✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United ta gayyaci yaran da ba su da galihu a Indiya

Wani yaro dan kimanin shekara 16 da haihuwa mai suna Rajib wanda kuma mahaifiyarsa ba ta da wata sana’ar da ta wuce karuwanci ya samu…

Wani yaro dan kimanin shekara 16 da haihuwa mai suna Rajib wanda kuma mahaifiyarsa ba ta da wata sana’ar da ta wuce karuwanci ya samu nasarar komawa kulob din Manchester United da ke Ingila.
Kulob din ya yanke shawarar horar da marasa galihu ne da ke Indiya a wani yunkuri na karfafa musu gwiwar samun nasara a rayuwa musamman a bangaren kwallon kafa.
Haka shi ma wani yaro da ba shi da sana’ar da ta wuce yin talla a kan titunan kasar ya samu nasarar shiga sahun wadanda za su tafi kolub din na Manchester a watan gobe.
Rahotannin da kafar sardarwar naij.com ta kalato ya nuna mahaifiyar Rajib wadda ke sana’ar karuwanci tana samun akalla Rufee 200 (kudin kasar) kwatankwacin Dala 3 wanda ya yi daidai da Naira 465 a matsayin kudin shiga a kullum.
Rajib ya ce “na yi murna kwarai da gaske da na kasance daya daga cikin yaran da za su tafi Ingila a wata mai zuwa don samun horo a kulob din Manchester United”.
Ya ce “ ina alfahari da mahaifiyata duk da sana’ar karuwancin da take yi kuma  ina fata na kubutar da ita daga wannan mummunar sana’a idan na samu nasara a kulob din Manchester,” inji Rajib a lokacin da yake hira da kafar watsa labarai ta AFP.
A nata bangaren mahaifiyar Rajib ta bayyana farin cikinta a kan wannan al’amari.  Ta ce “a kullum ina ziyartar bukkar yin addu’a ta Hindu don yi wa dana addu’ar samun nasara kuma ina fata zai kasance daya daga cikin wadanda za su yi nasara a kulob din na Manchester United.
Shi ma wani daga cikin matashin da ya samu nasara mai suna Arka Dey dan kimanin shekara 16 ya bayyana farin cikinsa. Ya ce kimanin shekara uku kenan da ya rasa mahaifinsa bayan ya yi fama da cutar kansa.
Kulob din Manchester dai yakan zakulo yaran da ba su da galihu a sassan duniya ne ciki har da Indiya don horar da su harkar kwallo.