✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United ta sha kashi a hannun West Ham 

Manchester United ta dawo mataki ma takwas a gasar Firimiyar Ingila.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sake yin rashin nasara a gasar Firimiyar Ingila a hannun West Ham da ci 2 da babu.

Jarron Bowen da Mohammed Kudus ne suka jefa wa West Ham kwallo a minti 73 da 78 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Wannan rashin nasara ya kawo Manchester United wasanni hudu ba tare da ta zura kwallo ko daya a raga ba.

Yanzu haka kungiyar ta dawo mataki na takwas a kan teburin gasar da maki 28 daga wasanni 18 da ta buga.

Sai dai kocin kungiyar Erik Ten Hag, ya bukaci ‘yan wasan kungiyar da su zage damtse don ganin sun bai wa mara da kunya.

Kocin ya koka game da rauni da wasu manyan ‘yan wasan kungiyar ke fama da shi.

Manchester United na fama da raunin ‘yan wasa, inda ‘yan wasa irin su Casemiro, Martinez, Maguire, Lindelof da sauran su ke jinya.

Sai dai a gefe guda wasu na ganin mai horar da kungiyar ba ya tabuka komai duk da cewar an kashe masa kudi wajen cefanen ‘yan wasa a farkon kakar wasannin bana.