✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manya suna sha kasa a zaben majalisa

Yayin da akasarin ’yan Najeriya suka fi damuwa da zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a makon jiya, an samu gagarumar juyin waina inda manya…

Yayin da akasarin ’yan Najeriya suka fi damuwa da zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a makon jiya, an samu gagarumar juyin waina inda manya suka sha kasa a zaben Majalisar Dokoki ta Kasa da ta kunshi Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

Zaben wakilan Majalisar Dokoki ta Kasar ya zo da ba-zata, inda manyan ’yan takara suka fadi, yayin da wadanda ake ganin za su sha kasa suka tsallake.

Daga cikin wadanda suka fadi a zaben akwai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Sarki da gwamnonin jihohin Gombe da Oyo masu barin gado da sauransu.

Wadannan manyan ’yan takara lissafi ya rikirkice musu ne a lokacin da aka fara fitar da sakamakon zaben Majalisar Dattawa da ta Wakilai a ranar Asabar da Lahadin da suka gabata.

Babban wanda shan kasar ya fi girigizawa shi ne Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Abubakar Bukola Saraki, wanda ya sha kaye a hannun tsohon abokin adawarsa Malam Ibrahim Yahaya Oloriegbe na Jam’iyyar APC. Kayen da Saraki ya sha ya ba mutane mamaki ganin yadda zuriyarsa ta dade tana juya akalar siyasar tsohuwar Jihar Kwara da ta hada da Kogi ta yanzu da kuma Jihar Kwara ta yanzu, sannan ya zamo jagoran siyasar jihar a shekarar 2003.

A shekarar 2011 ce, Sanata Bukola Saraki, ya kawo karshen ikon daular siyasar mahaifinsa Alhaji Abubakar Olusola Saraki, wanda ya rika juya siyasar jihar kusan shekara 40 da suka gabata, bayan mahaifin nasa ya yi amfani da tasirinsa wajen dora shi a kujerar Gwamnan Jihar sau biyu a jerer.

Bukola ya turje wa mahaifinsa kan yunkurin tsayar da kanwarsa Gbemisola, inda ya tsayar da Gwamnan Jihar mai barin gado Alhaji Abdulfatah Ahmed.

Wannan ne ya kawo karshen daular Olusola Saraki da ake yi wa kirari da Oloye, kuma ake bayyana shi da cewa:  “Duk inda Saraki ya yi, Kwara tana biye da shi.”

Bayan Sanata Bukola Saraki, ya karbe daular siyasar iyalan Saraki, sai ga shi kasa da shekara takwas, ya rasa ikon da yake da shi a siyasar jihar.

Juyin Juya-Halin ‘O to ge’ a Kwara

Al’ummar Jihar Kwara sun kaddamar da wani Juyin Juya-Hali da suka kira da ‘O to ge’ ma’ana ‘Ya isa haka’ a kokarinsu na rusa daular siyasa ta iyalan Saraki da Sanata Bukola Saraki ke jagoranta. Kuma wannan Juyin Juya-Hali ne ya yi waje da dukan ’yan takarar da Jam’iyyar PDP ta tsayar a zaben Majalisar Dokoki ta Kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Wannan kalma ta ‘O to ge’ ta rika watsuwa kamar wutar daji inda a karshe ta raba Sanata Bukola Saraki da kujerarsa a zaben da aka gudanar a ranar Asabar din, inda Malam Ibrahim Oloriegbe, na Jam’iyyar APC, ya kada Shugaban Majalisar Dattawan a Mazabar Kwara ta Tsakiya da kuri’a dubu 123 da 808, yayin da Sanata Bukola Saraki ya samu kuri’a, dubu 68 da 994, wato Oloriegbe ya yi masa tazarar kuri’a dubu 54 da 814.

Wadansu daga cikin jiga-jigan siyasar Jihar Kwara da suka jagoranci tawayen ‘O to ge’, sun hada da dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC, Malam Abdulrahman AbdulRazak da Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed, wanda ya sha kokawa kan daular siyasar gidan Saraki har ya taba bayyana cewa, “Babban matsalarmu a nan ita ce, yadda za a kawo karshen yadda wani gida ya kwashe shekara 40 cikin 50 yana juya akalar siyasar jihar yadda ya so.”

Kafar labarai ta Cable ta ce bincikenta ya nuna cewa da yawa masu jefa kuri’a a jihar a wannan zabe ba su san ma sunan babban mai ja da Saraki a takarar ba, su dai taken, ‘O to ge,’ ne ya ja su.

