Maniyyatan farko na jihar Legas kimanin mutum 460 sun tashi daga filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed a ranar Lahadi.
Jirgin Kamganin Med-View kirar Boyin 747 ya tashi da maniyyatan da misalin karfe 12 da minti 52 na dare a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Kasa da jami’an Hukumar Alhazai ta Jihar da jami’an Hukumar Lura da Filin Sauka da Tashin Jiragen Sama na Hukumar FAAN da kuma jami’an kamfanin.
Maniyyatan wadanda ake sa ran za su sauka a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Sarki Abdul’aziz da ke Jidda suna cikin maniyyata kimanin dubu biyu na jihar Legas wadanda za su sauke farali a hajjin bana.