayar da bayanan irin wadannan makamai domin kwamitin bincike ya tantance,” inji shi.

A cewarsa,hakan na nufin ba a san hakikanin adadin makaman ’yan sanda da suka bace ba saboda rashin cikakkun bayanan da suka dace.

Ya ce hukumomin ’yan sanda sun kuma gaza gabatar da bayanan makaman da takardun da suka danganci kudaden da aka kashe wajen sayen su domin tantancewa.

Dan majalisar ya ce duba da yanayin tabarbarewar sha’anin tsaro a Najeriya, akwai yiwuwar wasu daga cikin makaman sun fada hannun miyagun iri.

Daga karshe Majalisar ta umarci Shugaban ’Yan Sandan Naejriya da ya gaggauta gudanar da bincike tare da daukar mataki a kan duk masu hannu a bacewar makaman na ’yan sanda.