✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manufofin Tinubu ba su da alaƙa da turmutsutsin tallafi — Minista

Ministan ya ce irin wannan iftila'in ta taɓa faruwa a gwamnatocin baya.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ya kira ’yan siyasa da su daina danganta turmutsutsin da ya faru a jihohin Oyo, Anambra, da Abuja da manufofin tattalin arziƙin Shugaba Bola Tinubu.

Lamarin ya yi sanadin rasa rayuka sama da mutum 70, ciki har da yara kimanin 40.

Ministan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya danganta lamarin da matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar sakamakon gazawar tsare-tsaren Tinubu.

Sai dai ministan ya musanta hakan.

A wata sanarwa da babban mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar, ya jaddada muhimmancin tsara taron jama’a yadda ya kamata.

Idris, ya yaba da kyawawan niyyar masu shirya rabon abinci don tallafa wa marasa galihu, amma ya yi kira ga su haɗa kai da ’yan sanda da hukumomin bayar da agajin gaggawa kamar NEMA don tabbatar da tsaro da kare rayuka.

Ya kuma jaddada muhimmancin bin umarnin Sufeto-Janar na ’Yan sanda, Kayode Egbetokun, don yin aiki tare da ’yan sanda na yankuna domin samun ingantaccen tsari wajen tarukan jama’a.

Ministan, ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki da su guji amfani da lamarin don siyasa.

Ya bayyana cewa iftila’in ba shi da alaƙa da sauye-sauyen tattalin arziƙin Shugaba Tinubu.

Ya jaddada cewa irin waɗannan abubuwa sun faru a baya, kafin zuwan wannan gwamnati.

Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa suna da nufin inganta tattalin arziƙi da tallafa wa rayuwar ’yan Najeriya, musamman marasa galihu.

Ya yi kira a samu haɗin kai domin kaucewa irin wannan iftila’i a gaba.