Hukumar Kula da Alhazai ta kasar Saudiyya ta ayyana ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba, 2020 a matsayin ranar da maniyyata Umrah daga sassan duniya za su isa kasar don fara gabatar da ibadar.
Hukumar ta kuma shimfida wasu dokoki da sharudai ga miniyyatan domin kare su daga yaduwar cutar COVID-19.
- NAHCON ta fito da ka’idojin tafiya Umrah daga Nijeriya
- #EndSARS: Filato ta yi asarar N75bn a kwana biyu
- Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci a Najeriya —Salihu Tanko Yakasai
Sharudan da maniyatan za su cika kafin su samu amincewar tafiya aikin ibadar a Kasa Mai Tsarki su ne:
- Matafiyi ya kasance daga shekara 18 zuwa 50.
- Nuna takardar shaida daga amintaccen cibiyar gwaji da ke tabbatar da maniyyacin ba ya dauke da cutar coronavirus.
- Kar gwajin ya wuce sa’a 72 da yi kafin tashin maniyyaci daga filin jirgin saman kasar da ya fito zuwa Saudiyya.
- Kiyaye ka’idojin neman izinin ziyara zuwa Masallacin Annabi (SAW) da zuwa addu’a Rawdha kamar yadda aka gindaya.
- Shaidar amincewar ranar tafiya da dawowa.
- Killace kai na tsawon kwana uku a masauki kafin fara gabatar da aikin Umrah.
- Samun abun hawan zirga-zirga daga filin jirgi zuwa masauki.
- Samun abun hawa domin zirga-zirga daga masauki zuwa Harami da Mikati.
Mu ma anan muna fatan Allah yasa a sauke farali lafiya, ya karbi ibadun da za a gabatar, ya bamu lafiya da zama lafiya.