Manoman karkara a kasar Sin sun samu garabasar Yuan miliyan biyar da dubu 600, kimanin Dala dubu 850, wato daidai da Naira miliyan 34, saboda kokarinsu wajen dashen itatuwa a kauyen Lintao da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin a Lardin Ganasu, kamar yadda kafar yada labarai ta Chinnanews.com ta ruwaito.
Manoman karkarar da suka samu garabasar kudi, yawansu ya kai magidanta 80 Zhang Zinhai, wani da ya samu kaso mafi tsoka na Yuan dubu 100. Ya ci burin dasa dimbin itatuwa a shirin dashen badi.
Ya samu hanyar samun kudi mafi sauki fiye da sauran al’umma, saboda a cewarsa: “Babu bukatar kashe kudi a wannan aikin.”
A shekarar 2013, wani kamfani a kasar ya samar da irin dashe na tsirran itatutuwa dubu 400 ga daukacin magidantan da ke zaune a yankin. Bayan shekara uku an yanke cewa manoman za su mayar da yawan irin tsirran da aka ba su daga kamfnain, inda aka tsara biyansu kudi. Shi kuma kamfani zai sayar da wadannan bishiyoyi a Artewacin kasar Sin, wato yankin Mongolia da Shandi, ta yadda za su dasa korayen furanni a yankunansu.
Manoma sun samu garabasar Naira miliyan 34 saboda dashen itatuwa a Sin
Manoman karkara a kasar Sin sun samu garabasar Yuan miliyan biyar da dubu 600, kimanin Dala dubu 850, wato daidai da Naira miliyan 34, saboda…