✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Man United ta lallasa Man City da ci 2-0

Kwallon da Antonio Martial yaci a minti na 30 da kuma wanda McTominay yaci a minti na 90 ne suka bai wa Manchester United nasara…

Kwallon da Antonio Martial yaci a minti na 30 da kuma wanda McTominay yaci a minti na 90 ne suka bai wa Manchester United nasara akan Manchester City a wasan da suka buga a yau Lahadi wanda aka yi a Old Trafford.

Martial, ya jefawa United kwallonta ta farko a minti na 30 da fara wasan da taimakon sabon dan wasanta Bruno Fernandez wanda ta siyo a watan Janairu data wuce. Sai McTominay ya jefa kwallo ta biyu ne a daf da tashi a wasan inda aka tashi ci 2-0.

Man United din dai ta lallasa City din a karo na biyu kenan a gasar Premier League ta bana bayan nasarar ci 1-0 da tayi a ranar 29 ga watan Janairu a filin wasan City din na Etihad.

Duk da rashin nasarar da tayi, City zata ci gaba da kasancewa a matsayi na biyu a teburin Firimiya da maki 57, inda ita kuma Man United zata farfado zuwa matsayi na biyar da maki 45.

Tuni dai Liverpool ta bai wa sauran kungiyoyin gasar tazara, inda a halin yanzu suke fafutukar samun gurbin buga wasan gasar Zakarun Turai na badi.