✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manchester United ta ware wa sabon kocinta Fan miliyan 120 don cefanen ’yan wasa

Za a yi amfani da kudaden ne wajen yin sabbin dubin ’yan wasa

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ware wa sabon kocinta, Erik ten Hag zunzurutun kudi har Fan miliyan 120 don yin cefanen sabbin ’yan wasa a kakar wasa mai zuwa.

Kocin, mai shekara 52 a duniya, ya sanya wa Manchester United hannu a ranar Alhamis din da ta gabata, inda zai karbi ragamar kungiyar daga hannun kocin wucin gadi, Ralf Rangnick, a karshen kakar wasa ta bana.

Kungiyar ta dai damka wa sabon kocin ragamarta, inda ta ba shi kudaden don sayen ’yan wasan da za a gina sabuwar kungiyar.

Ana sa ran ’yan wasan kungiyar irin su Paul Pogba da Nemanja Matic da Jesse Lingard da Juan Mata da Edinson Cavani za su bar kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana.

Sabon kocin dai ya kulla yarjejeniyar shekara hudu da Manchester United.