Sauran wadanda faduwar tasu ta bayar da mamaki su ne Gwamna Ibrahim Hassan  Dankwambo na Jihar Gombe da kuma Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyop, da suka tsaya takarar kujerar sanata a daidai lokacin da suke kammala wa’adinsu na biyu a matsayin gwamnonin jihohinsu.

Dankwambo na Jam’iyyar PDP ya gaza lashe kujerar Sanata a Mazabar Gombe ta Tsakiya ce bayan ya sha kasa a hannun Alhaji Sa’idu Alkali na Jam’iyyar APC, yayin da Ajimobi na Jam’iyyar APC ya sha kasa a hannun dan takarar PDP Mumammed Kola Balogun a Mazabar Oyo ta Kudu.

Gwamna Ajimobi, ya taba zama sanata a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007.  Alkali ya samu kuri’a dubu 152 da 546, yayin da Dankwambo ya zo na biyu da kuri’a dubu 88 da 16. Shi kuma Kola Balogun na PDP ya samu kuri’a dubu 105 da 720, shi kuma Ajimobi na APC ya samu kuri’a dubu 92 da 217.

Wani Sanata da faduwarsa ta zo a ba za-ta shi ne Sanata Andy Ubah, wanda ya rika yi wa Shugaba Buhari kamfe bisa fatar in y samu nasara ya zama Shugaban Majalisar Dattawa idan Buhari ya zarce saboda shi ya fito ne daga yankin Ibo. Amma kwatsam sai ya sha kasa a hannun fitaccen dan kasuwar nan Cif Ifeanyi Ubah na sabuwar Jam’iyyar Young Progressibe Party (YPP) domin wakiltar Anambra ta Kudu. Ifeanyi Ubah ya kuma kayar da dan uwan Andy Uba wato Chris Uba wanda ya tsaya takara a karkashin Jam’iyyar PDP.

Sanata Mao Ohuabunwa na PDP mai wakiltar Abiya ta Arewa shi ma ya sha kasa a hanun tsohon Gwamnan Jihar Cif Orji Uzor Kalu na Jam’iyyar APC duk da cewa yankinsu yanki ne da Jam’iyyar PDP ta yi kaka-gida. Sannan Sanata Rafiu Ibrahim na PDP da ke wakiltar Kwara ta Kudu, wanda kuma shi ne ya yi takarar da Gwamnan Jihar Abdulfatah Ahmed a zaben fid da gwani, kuma Sanata Bukola Saraki ya umarce Gwamnan ya hakura ya bar masa, shi ma bai kai labara ba.

Daga Jihar Bauchi Sanata Nazif Gamawa na PDP da Sanata Isah Hamma Misau na PDP su ma sun sha kasa a zaben na ranar Asabar duk da cewa bakin jinin da ake zargin Gwamnan Jihar ke da shi zai iya ba su nasara. Sanatocin biyu sun sha kasa a hannun ’yan takarar APC Alhaji Adamu Bulkachuwa daga Bauchi ta Arewa inda Nazifi ya fito da kuma Alhaji Halliru Jika daga Bauchi ta Tsakiya inda Hamma Misau ya fito. Alhaji Suleiman Hunkuyi na PDP mai wakiltar Arewacin Kaduna da Shehu Sani na PRP mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ma, sun sha kasa. Sai kuma Sanata Binta Masi Garba,ta APC daga Adamawa ta  Arewa da Barnabas Gemade na SDP daga Benuwai ta Arewa da George Akume tsohon Gwamna kuma Sanata daga Benuwai duk sun sha kasa a zaben na Asabar Yawancin sanatocin musamman na yankin Arewa, an zabe su a wancan karon a karkashin Jam’iyyar APC ce, amma daga baya saboda rikici tsakaninsu da gwamnoninsu ko wani sabani na daban suka fice zuwa PDP, ko wata jam’iyyar daban kamar Barbabas Gemade wanda ya koma SDP.

Wani wanda faduwarsa ta zo a ba-zata shi ne tsohon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa Dokta Godswill Akpabio, wanda ake ganin an yi zawarcinsa ne zuwa APC domin ya kara wa jam’iyyar karfi a yankinsa, amma sai aka doke shi a takararsa ta sanata. Da yawan mutane suna tunanin shi ne zai maye gurbin Sanata Bukola Saraki a matsayin Shugaban Majalisar in da ya samu nasara.

Shi ma Sanata Shehu Sani na PRP, ya sha kasa ce a hannun Malam Uba Sani na Jam’iyyar APC, Shehu Sani dai yana asakala da Gwamna Nasir El-Rufa’i tun kafa gwamnatin APC a jihar.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Mista Barnabas Bala Banted, wanda ya ce ba zai koma matsayinsa na Mataimakin Gwamna ba don hakan ya tsaya takarar Sanata a Kudancin Kaduna, ya kasa kai labari inda Sanata mai ci, Danjuma La’ah Sardaunan Kagoro ya doke shi.

