Kulob din Manchester United da kuma na Arsenal da ke Ingila ne za su hadu a wasan kwata-Fainal a gasar cin kofin kalubale na Ingila da aka fi sani da FA Cup a ranar 7 ga watan gobe. 
Manchester United ta kai wannan matsayi ne bayan ta lallasa kulob din Preston North End da ci 3-1 a ranar Talatar da ta wuce yayin da Arsenal kuma ta kai wannan mataki bayan ta doke kulob din Middlesbrough da ci 2-0 a ranar Lahadin da ta wuce.
Dukkanin kulob din biyu dai sun taba lashe kofin FA har sau 11. Sannan kulob din Arsenal ne ya samu nasara a kan na United a shekarar 1979 da kuma 2005 a wasannin karshen da suka hadu a gasar ta FA.