Sabon dan wasan Bayern Munich, Sadio Mane na kasar Senegal, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2022.
Wannan dai shi ne karo na biyu da dan wasan mai shekaru 30 ya lashe kyautar, bayan wadda ya lashe a 2019.
- Dalilin da manyan kungiyoyin Turai ba sa son sayen Ronaldo
- Ronaldo ya yi watsi da tayi mai tsoka na wata kungiya a Saudiyya
Tsohon dan wasan gaban Liverpool ya yi takarar ce tare da Edouard Mendy mai tsaron ragar Senegal da Chelsea da kuma Mohamed Salah dan asalin kasar Masar da ke taka leda a Liverpool da ke Ingila.
Wadda ta ci kyautar a bangaren mata kuma ita ce Asisat Oshoala ta Najeriya da Barcelona.
Asisat ta tawagar Super Falcons, ta yi takarar ce da Ajara Nchout Njoya ta Kamaru da Inter Milan da kuma Grace Chanda ta Zambia da BIIK Kazygurt.