Cibiyar Kula da Amfanin Gona ta Najeriya (NCE), ta ce ta horar da manoma 200 a Jihar Gombe kan hanyoyin adana amfanin gona da kuma sayarwa a kasuwanni.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron horarwar na wuni biyu da ya gudana a Gombe, Manajan Hukumar, Mista Benson Lawal, ya ce manufar ba da horon ita ce karfafa wa manoma gwiwar yadda za su samar da abinci a kasa.
Ya ce sun shirya fitar da manoman Najeriya daga kangin talauci ta hanyar koya musu dabarun adana amfaninsu bayan girbi da kuma yadda za su sayar a kasuwanni domin bunkasa rayuwarsu da kuma taimaka wa habakar tattalin arzikin kasa.
“Mun koya musu yadda za su adana amfaninsu har sai lokacin da suka bukaci sayar, har ila yau mun karfafe su ta hanyar da za su rungumi harkar musaya.
“Muna da tabbacin ilimin da muka samar wa manoman bayan samun horon zai taimaka musu wajen sayar da amfanin nasu a farashi mai kyau sannan su samu kudin shiga wanda zai inganta rayuwarsu,” inji shi.
A cewarsa NCE ta zo da wannan horo ne lura da cewa manoma suna noma abinci da kuma kayan da za a noma a sayar ba tare da an samu wata gwaggwabar riba ba saboda ba su san yadda za su sayar da kayan ba tare da sun lalace ba.
Kwamishinan Ciniki, Masana’antu da Yawon Bude-Ido na Jihar Gombe, Alhaji Nasiru Aliyu, ya ce sun yi kokarin ganin an samar da wuraren ajiya guda 25 a fadin jihar da zimmar adana amfanin gona.
A cewarsa, irin wannan tallafi zai bunkasa harkar aikin gona a jihar. Wakilin Aminiya ya ce kimanin manoma 200 ne aka zakulo daga kananan hukumomin jihar 11 domin su shiga shirin a dama da su.