✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United za ta yi balaguro a Chaina

A watan Yulin wannan shekara ce kulob din Manchester United zai yi balaguro a kasar Chaina a shirye-shiryen tunkakar kakar wasa ta 2016 zuwa 2017,…

A watan Yulin wannan shekara ce kulob din Manchester United zai yi balaguro a kasar Chaina a shirye-shiryen tunkakar kakar wasa ta 2016 zuwa 2017, kamar yadda kulob din ya fitar da sanarwar yin haka a ranar Talatar da ta wuce.
Kulob din ya ce yana sa ran zai shafe kimanin kwanaki takwas ne a can, kuma ya shirya wasannin sada zumunta  da akalla kulob biyu a lokacin ziyarar.
Sai dai kulob din ya ce nan da kwanaki masu zuwa ne zai bayyana sunayen kulob din biyu da zai yi wasannin sada zumuntar da su da wuri da kuma kudin tikitin shiga wasannin.
Wannan shi ne karo na 11 da kulob din yake kai irin wannan ziyara kasar Chaina. Kulob din ya ce yana da magoya baya da yawan ya kai miliyan 107 da ke zaune a kasar Chaina da hakan ta sa yake yawan kai irin wannan ziyara can, don faranta wa magoya bayan rai.
Kulob din ya kara da cewa kawo yanzu kimanin ’yan kallo su kimanin dubu 500 ne suka shiga wasannin sada zumuntar da kulob din ya shirya da kulob daban-daban a shekarun baya.  Kulob din ya ce ko a shekarar 2013 a lokacin da United ta kara da kulob din Kitchee kimanin ’yan kallo dubu 40 ne suka kalli yadda wasan ya kaya.  Kulob din ya ce hakan ya nuna akwai dimbin magoya baya a kasar da ke nuna musu so da kauna inda ya sha alwashin faranta musu rai a duk lokacin da kulob din ya samu damar yin haka.
kasar Chaina dai ta zama kasar da mafi yawan kulob-kulob daga Ingila suke tururuwar tafiya can don yin balaguro a duk shekara.
A watan Disambar bara (2015) wani katafaren kamfani da ke Chaina ya mallaki kashi 13 daga cikin 100 na kulob din Manchester City bayan shugaban kasar di Jinping ya kai ziyara kulob din.