✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Man United za ta yi tankade da rairaya

Kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayyana naiyarsa na yin tankade da rairaya a ’yan kwallonsa inda koci Jose Mourinho ya nuna zai…

Kulob din Manchester United da ke Ingila ya bayyana naiyarsa na yin tankade da rairaya a ’yan kwallonsa inda koci Jose Mourinho ya nuna zai bar ’yan kwallo bakwai ne kacal yayin da zai kori sauran a karshen kakar wasa ta bana.

Kocin United Mourinho ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta wuce jim kadan bayan kulob din West Brom ya lallasa na United da ci daya mai ban haushi a gasar firimiyar Ingila da hakan ta ba kulob din Manchester City damar lashe kofin  na bana, duk da ana saura wasannin biyar a kammala gasar.

Kamar yadda jaridar Irish Independent da ake wallafawa a Ingila ta kalato, ta ce Mourinhon zai yi tafiya da ’yan kwallon bakwai ne kacal da ya fi yarda da su yayin da zai sallami sauran.

’Yan kwallon da kocin zai tafi tare da su a kakar wasa mai zuwa sun hada da golan kulob din Dabid De Gea da Aledis Sanchez da Romelu Lukaku da Nemanja Matic da Jesse Lingard da Ashley Young da kuma Juan Mata.

Kocin ya ce duk ’yan kwallon da ba wadannan ba, to za su kama gabansu ne, kuma zai yi haka ne don ya kalubalanci kulob din Man City a kakar wasa mai zuwa musamman a wajen lashe gasar firimiyar Ingila.

Sai dai masana harkar kwallo suna mamakin yadda kocin zai rabu da zaratan ’yan kwallonsa irin su Paul Pogba wanda kulob din ya kashe zunzurutun Fam Miliyan 100 wajen sayo shi daga kulob din Jubentus kimanin shekaru 2 da suka gabata da Anthony Martial da kuma Rashford a karshen kakar wasa ta bana.