✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manny Packuiao ya gina wa talakawa gida 1,000

A yunkurinsa na kyautata wa al’ummarsa, shahararren dan damben boksin din nan dan asalin kasar Filifins Manny Packuiao ya gina rukunan gidaje dubu 1 kuma…

A yunkurinsa na kyautata wa al’ummarsa, shahararren dan damben boksin din nan dan asalin kasar Filifins Manny Packuiao ya gina rukunan gidaje dubu 1 kuma ya raba su kyauta ga talakawan da ke  yankin Sarangani na Filifins yankin da ya fitio.

dan damben ne da kansa ya sanar da haka a shafin sada zumuntarsa na facebook a shekaranjiya Laraba.

“Ina mai sanar da duniya cewa na gina gidaje dubu 1 kuma na raba su kyauta ga mabukata da ke zaune a mazabata ta Sarangani da ke Filifins. Kuma na yi haka ne don in bayar da gudunmawata wajen ci gaban yankin da kasar Filifins.”

Idan za a tuna a wani wasan damben boksin da Manny Packuiao ya yi da Floyd Mayweather a baya-bayan nan, duk da an doke shi a wasan amma ya samu kyautar Dala miliyan 100 kwatankwacin Naira biliyan 36 kuma da irin kudaden da yake samu a harkar dambe ne ya yi amfani wajen taimaka wa talakawa.

dan damben wanda ya fuskanci kalubalen rayuwa saboda talauci ya nuna akwai bukatar ya tallafa wa marasa galihu yanzu da Allah Ya hore masa. 

Gwamnatin Filifins da wadanda suka ci gajiyar gidajen sun mika godiyarsu ga Packuiao bisa wannan karamci, inda suka yi masa addu’a da fatan alheri.