Wanda zabensa ya zo da ba-zata a bangaren wadanda suka yi nasara shi ne Sanata Dino Melaye na Jam’iyyar PDP wanda ya doke Sanata Smart Adeyemi na Jam’iyyar APC da rata mai yawa duk da tsamar da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Akwai kuma wadanda ba kayar da su aka yi ba a zaben illa sun ajiye kwallon mangwaro ne suka huta da kuad da suka hada da Sanata Ben Murray-Bruce da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da sauransu.

Sannan a cikin sanatocin da suka dawo majalisar Sanata Ali Ndume, wanda majalisar a karkashin jagorancin Bukola Saraki ta dakatar da shi na shekara guda da kuma Sanata Omo-Agege, wanda shi ma aka taba dakatar da shi, har aka zarge shi da dauke sandar majalisar.

Akwai kuma sababbin zuwa majalisar da suka hada da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawa da Rochas Okorocha na Jihar Imo da Abdul’aziz Yari na Zamfara da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau daga Jihar Kano da sauran sababbin zuwa da dama.

A bangaren Majalisar Wakilai zaben da aka gudanar a Jihar Bauchi ne ya fi kowanne jan hankali, inda Jam’iyyar PRP ta kama manyan garuruwan jihar biyu kuma cibiyoyin manyan masarautun jihar wato Bauchi da Katagum. A Bauchi dan Majalisar Jihar a karkashin Jam’iyyar APC da ake zargin Gwamnan Jihar Mohammed Abdullahi Abubakar ya hana shi tsayawa takarar Majalisar Wakilai ne ya koma PRP kuma ya kai bantensa, inda ya kayar da ’yan takarar jam’iyyun APC da PDP da suke da karfi. Sai kuma Katagum inda dan takarar Jam’iyyar PRP ya kayar da dan Majajisar Wakilai mai ci. Sannan da kyar Jam’iyyar APC ta kwaci kanta a hannun Jam’iyya ANPP a zaben Sanatan Bauchi ta Arewa. Amma ta yi rawar ganin kawo Sanatan Bauchi ta Kudu duk da cewa akwai rikici kan dan takarar kujerar. Sanata Lawal Yahaya Gumau ne Jam’iyyar APC ta tsayar takara, sai dai ana saura wuni biyu a fara kada kuri’a bayan dage zaben farko, sai Alhaji Ibrahim Zailani ya gabatar da takardar umarnin kotu cewa shi ne dan takarar jam’iyyar, lamarin da ya sa Hukumar INEC ta ki bayyana sunan wanda ya ci zaben illa Jam’iyyar APC.

Wane ne zai zama Shugaban Majalisar Dattawa

Ganin Sanata Bukola Saraki na gab da barin shugabancin Majalisar Dattawa kuma Jam’iyyar APC ta samu rinjaye sosai a zaben bana inda yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu suka dan tagaza, akwai yiwuwar Sanata Rochas Okorocha da Sanata Orji Uzor Kalu wadanda suka lashe zaben a Jam’iyyar APC su nemi tsayawa takarar kujerar. Sai dai kuma akwai kalubale a kansu ganin cewa su sababbin zuwa ne. Sannan kasancewar Jam’iyyar APC a baya ta tura kujerar ga yankin Arewa maso Gabas kafin su Sanata Bukola Saraki su yi mata bore su hada kai da ’ya’yan PDP su juyar da ita zuwa Arewa ta Tsakiya, akwai yiwuwar sanatocin da suka fito daga yankin Arewa maso Gabas su nemi a ba su matsayin. Idan haka ta samu to Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawal da a baya jam’iyyar ta so da kujerar zai iya nema. Sanata Ahmed Lawan tsohon sanata ne kuma yana da kima da mutunci a idon mutane da ma sauran sanatoci. Sannan ga Sanata Danjuma Goje daga Jihar Gombe wanda shi ma ake rade-radin yana son hayewar kan kujerar, kuma a wannan karo ya yi kokari wajen ganin jiharsa ta Gombe ta dawo Jam’iyyar APC ta hanyar kawo sanatoci uku da daukacin ’yan Majalisar Wakilai da suka fito daga jihar. Sannan akwai yiwuwar tsohon Shugaban Majalisar Sanatocin Arewa Sanata Abdullahi Adamu daga Jihar Nasarawa wanda ya fito daga Arewa ta Tsakiya zai yi kokarin ganin yah aye kujerar.