Akalla gidajen mai 10 ne Hukumar Albarkatun Mai (DPR) ta rufe a Jihar Bauchi cikin mako guda, saboda karya dokar sayar da fetur da Gwamnatin Tarayya ta gindaya.
Shugaban Sashen Ayyuka, Abdullahi Iliyasu, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Bauchi, yayin zagayen gidajen sanya idanu kan gidajen mai.
- Saudiyya ta wajabta wa alhazai karbar rigakafin COVID-19
- Boko Haram ta kona asibiti da makaranta a Yobe
- Tsadar Fetur: DPR ta rufe gidajen mai 5 a Katsina
“Gidajen mai kadan ne aka samu sun kara farashinsu zuwa N170, saboda haka mun sanya musu takunkumi da kuma tarar N100,000 kan kowane famfon mai da suke da shi a gidan man,” a cewar Iliyasu.
Ya ce an kama gidajen mai biyar da laifin sayar da man sama da farashin N162 da aka amince da shi.
Ragowar biyar din kuma an same su da laifin rashin tanadar da matakan kariya a gidajen man nasu.
Sai dai ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk gidan man da aka kama da laifin saba doka.
Kamfanin Dillacin Labarai (NAN), ya rawaito cewar akwai gidajen mai akalla 500 da suke karkashin kulawar DPR, don tabbatar da daidaiton farashin sayar da man kan kowace lita.