Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).
Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, mun dakata a karkashin kanun ‘Kwanakin da aka haka azumi a cikinsu’ inda muka fara gabatar da hanin azumtar ‘Ranakun Idi Biyu’, yau ga ci gaba:
2. Ranakun Tashrik (Shanyar Nama): Wato ranaku uku bayan ranar Idin Layya, ke nan rana ta biyu da ta uku da ta hudu, ranakun Layya.
Bai inganta a yi azumin tadawwu’in wadannan kwanaki ba, saboda zancen mafi yawa daga ma’abuta ilimi, dalilin Hadisin Nubaishatal Hazliy (Allah Ya yarda da shi), ya ce, ‘Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ranakun Tashriki, ranaku ne na ci da sha.” Sahihin Hadisi ne da Muslim ya fitar a Hadisi na 1,141.
Haka nan an samo daga Abu Murrata ‘Maulan’ Ummu Hani cewa shi da Abdullahi dan Amr, (Allah Ya yarda da su), sun shiga wajen mahaifinsa, Amru dan Aas, (Allah Ya yarda da shi), sai ya gabatar musu da abinci, ya ce, “Ku ci.” Sai shi Abu Murrah ya ce, “Ni ina azumi.” Sai Amr ya ce, “Ci, wadannan kwanukan su ne Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yake umurtar mu da mu ci abinci, kuma yana hana mu azumtar su.” Sahihin Hadisi ne da Abu Dawud, Hadisi na 2,418; da Ahmad, mujalladi na 4, Hadisi na 197, suka fitar.
Sai dai an yi rangwame ga mai aikin Hajjin da bai samu abin yin hadaya ba, ya yi azumi a cikin kwanukan, kamar yadda aka fada a bayanin aikin Hajji, saboda Hadisin da aka samo daga A’ishatu da dan Umar (Allah Ya yarda da su), yayin da suka ce, “Ba a yi rangwame ga kowa ya yi azumi a ranakun Tashrik ba, sai dai wanda bai samu (abin yin) hadaya (a lokacin aikin Hajji) ba.” Sahihin Hadisi ne da Buhari ya fitar a hadisai na 1,997-1,998.
3. Kebance ranar Juma’a da azumi: Yin azumi a ranar Juma’a kebance bai inganta ba, sai da in mutum zai azumci ranar gabaninta (ranar Alhamis) ko ranar da ke gabanta (ranar Asabar) tare da ita. Ko kuma ya kasance mai yin azumin Annabi Dawuda (Alaihis Salam), wato ya azumci yau ya ci abinci gobe, lamarin da zai sa ya azumci Juma’a a kebance, to, wannan babu wata matsala a kan haka.
An samo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce, ‘Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Kada dayanku ya azumci ranar Juma’a kawai, sai dai in zai azumci ranar kafin ta ko bayan ta.” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,985; da Muslim, Hadisi na 1,144, suka fitar.
Haka nan an samo daga Juwairiyyatu bintu Alharis (Allah Ya yarda da ita), cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya shiga wajenta a ranar Juma’a, alhalin tana azumi, sai ya ce mata, “Jiya kin yi azumi?” Sai ta ce, “A’a.” Sai ya ce, “Kina da nufin za ki yi azumi gobe?” Sai ta ce, “A’a.” Sai ya ce, “To, ki ci abinci.” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,984; da Muslim, Hadisi na 1,143, suka fitar.
Mazhabobin Imam Shafi’i da Ahmad sun tabbatar da haka, amma Imam Abu Hanifa da Malik sun saba musu da suka ce, “Ba makaruhi ba ne.” (Hashiyar Ibnu Abidin, mujalladi na 3, shafi na 336; da Almuwadda, mujalladi na 1, shafi na 330; da Sharhu Muslim, mujalladi na 3, shafi na 210; da Almughniy, mujalladi na 4, shafi na 427).
Su Hanafiyya sun ba da dalilinsu ne saboda Hadisin Ibn Mas’ud (Allah Ya yarda da shi), cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance yana azumtar kwanuka uku na tsakiyar kowane wata, kuma kadan ne yakan ci a ranar Juma’a.” Isnadin Hadisi ne ‘layyin’ (lange-lange -mara karfi), wanda Abu Dawud, Hadisi na 2,450; da Tirmizi, Hadisi na 742; da Annasa’i, Hadisi na 2,367; da Ibnu Majah, Hadisi na 1,725 suka fitar ta hanyar
Asim daga Zir bn Hubaish daga dan Mas’ud. Shi Asim yana da ‘awham’ (abubuwan da ba su da tabbas) kuma akwai magana (mukal) game da riwayarsa daga Zir.
Sannan ana iya yin jawabi daga jawabai game da haka, cewa abin da ya bayyana game da wannan Hadisi shi ne cewa da’ifin Hadisi ne. Ingantacciyar magana kuwa ita ce Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya kasance yana azumtar ranar da ke gabanin ranar Juma’a ko kuma ranar bayanta tare da Juma’ar. Idan kuwa aka yi dubi da haka, lallai ba za a iya cika dalili ba da cewa ana iya kebantar ranar Juma’ar da azumi. Sannan kuma wannan aiki ne, wancan kuwa magana ce, kuma ana gabatar da magana ne a kan aiki a yayin da suka yi ga-da-ga, alhali kuma ba za a iya hada su a yi aiki da su a lokaci guda ba. (Altalkhis, mujalladi na 2, shafi na 216; da Subulus Salam, mujalladi na 2, shafi na 347).
Shi kuwa Imam Malik (Allah Ya yi masa rahama), Hadisin hanin haka bai kai gare shi ba, saboda haka wanda yake da ilimin hujja ya shiga gaban wanda ba shi da ilimin ta.
Fa’ida: Idan ranar Juma’a ta dace da ranar Arafa, babu laifi a kebanci ranar da azumi, saboda hanin da aka yi na ganganta kebance ranar ne tun asali, kamar yadda bayanin haka ya zo a littafin Sharhul Umdah, mujalladi na 2, shafi na 652; da Azzad, mujalladi na 2, shafi na 86.
4. Ranar shakka: Ba ya inganta a gabaci Ramadan da azumin kwana daya ko biyu da nufin kewayewa da Ramadan din, don a samu dacewa da an shiga Ramadan, wato azumin tarbe ke nan. Wannan hanin kuwa bai shafi wanda yake da al’adar azumtar misali Litinin da Alhamis ko azumin Annabi Dawud (Alaihis Salam), ko wanin makamancin haka ba. In da ba irin wadannan dalilai to, azumtar hakan haramun ne saboda Hadisin Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Kada dayanku ya gabaci Ramadan da azumin rana daya ko biyu, sai dai mutumin da ya saba yin wani azumin tadawwu’i, to shi kam sai ya azumci abinsa.” Sahihin Hadisi ne da Buhari, Hadisi na 1,914; da Muslim, Hadisi na 1,082 suka fitar.
Kuma an samo daga Ammar bn Yasir (Allah Ya yarda da shi), inda ya ce, “Duk wanda ya azumci ranar da ake shakka (kafin Ramadan), ya saba wa Baban kasim (Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam).” Sahihin Hadisi ne da Abu Dawud, Hadisi na 2,334; da Tirmizi, Hadisi na 681; da Annasa’i, mujalladi na 4, shafi na 153; da Ibnu Majah, Hadisi na 1,645, suka fitar.
Nan za mu dakata, sai mako na gaba mu ci gaba, in Allah Ya kai mu.
Wassalamu alaikum warahmatullah!
Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (6)
Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna…