’Yan sanda a birnin Manchester na kasar Ingila sun kama dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Mason Greenwood, bisa zarginsa da laifin aikata fyade da cin zarafi.
Ranar Lahadi aka kama dan wasan, inda ya kwana a can a kokarin ’yan sandan na fadada bincike a kan lamarin.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 3 a Zariya
- ’Yan sanda sun kama yaran Bello Turji 57 a Sakkwato
Rundunar ’Yan sandan ta Greater Manchester ta sanar da cewa, “An kara wa jami’an ’yan sanda masu bincike lokaci domin binciken wani saurayi mai shakera 20 da aka kama da zargin aikata fyade da cin zarafin wata mata. An kama wanda ake zargin ne a jiya [Lahadi] kuma yana tsare.”
Da take sanar da matsayarta kan lamarin zargin dan wasan wanda ke karbar Fam 75,000 a duk mako a matsayin albashinsa, kungiyar Manchester United ta sanar da cewa ta dakatar da dan wasan daga atisaye da buga wasannin kungiyar baki daya, har sai baba ta gani.
“Mason Greenwood ba zai dawo atisaye ba, kuma ba zai buga wasannin kungiyar Manchester United ba har sai baba ta gani,” inji kungiyar.
Kazalika, kamfanin Nike ya sanar da cewa yana cigaba da bibiyar lamarin da a cewarsa ya dame shi matuka.
Lamarin dai zai iya kawo cikas ga harkar tamaulan matashin dan wasan, duba da yanayin girman zargin da ake masa.
An kama dan wasan ne bayan wata budurwa ta saki wasu hotuna da bidiyo a kafafen sada zumunta na zamani, inda ta zarge shi da yi mata fyade da kuma cin zarafinta.
Har zuwa yanzu dai dan wasan bai ce komai ba.