✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United ta ci kasa; Benfica ta zura wa Ajax kwallo 1 mai ban haushi

Atletico Madrid da Benfica sun wuce mataki na gaba ma gasar.

A daren ranar Talata ne Manchester United ta karbi bakuncin Atletico Madrid a Gasar zakarun Turai, sai dai mai masaukin baki ta fadi ba nauyi.

Bayan yin kunnen doki a wasan farko tsakanin Atletico Madrid da Manchester United sati biyu da suka wuce ne aka sake karawa don fitar da gwani.

An murza wasan ne a filin wasa na Old Trafford da ke birnin Manchester a Birtaniya.

Dan wasan baya na Atletico Madrid, Renan Lodi ne ya jefa mata kwallo a minti na 41, wadda ita ce kwallo daya da ta raba tsakanin zare da abawa.

Yanzu haka dai Atletico Madrid ta wuce matakin Kwata Fainal bayan samun rinjaye da kwallo biyu daga wasa biyu da ta buga da Manchester United.

A daya wasan kuwa da aka gwabza tsakanin Ajax da Benfica, shi ma ci daya mai ban haushi ne ya raba gardama tsakanin kungiyoyin biyu.

Benfica ce ta samu nasara wajen jefa kwallo daya tilo ta hannun dan wasanta Nunéz a minti na 77.

Tuni ita ma kungiyar ta samu tikitin zuwa zagaye na gaba na Gasar Zakarun Turai ta UEFA Champions League.