Wani bincike da kafar watsa labarai ta NaijaNews ta buga a shafin intanet ta bayyana masu horarwa 10 da suka fi daukar albashi a sassan duniya.
Ta yi wannan bincike ne jim kadan bayan Jose Mourinho ya zama sabon kocin kulob din Tottenham na Ingila.
Ga jerin sunayensu kamar haka:
- Pep Guardiola: Shi ne kocin kulob din Manchester City na Ingila. Rahotanni sun ce shi ne kocin da ya fi daukar albashi a duniya. Yanzu haka yana karbar albashin Fam miliyan 20 (kimanin Naira biliyan 9 da miliyan 200) a shekara.
- Jose Mourinho: Ya kasance na biyu ne jim kadan bayan ya sanya hannu a kwantaragin shekara 4 a Tottenham a makon jiya. Yana karbar tsabar Fam miliyan 15 a shekara (kwatankwacin Naira biliyan 6 da miliyan 900).
- Diego Simeone: Shi ne kocin kulob din Atletico Madrid na Spain. Ya kasance na uku inda yake karbar Fam miliyan 13 a shekara (kwatankwacin Naira biliyan 5 da miliyan 900).
- Rafa Benitez: Shi ne kocin Daliang Yifang da ke kasar China. Yana karbar Fam miliyan 11 da dubu 500 a shekara (kimanin Naira biliyan 5 da miliyan 290).
- Fabio Cannabaro: Shi ne kocin Guangzhou Ebergrande na kasar China. Yana karbar Fam miliyan 10 a shekara (kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 600).
- Zinedine Zidane: Shi ne kocin Real Madrid na Spain. Shi ma yana karbar Fam miliyan 10 ne a shekara (kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 600).
- Antonio Conte: Shi ne kocin Inter Milan na Italiya. Yana karbar Fam miliyan 9 a shekara (kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 140).
- Thomas Tuchel: Shi ne kocin Paris Saint Germain (PSG) na Faransa. Yana karbar Fam miliyan 8 a shekara (kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 680).
- Ernesto Balberde: Shi ne kocin FC Barcelona na Spain. Shi ma yana karbar Fam miliyan 8 ne a shekara a matsayin albashi wanda ya yi daidai da Naira biliyan 3 da miliyan 680.
- Jurgen Klopp: Shi ne kocin Liberpool da ke Ingila kuma shi ne na 10 a jerin koci-kocin da suka fi daukar albashi a duniya. Yana karbar Fam miliyan 7 a shekara (kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 220).