Shahararren dan kwallon Ajantina da kulob din Real Madrid, Angel Di-Maria ya zama dan kwallo mafi tsada a tarihin kwallon kafa a Ingila bayan ya sanyawa kulob din Manchester United na Ingila hannu a kwantaragin shekara biyar a kan Fam miliyan 59 da dubu 700 wanda ya yi daidai da Naira Biliyan 15 da miliyan 480.
Di-Maria ya sanya hannu a kulob din ne bayan ya samu nasarar gwaje-gwajen lafiyarsa da Likitan kulob din ya gudanar a kansa a ranar Talata da ta wuce.
Sanya hannun dan kwallon ta sa ya zarce kowane dan kwallo da aka taba saya a Ingila a tarihin gasar ta firimiya. tsada.
Hakan ta sa ya zarce kudin da kulob din Chelsea ya sayi Fernando Torres a kan Fam miliyan 50 a shekarar 2011 daga kulob din Liberpool. Haka kuma ya zarce kudin da kulob din Manchester United ya sayi Juan Mata a kan Fam miliyan 37.1 a watan Janairun wannan shekara daga kulob din Chelsea.
Ga kadan daga cikin tarihin ’yan kwallon da aka saya a gasar ta firimiya wadanda suka fi tsada kamar haka:
A shekarar 2011 ne kulob din Chelsea ya sayi Fernando Torrers daga Liberpool a kan Fam miliyan 50.
A shekarar 2013 kulob din Arsenal na Ingila ya sayi Mesut Ozil daga Real Madrid na Sifen a kan Fam miliyan 42.4.
A shekarar 2011 kulob din Manchester City ya sayi Sergio Aguerro daga kulob din Atletico Madrid na Sifen a kan Fam miliyan 38.
A shekarar 2014 kulob din Manchester United ya sayi Juan Mata daga Chelsea a kan Fam miliyan 37.1.
A shekarar 2011 kulob din Liberpool na Ingila ya sayi Andy Caroll daga Newcastle United a kan Fam miliyan 35.
A shekarar 2014 kulob din Arsenal ya sayi Aledis Sanchez daga kulob din FC Barcelona na Sifen a kan Fam miliyan 35.
Ana sa ran Di-Maria zai fara yi wa kulob din United wasa a gobe Asabar a gasar firimiya a wasam da kulob din zai yi da na Burnley.
Manchester United ta sayi Di-Maria a kan Naira biliyan 15
Shahararren dan kwallon Ajantina da kulob din Real Madrid, Angel Di-Maria ya zama dan kwallo mafi tsada a tarihin kwallon kafa a Ingila bayan ya…
