✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mane ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na bana

Mane ya yi takara da Mohammed Salah na Liverpool da golan Chelsea, Edouard Mendy.

Sabon dan wasan Bayern Munich, Sadio Mane na kasar Senegal, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2022.

Wannan dai shi ne karo na biyu da dan wasan mai shekaru 30 ya lashe kyautar, bayan wadda ya lashe a 2019.

Tsohon dan wasan gaban Liverpool ya yi takarar ce tare da Edouard Mendy mai tsaron ragar Senegal da Chelsea da kuma Mohamed Salah dan asalin kasar Masar da ke taka leda a Liverpool da ke  Ingila.

Wadda ta ci kyautar a bangaren mata kuma ita ce Asisat Oshoala ta Najeriya da Barcelona.

Asisat ta tawagar Super Falcons, ta yi takarar ce da Ajara Nchout Njoya ta Kamaru da Inter Milan da kuma Grace Chanda ta Zambia da BIIK Kazygurt.

%d bloggers like this: