✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman Benuwe sun samu sabuwar manhaja don bunƙasa hanyoyin samun kuɗin tallafi

Ƙananan manoma a Jihar Benuwe sun nuna kyakkyawan fatansu na samun ƙaruwar abinci a cikin ƙasa a dalilin samun sabuwar manhajar wayar salula mai suna…

Ƙananan manoma a Jihar Benuwe sun nuna kyakkyawan fatansu na samun ƙaruwar abinci a cikin ƙasa a dalilin samun sabuwar manhajar wayar salula mai suna FarmersWallet a Turance.

Wannan dandali na hada­hadar kudi wanda ke bai wa manoma damar adana kudi kadan-kadan domin amfani da su a lokutan shuka mai zuwa, zai sauya rayuwar miliyoyin ƙananan manoma a fadin Jihar Benuwe da sauran sassan ƙasar domin zai ba su damar samun hada-hadar kudi da kayan aikin noman da kuma hanyoyin kasuwanci.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, sabuwar manhajar za ta taimaka wa ƙananan manoma wajen ƙara samar da abinci a ƙasar, bayan ƙaddamar da manhajar FarmersWallet a ranar Litinin a Makurdi, babban birnin jihar.

Babban Jami’in Gudanarwa na Manhajar FarmersWallet, Injiniya Iorlaha Ɓalentine ya ce, wannan tsari an yi shi ne domin shawo kan matsalar rashin samar da wadataccen abinci ga ƙananan manoma suka jima suna fuskanta wajen cim ma burin su na bunƙasa noma.

“Mun samar da dandali na zamani na hada harkokin kudade ta hanyar fasahar zamani na farko a Nijeriya, wanda ke bai wa masu amfani da mu daga ƙananan manoma damar adana kudi yadda suka ga dama kuma cikin tsaro don aikin gona irin su shuka da siyan kayan aikin gona da takin zamani da kuma na’urorin noma, tare da samar da hanyar samun rancen kudi kadan-kadan da inshora da bayanan damar da kasuwa da kuma shawarwari na ci gaban harkar noma.

An tsara FarmersWallet ce domin magance matsalolin da ƙananan manoma ke fuskanta kuma mun yi imani cewa, zai taka muhimmiyar rawa wajen bude ƙofa ga zuba jari daga wajen manoman da kansu da ƙarfafa darajar nomanmu da kuma tabbatar da cewa, ƙananan manoma sun fi samun ƙarfin cike buƙatun samar da ƙaruwar abincin ƙasar,” in ji Shugaban.

China Peters, Shugaban Ƙungiyar Masu Kayayyakin Amfanin Gona a Jihar Benuwe ya bayyana cewa, damar da wannan manhajar ta samar za ta inganta muhalli, inda manoman jihar za su bunƙasa, wanda ba kawai ga iyalansu ba har ma ga tattalin arzikin Jihar Benuwe da ƙasar baki daya.

“A wani lokaci da sashen aikin gona ke fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da sauyin yanayi, sauyin farashin kasuwa da kuma samun kudi da ingantattun kayan aikin gona, ƙaddamar da manhajar FarmersWallet wani mataki ne mai matuƙar muhimmanci a wannan lokacin,” in ji Peters.

Shugaban riƙo na Ƙungiyar Manoma ta Nijeriya (AFAN) na jihar, Cif Abel Owiocho ya jaddada cewa, aikin gona da ke hade da fasahar zamani shi ne abin da ake yi a yanzu, inda ya buƙaci manoma a fadin jihar da su rungumi wannan sabuwar hanyar domin amfanin kansu.

“Fasaha ita ce zahirin abin da ake amfani da ita a halin yanzu. Ya kamata mu rungume ta duk da ƙalubalen da wasu manoma ke fuskanta a karkara da ba su da ilimin amfani da manhajoji. Amma za mu kai wannan ilimi zuwa gare su,” in ji Owiocho.