Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya gaji da yi wa manyan hafsosihn tsaron kasar uzuri saboda gazawarsu wajen magance matsalar tsato.
Da yake bayani kann gazawar hafsoshin tsaron a ganawarsa da su ranar Laraba, Buhari ya ce ya gama yi musu uzuri, yanzu ya rage nasu su gyara, ko su san inda dare ya yi musu.
Mai Ba Shugaban kasa Shawara Kan Tsaro, Babagana Mongunu ya ce, “Shugaba Buhari ya kuma fada masu cewa ba zai lamunci ci gaba da sukurkucewar al’amuran tsaro ba, kuma babu wanda ya tilasta shi yin aiki da su, don haka ya rage nasu su yi abin da ya kamata”.
Buhari ya kuma umarci Mongunu da ya yi aiki tare da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Kasa Mai Yatsu Isa Pantami domin magance matsalar tsaro.
- Buhari ya ba ’yan Katsina hakuri kan matsalar ’yan bindiga
- Matsalar tsaro: An kama jarogran zanga-zangar da aka yi a Katsina
Ya kara da cewa wajibi ne a magance matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi da kananan makamai, da kuma hana amfani da layukan waya marasa rijista domin idan ba hakan aka yi ba, ba za a kai ga gaci ba.
Hakan na zuwa ne washegarin ranar da masu zanga-zanga kan tabarbarewar tsaro suka fito kan tituna a jihar Katsina, mahaifar shugaban inda ‘yan bindiga suka kashe mutane da dama, suna kira gare shi da gwamnan jihar Aminu Bello Masari su ajiye mukamansu.
Matsalar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun addabi yankin Arewa Maso Yamma, lamarin da ake ganin gwamnati ta yi kasa gwiwa wajen magancewa.
Masharhanta sun sha kira ga Shugaba Buhari da ya sallami manyan hafsoshin tsaron saboda kasa a aikin da ya ba su. Suna kuma ganin wajibi ne a yi amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen dakilewa da kuma yakar masu aikata manyan laifuka, wadanda su ma suke amfani da su domin yin aika-aika.
Kazalika sun ce dole a kawo karshen matsalar yawaitar makamai ba bisa ka’ida ba a hannun mutane da kuma ta’ammuli da miygaun kwayoyi muddin ana so a yi nasara wurin yakar miyagun ayyukan.