✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma dubu 120 ne suka amfana da bashin noma a Kano

A kalla manoma dubu 120 a Jihar Kano ne suka amfana daga shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da bashi ga manoma da aka fi sani da…

A kalla manoma dubu 120 a Jihar Kano ne suka amfana daga shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da bashi ga manoma da aka fi sani da ‘Anchor Borrower Programme’ a wannan lokaci da ake fuskantar noman rani.

Shugaban Kungiyar Manomnan Shinkafa ta Jihar Kano (RIFAN), Alhaji Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da manema labarai.

Alhaji Aliyu ya ce tuni aka tura sunayen manoman da suka yi rajista zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN) don tantancewa da kuma bin hanyoyin karbar rancen.

Shugaban ya ce, kowane manomi zai karbi bashin kayan noma da kimarsu ta kai ta Naira dubu 220 da suka hada da kayayyakin noma da kudin da za a biya kwadago. “Kimanin manoma dubu 150 ne suka yi rajista don shiga shirin sai dai an rage manoman zuwa dubu 120 saboda batun lambar bayanai na  banki (BBN), tuni aka mika sunayen manoman da suka yi nasara ga Bankin Najeriya don fara aikin bayar da bashin don ganin lokacin noman rani yana kara kusantowa,” inji shi.

Shugaban ya shawarci manoman da ba su samu nasarar shiga shirin ba saboda batun BBN su yi hakuri inda ya tabbatar musu cewa su za a fara ba muhimmanci idan an zo rabon bashin noma na damina.

Alhaji Aliyu ya kuma shawarci wadanda suka samu nasara cewa su yi kokarin amfani da bashin da suka samu don bunkasa harkar nomansu na shinkafa a fadin jihar da kuma kasa baki daya. “Wannan dama ce ga ’ya’yan kungiyarmu ta su bunkasa tattalin arzikinsu tunda Gwamnatin Tarayya ta daura niyyar taimaka wa harkar noma don samar da wadataccen abinci a kasa,” inji shi.

Ya yi kira ga manoma a fadin kasar nan su rungumi noman shinkafa don kawo karshen shigowa da shinkafa daga kasashen ketare.

Idan za a iya tunawa a bara ambaliyar ruwan sama ta salwantar da fiye da kadada dubu biyar na gonakin shinkafa a fadin jihar inda manoma suka yi asarar shinkafar da ta kai Naira biliyan biyar.