Dan kwallon kafar Senegal, Sadio Mane ya ba da kyautar Naira miliyan 285 kwatankwacin Dalar Amurka 694,000 don gina asibiti a wani kauye.
Kauyen na Bambali, mai nisan kilomita 400 daga Dakar, babban birnin kasar Senegal, ya shafe shekaru babu ko asibiti daya a cikinsa, kuma nan ne mahaifar Sadio Mane.
- An sake ceto wasu karin daliban da aka sace a Kebbi
- Yajin Aiki: Kada mu dauki mataki a zarge mu da wata manufa — ASUU
Hakan ne ya sa dan wasan gaban na kungiyar Liverpool bayar da tallafin makudan kudaden don gina sabon asibiti a kauyen mai mazauna akalla mutum dubu biyu.
Mane ya kuma bayar da kyautar kimanin Naira miliyan 143 domin gina makaranta a kauyen nasu.
Sabon asibitin zai kunshi bangaren haihuwa, sashen kula da lafiyar hakori da kuma sashen kula da sauran cututtuka.
A makon jiya ne dan wasan ya yi wata ganawa da Shugaban Kasar Senegal, Macky Sall, kan batun gina sabon asibitin a mahaifar tasa.
“Mane ya gabatar mana da tallafin gina sabon asibiti a kauyen Bambali, wanda hakan zai taimaka wa harkar lafiya,” a cewar wani sako da Shugaban Kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A yanzu haka Mane yana taka leda ne a kungiyar Liverpool FC, inda ya lashe gasar Firimiyar Ingila, Gasar Zakarun Turai, UEFA Super Cup da kuma FIFA Club World Cup.
Dan wasan ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan nahiyar Afrika (CAF) a 2019.