Kulob din Manchester United da ke Ingila ya fara zawarcin dan Najeriya mai suna Mathew Olusande. Shi dai Mathew an haife shi ne a Amurka amma iyayensa ’yan Najeriya ne da ke zaune a Amurka. Sai dai bai taba buga wa Najeriya kwallo a kowane mataki ba, amma yanzu haka yana buga wa kulob din New York Red Bulls na Amurka wasa.
Kamar yadda jaridar Mail ta Ingila ta kalato, an nuna Mathew mai shekara 17 ya kai ziyara kulob din United na Ingila don samun horo, tun bayan da aka gama kakar wasa ta bana a Amurka. A nan ne Kocin United Luis ban Gaal ya yaba masa bayan ya ga yadda yake taka leda kuma tuni ya fara yunkurin dauke shi don ya zama dan kwallon Manchester United na dindindin.
Rahoton ya nuna cewa dan kwallon ya yi wa Amurka wasanni daban-daban a matakin matasa. Yana yin kwallon ne a matsayin mai tsaron baya a tsakiya da kuma a gefen baya (bangaren dama).
Rahotanni sun ce abin da ya kawo tsaikon canja shekar dan kwallon ita ce rashin samun takardar izinin zama a Ingila.
A wani labarin kuma, tsohon kocin Real Madrid na Sifen da AC Milan na Italiya da PSG na Faransa da kuma Chelsea na Ingila Carlo Ancelotti ya bayyana sha’awarsa na horar da kulob din Manchester United idan aka ba shi damar yin haka.
Manchester United ta fara zawarcin dan Najeriya
Kulob din Manchester United da ke Ingila ya fara zawarcin dan Najeriya mai suna Mathew Olusande. Shi dai Mathew an haife shi ne a Amurka…